Email
yakan bamu damar tura abubuwa da dama kama daga rubutaccen sako, sauti, hoto da
kuma hoto mai mosti cikin sauki zuwaga abokan hulda ko kuma abokan arziki. A
makon daya gabata nayi cikakkiyar bayani dalla dalla ma’anar sa da kuma yadda
ake bude shi tare dashi gmail. A wannan karon kuma insha Allahu zan nuna muku
hanyar da ake bi wajen shiga account na gmail din da aka bude.
Matakin Farko:
Mutum zai ziyarchi addreshin gmail din wato www.gmail.com zai kaisa izuwa ga shafin
nan wanda shine babban shafinsu na shi gmail.
A
sama can bangaren hannun dama mutum zaiga inda aka rubuta “Sign in” wanda
ma’anar sa a hausance shiga ciki. ba lallai bane mutum yaga wannan shafin mafi
yawancin lokutan yana kai mutum ne izuwa ga mataki na biyu koda yake ya dan
ganane da wani irin browser mutum yake aiki dashi ko kuma wani irin salula
mutum ke aiki dashi a mafi akasarin lokutan yana nunawane wa masu aiki da
chrome browser ko kuma masu aiki da kwanfuta.
Mataki na Biyu: za’a umurci mutum yasaka
email nasa a dan akwatin dake k’asan nan misali email namu na shafin nan shine [email protected]
sai na sanya shi a cikin akwatin tare da latsa ma bullin “Next”
wanda zai bada
damar zuwa mataki nagaba. Akwai wasu sa’in da zai rubuta wa mutum “Email not
found” kodai maka mancin haka yana gayawa mutum cewar email daya sanyan nan ba
dai dai bane wata kila an yi tuntuben kalma wajen rubutu dole mutum ya lura a
lokacin da yake rubutawa dan gujewa kuskure.
Mataki na Uku: Zai
tambayi mutum ya sanya numbobin sirri wato wanda aka fi sani da password a
turance, sai mutum ya sanya shi tare da latsa mabullin “Next”
in dai mutum ya
sanya numbobin sirrinsa daidai zai kaisa izuwa ga account nasa in kuma ba dai
dai bane zai fito da wani rubuta mai kala ja dauke da “incorrect password” ko
kuma “wrong password” koma wanne ya sanya maka daga ciki yana gaya maka cewar
numbobin sirrin ba daidai bane sai ka goge su sannan ka canza zuwa wani wanda
ka sanya a lokacin da kake budewa.
Wannan
shine cikkakiyar hanya da ake bi wajen shigan email naka na gmail ku kasance
tare da Duniyan Fasaha don samun sabbin ababe da zasu amfaneku a al’amuran yau
da kullum.
-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:
Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan
Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
No comments:
Post a Comment