Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Yadda Ake Bude Email: Bayani Dalla Dalla Dauke Da Hotuna


Yadda Ake Bude Email: Bayani Dalla Dalla Dauke Da Hotuna
A kowani waye wan gari sababbain dabaru na fasaha ake kirkira daga kwararru a bangare daban daban dake fadin duniya A wannan zamani da muka tsinci kanmu, wanda za’a iya samun dukkanin wani bayani da ake bukata a yanar gizo, yanar gizo yana girma fiye da yanda muke tsanmani idan muka kai duba izuwa ga tura sako zamanin baya kafin ka tura ma mutuum sako sai ka biya wani ya kai ko kuma kaje da kanka amma yanzu da zuwar yanar gizo zaka iya turama mutum sako cikin yan dakikai a kuma a farashin da bai taka kara ya karya ba, a lokutanmu na yanzu in zaka tura sako daya shafi bangaren rubutu yana da kyau ya kasance kana da abu wanda ake kira da suna “Email”.
Sannan Akwai abubuwa da dama da ba za’a iya cin moriyarsu ba idan babu Email. Misali yanzu Kama daga rajistan makaranta, neman aiki, rajista a wani shafin yanar gizo domin samun bayanai kai tsaye, ko rajista a kafafan sada zumunta, babu abun da za’a iya yi a yau idan babu Email. Kai ko wayarka ta android na bukatar Gmail domin ta yi maka aiki yadda ya kamata. A takaice dai rashin Email ga mutum a wannan zamani mummunan hatsari ne. Amma abun mamaki shine, da yawa a cikin hausawa har yanzu ba su rungumi wannan dama ba wacce intanet ta kawo mana. Wadanda ke da Email din ma tuni sun manta da number sirrinsu ‘password’ domin ba sa amfani da shi.
A dan haka ne aka bar mu a baya sosai kuma ci gabanmu ke ta yar hawainiya idan aka kwatanta ta da ci gaban da sauran duniya ke samu. Lokaci ya yi da ya kamata mu sauya hakan. Abun dadin shine; bude Email yana da matukar sauki kuma ba’a bukatar sisinka:

GA BAYANI DALLA DALLA

Email dai wani na’urane da aka kirkiresa dan taimakawa mutane wajen tafiyar da al’amuransu na yau da kullum akwai email kala kala ma’ana akwai kamfanoni dayewa wayen da suka bude nasu amma dai duk aiki daya suke sunansu kadai ya banbanta. Akwai Yahoo mail, akwai Gmail, Akwai rocket mail akwai Hotmail akwai Naij mail da sauransu gabadayansu sunansu email amma kamar yanda na liissafa wasu ko wani kamfani da Sunanda suke aiki dashi duk kuma aiki daya sukeyi. Amma gaskiya bisa fahimta ta a cikinsu dukka Gmail yafi su sauki yafisu girma yafi su tsaro saboda mallakar babban kamfanin nan ne wato Google kuma sun mamaye ko ina. Abunda yasa nace yafiso tsaro duk lokacin da aka bude kanfani ana samun tsagerun da suke lalata kayan na’ura ta hanyar canza musu tunani  ko kuma cire ko goge kayan mutane a yanar gizo amma tun kafuwar kamfanin nan na Google har izuwa yau da nake Magana ba’a taba goge ko cire kayan da google ya kirkira ba ba’a ma haifi wanda zai taba kayansu ba a takaice kenan.


 Sannan amfanin Gmail ya zo ya kere sauran ‘yan uwansa da nisa. Misali idan kana da Gmail, za ka iya ajiye dukkanin hotunanka da bidiyo da wakokin a yanar gizo yadda ba za su taba bata ba har abada. Bayan haka, gmail ka ke bukata ka yi rajista a Youtube kuma ka samu damar shiga Google play store na wayar ka ta Android dan saukar da application, da dai sauransu. Saboda haka na yanke shawaran nuna muku yanda ake bude Email Da Gmail in dai ka gane wannan zaka iya bude na kowani kamfani:

Matakai
=>Bude browser din ka ta OPera mini, UC browser ko Chrome ko FireFox ka rubuta www.gmail.com a akwatin rubutu kamar haka
Yadda Ake Bude Email: Bayani Dalla Dalla Dauke Da Hotuna

=> Za ka ziyarci wannan shafin a kasa. zaka ga inda aka rubuta “create new account” kamar yadda kwarin ya nuna sai ka danna kai din.
Yadda Ake Bude Email: Bayani Dalla Dalla Dauke Da Hotuna

=>Daga nan zai kai ka shafin da za’a tambayeka number wayar ka sai ka sa wanda kake amfani dashi kada kasa number da baya kusa da kai saboda za,a turo ma sako kai tsaye, 

Yadda Ake Bude Email: Bayani Dalla Dalla Dauke Da Hotuna


bayan kasa zaka samu sako ta akwatin wayarka wato sms wanda zaka ga an rubuta “Goto https://g.co” da wasu tarkacen sai ka danna kai din zai kaika izuwa ga wani shafi.
Yadda Ake Bude Email: Bayani Dalla Dalla Dauke Da Hotuna

==> za,a tambayeka ta cika wani form kafin ka wuce gaba sai kayi hakan ta hanyar shigar da abunda ake nema daidai kamar haka

=> Inda aka rubuta ‘First Name’, rubuta sunan ka/ki cikakke. Inda aka rubuta ‘last Name’, rubuta sunan mahaifinka sai Ka sauko kasa inda aka rubuta ‘Date of Birth’ ka zabi watan haihuwar ka sannan ranar da aka haifeka sai shekaran haihuwar ka dukka ta hanyar rubuta su da lambar Idan ba’a san ranar haihuwa ba, za’a iya rubuta koma me. Amma shekarun su zama daidai. Idan shekarun ma ba’a sani ba, a kiyasta dai dai misali. sai kuma nagaba shine ‘Gender’ ma’anarsa jinsi in kai na miji ne sai ka zabi ‘Male’ in kuma ke na mace ce sai ki zabi ‘Female’ daga nan sai a danna in da aka rubuta ‘Next’  
Yadda Ake Bude Email: Bayani Dalla Dalla Dauke Da Hotuna

 zai kai ka izuwa ga wani shafi inda za’a umurce ka da ka zabi ‘Username’ ka rubuta lakani, duk abin da ka rubuta a nan shi zai zama Email Din ka. Misali idan ka rubuta afreen, Email dinka zai zama [email protected] sai a latsa ma bullin “Select” in dai kaga ya rubuta wata alama mai dauke da jan cala toh wannan bazzyi ba sai ka sake sa wani, ba lallai ne sunan da ka sa da fari yayi ba zayyu wani ya taba dudewa dashi in har hakan ya kasance sai ka sake zaban wani ko kuma ta hanyar sa masa wasu lambobi a gaban ko bayan misali [email protected] Ya  kamata gaskiya mutum ya yi amfani da sunan shi gaba daya ko kuma a kiyasce. Idan an rigaya an dauki sunan ka, zaka ga sun baka zabi dauke da sunan an kara lambobi a karshe.
Yadda Ake Bude Email: Bayani Dalla Dalla Dauke Da Hotuna
 
==> in har ka samu wanda yake aiki bayan ka danna ma bullin ‘select’ zai kai ka izuwa ga wani shafi inda za’a umurce ka sa lambar tsaro wato “password” sai kayi hakan tare da maimaita abunda ka sa da fari a akwati na biyu inda a rubuce “Confirm Your password” a nan sai a zabi password mai kyau wanda ba za’a yi saurin mantawa ba. A tabbata abu ne da za’a iya tunawa duk daren dadewa. sannan sai ka danna inda aka rubuta “Finish”. 
Yadda Ake Bude Email: Bayani Dalla Dalla Dauke Da Hotuna

Shikenan an gama. Yanzu idan ka ziyarci adireshin www.gmail.com, zai bude maka wannan akwati

Sai ka rubuta Email din da ka zaba, da password, ka danna dan akwatin nan har sai ka ga wannan dan alamar ta ‘good’ sai ka danna inda aka rubuta ‘sign in’. Duk wanda ka baiwa Email dinka ya turo sako, to zaka ganshi a nan, haka zalika zaka iya samun sako daga shafunan yanar gizo idan ka yi rajista da su. Bayan haka, kaima kuma za ka iya tura sako ga wasu Email din. Idan da wata tambaya, za’a iya rubutawa a kasa.


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive