Yadda ake masa
Barkanmu da warhaka Uwargida tare da fatan
ana cikin koshin lafiya. Akwai hanyoyi da dama wadanda ake bi don yin masa.
Yadda wata zata tsara na ta masar daban take da yadda wata uwargidan za ta
sarrafa na ta. Akwai nau’ukan masa da dama kamar masar Gero da Dawa da Semo da
kuma Shinkafa da dai makamantansu. A yau na kawo muku yadda ake masar Shinkafa
a cikin hanya mai sauki ba tare da an bada ayi ko kuma a saya ba.
Ababen
da ake bukata
·
Danyen
shinkafa
·
Albasa
·
Man gyada
·
Yis da
‘baking powder’
·
Siga
·
Albasa
Hadi
A jika danyar shinkafa na tsawon awa daya
sannan a wanke ta carak a zuba a cikin na’uran markade. Sannan a tafasa
shinkafar kadan kafin ta nuna sosai sai a sauke a zuba a cikin wannan danyar
shinkafar sannan a yayyanka albasa a kai sannan a markada har sai shinkafar ta
yi laushi sosai sannan a zuba a cikin roba.
Bayan haka, sai a zuba yis a ruwan dumi kadan
sannan a zuba a ciki. A sake dauko ‘baking powder’ a zuba a gauraya sosai
sannan a rufe a sanya a rana har sai hadin ya tashi.
Sannan a dauko Tanda a daura a kan wuta. A
zuba siga a roba da ruwa kadan yadda za ta narke sannan a zuba a kullun masar a
sake gaurayawa . sannan a zuba man gyada kadan idan ya yi zafi sannan a debo
kullun a zuba a ramukan tandar. Idan ya dan nuna sannan a sake juya masar zuwa
dayan gefen domin ta nuna. Bayan ta nuna sannan a sauke a sanya a kwano.
Za a iya cin wannan masar ko waina da yajin
kuli ko miyar taushe ko kuma miyar Alayyahu. A ci dadi lafiya.
І'm really enjoying thhe theme/Ԁesign of yoսг
ReplyDeleteweb site. Do you ever run into аny web browser compatibility problems?
A few oof my bⅼog readers һave complained аbout mmy blog not oⲣerating correctly inn Explorer but looks geat
іn Opeгa. Do yyou have any suggestiions to help fix this problem?
Hello! I could have sworn I've been to your blog before but after looking at a few of the posts I realized it's new to me.
ReplyDeleteAnyhow, I'm definitely pleased I came across it and I'll be bookmarking it and checking back often!
.you really tried brother keep it up
ReplyDelete