Yadda ake sa rubutu (post) a Blogger
Assalamu
Alaikum yan uwa barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa daku a cikin sabon
shirin namu wanda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha, a
makon daya gabata nayi jawabi filla filla matakan da za’abi wajen bude blog
tare da blogger a wannan karnin kuma insha Allahu zanyi bayanine yadda ake saka
rubutu (posting) a shi blogger wanda hakan yakan baiwa maziyarta shafinka damar
karanta wannan rubutun.
Abu
na fari da mutum zai fara anan shine shiga account dinsa domin kuwa ba yadda
za’a yi mutum yasa wani rubutu a shafinsa ba tare da ya shiga account dinsa ba
a rubutun daya gabata nayi jawabi dalla dalla Yadda ake shiga account wato login a blogger, sannan kuma bazai iya
sa wani abu ta hanyar ziyartan shafinsa ba misali in addreshin shafina
duniyanfasaha.guidetricks.com shiga wannan addreshin kawai zai bani damar
karanta abinda aka sanya ne; in har mutum yana so ya saka rubutu to dole sai
yabi matakan da zan zayyano.
Idan
mutum yana so yayi post a shafinsa na blogger a daidai hannunsa na hagu bayan
yashiga wato login a account nasa sai ya latsa inda aka rubuta Post na fari zai
kaisa izuwa nan.
Za’a
tatar da karamin akwati na fari ana kiransa title a turance shine inda mutum
zai rubuta suna ko silar abinda yake son rubutawa misali anan sunan wannan post
din “yadda ake post a blogger” sai mutum ya sanya ta a daidai wajen.
Babbar
nan kuma shine wajen da za’a saka duk jawaban da ake son nunawa karkashin suna
da aka sa misali duk wannan dogon surutan nawan suna cikin wannan babbar
akwatinne amma shi asalin suna silar wannan rubutun na Yadda ake post a blogger yana cikin akwatin na fari ne. haka zalika
mutum zai iya cope abu daga wani dandalin sadarwa kamar su whatsapp ko kuma
facebook sannan yayi pesting nasa kamar yadda akeyi a wajajen da aka copo abun
(ta hanyar latsawa a tsaya nayan wasu dakikai sannan na danna ma bullin
“paste”). Bayan mutum ya kammala sai ya latsa ma bullin “publish” wanda ke rubuce
a sama a daidai hanunsa na dama domin fitar abinda ya rubuta a shafinsa.
Yana
da kyau mutum ya kula da wayannan madannan guda hudu wanda suke sama a hannun
dama wato “publish”, “Save”, “Preview” da kuma “Close” akwai banbanci sosai
tsakanin wayannan madannan.
Abu na fari wato publish amfaninsa shine duk sa’in
da ka latsa wannan mabullin to duk abinda ka rubuta zai fito a shafinka wanda
duk ya ziyarci shafinka zai gani sannan kuma zai iya karantawa. Abu na biyu
kuma a jerin madannan shine “save” amfanin wannan mabullin shine misali ina rubutu
yanzu sai wani matsala ya taso wanda ya zamana dole ne na bar abinda nakeyi na
je izuwa ga shi to mutum sai ya latsa wannan mabullin wanda duk sa’in da ya
dawo zai sami abinda ya rubuta yadda yake sai dai akwai banbanci tsakanin sa da
wanda nayi bayani a baya wato publish shi save in ka latsa sa ba zai fito a
shafinka ba ma’ana ko mutum ya ziyarci shafinka bazai gani ba amma kuma kai ko
wani sa’in ka dawo admin dashboard naka zaka tarar da abinda kayi saving nasa
yana nan daram sai dai in ka goge (wato kai daya ne zaka iya ganin yayin da
kayi saving).
Na
uku kuma shine “preview” wannan mabullin amfaninsa shine zai baka damar ganin
yadda abinda ka rubuta zai fito a shafinka kama daga surar rubutun da kuma
tsari. Abu na karshe kuma a jerin mabullan shine “close” amfanin sa shine
cirewa ko kuma koma wa baya ba tare da ya adana ba amma wasu sai’in yakan iya
adanashi wato auto saving a turance sabida duk lokacin da kake rubuta wani abu
a wajen abar rubutun yana adanashi sabida gugewa wata matsala irinsu daukewar wuta
ko kuma daukewar layin sadawar wanda koda hakan ya faru zaka samesu yadda suke
ba tare da ka sake wani sabon aiki ba.
Wannan shine takaitacciyar bayani
yadda ake saka rubuta a shafin blogger. Ku kasance tare da Duniyan Fasaha domin
samun ingattaciyar abubuwa wanda zasu taimakeku a harkokin yau da kullum naku a
koda yaushe Jikan marubuta kuma sharifin zamani ‘Muhammad Abba Gana’.
-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:
Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan
Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
I enjoy what you guys are up too. Such clever work and coverage!
ReplyDeleteKeep up the awesome works guys I've incorporated you guys to my personal blogroll.
Thank you for some other informative blog. The place else could I get
ReplyDeletethat kind of info written in such an ideal way? I've a undertaking that I'm just now
running on, and I've been on the look out for such info.
Muna godiya
ReplyDeleteHausathechn.comiques blogspot.com
ReplyDeleteMasha'allah
ReplyDelete