Yadda zaki Kula da farcenki
Farce
yana da amfani kwarai da gaske ta fuskar ginuwar jiki. Sai dai hakan ba zai
samu ba sai idan har mun ba su kulawa ta musamman. Lafiyayyu kuma kyawawan
farata su ne wadanda suke sumulsumul babu wata
gargada ko karkacewa a jikinsu. Za ki samu cewa gaba dayansu sun
zama
launi guda ba tare da wani dameji na rauni ko tabo a kai ba.
Ga
wadansu hanyoyi da muke ganin matukar za mu kula da bin su dakidaki, to za mu
samu biyan bukata na mallakar kyawawa kuma lafiyayyun farata:
1.==> Ki guji cire farce da hakori:
Ko da ya zama cewa wani abu ya taba farcenki ya yi irin dagowar nan, kada ki sa
hakori ki cizge shi, domin hakan zai sa ya fita ba bisa ka’aida ba ta yadda har
zai sa a tsarin farcen ya zama wani iri daban. Wato sai ki ga wani bangaren na
farcen ya fi wani tsawo. A maimakon haka ki sami reza ko kuma abin yankan farce
da ake kira da nail cutter ki yanke farcen da shi.
2.==>
Bayan kin kammala da yanke faratanki za ki iya samun man farce ki shafe su da
shi, wanda hakan shi zai sanya faratanki su rika walkiya da sheki, ba lallai
sai kin sanya jan farce ba.
3.==>
Ki kula da farcenki ta hanyar zuwa salun akaiakai.
4.==> Ki
guji tara farce ya yi tsayi mai yawan gaske, wato akwai bukatar su zama a yanke
a koyaushe.
5.==> Kada
ki bari farcenki ya zama a jike koda yaushe, domin hakan zai sa ya rika
kakkaryewa tun kafin ma ki kai ga yankewa. Idan ya zama za ki yi aiki da ruwa,
yana da kyau ki sami irin safar hannun nan ki sa, don ta kare miki faratanki
daga lalacewa.
6.==>
Kada ki yi amfani da alkamashi wajen yanke farcenki, ko da farcen ya kasance
mai rauni ne, balle kuma ga wanda ba shi da wata matsala.
Idan
har ke mai sha’awar tara farce ce to ki tabbata cewa kina kula da su ta hanyar
fitar da duk wata dauda da ke shiga cikinsu ta zauna. Idan kika kula barin
dauda ta zauna cikin farce ba shi da kyawun gani a ido ma, ballantana ga
lafiyar jiki.
Thank you a lot for giving everyone an extraordinarily remarkable opportunity to read in detail from this website.
ReplyDeleteIt is always very cool and also packed with a lot of fun for me and my office co-workers to search
the blog at the least thrice weekly to learn the new things you have.
Of course, we are actually happy with the special tips you serve.
Certain 4 facts on this page are rather the most suitable we
have all had.
Vidéo craquante d'une chatte et son petit.
ReplyDeleteResearch Opinions handle and help online surveys.
ReplyDelete