Ya Password din ka yake? Ya kuma ya kamata a ce yake?
|
Assalamu Alaikum Barkanmu da sake saduwa daku
cikin sabon cikin shirin namu wanda yake zuwa muku kai tsaye daga mujjalar
duniyan fasaha, insha Allahu yau zamu tattauna game da yanda password naka yake
da yanda ya kamata ya zama, Ya ka ke rubuta password dinka a akwatin Email din
ka? Ko kuma na facebook ko kuma twitter da duk dai wani shafin internet da kake
shiga. Idan har kai ma’abocin kokarin rubuta lambobi masu sauki ne kamar
123456, ko kuma 98654, ko kuma kana amfani da sanan suna ne wajen password din
ka kamar salisu, Ibrahim, ko kuma kai mai son saka sunan masoyiyarka ne kamar
Fatima, amrat, beebah ko Aisha, ko kuma kai ma’abocin rubutun kalmomin soyayya
ne kamar iloveyou, ko kuma fatimamylove ko kuma thankyou, to ina tabbatar da
cewar wannan password din naka zai zama mai sauki wajen ganowa ko bai zai yiwa
hackers wahalar shiga ba domin sacewa ko kuma aika maka da virus cikin
shafukanka ba.
Ga
yadda ya kamata ka rubuta password dinka
·
Karanci harrufa
goma (10)
·
Ya kunshi
kananan harrufa da manya a cikin sa
·
Ya kunshi
alamomin rubutun na musamman
·
Ya kasance
akwai lambobi a cikin su
·
Kada ya
kunshi sunan masoyi, ko mahaifa da makamantansu
·
Kada ka yi
amfani da sanannun kalmomi, kamar iloveyou, ihateyou, ihateu, da makamantansu
·
Kada kayi
amfani da lamban wayarka ko na wani
·
Kada kuma
ka yi amfani da ranar haihuwarka kamar, oct1977.
Ga misali
Dun!yanfasafaAbbaGana@er6969 – Wannan
password yayi karfi sosai.
To ka yi la’akari idan ka kirkiri password dinka
da wannan hada hade ya kake gani?
No comments:
Post a Comment