Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Yanda zaka magance tabon fuska kashi na 2 – Gyaran Fuska

Yanda zaka magance tabon fuska kashi na 2 – Gyaran Fuska
Yanda zaka magance tabon fuska kashi na 2 – Gyaran Fuska

Assalamu Alaikum barkanku da warhaka barkanmu da sake saduwa da ku cikin sabon shirin namu insha Allahu yau zanyi bayanine a kan yanda zaka magance tabon fuska duk da cewa wannan bashine karo na fari dana fara rubuta wannan ba, na samu wannan tambayar daga wajen mutane sama da 30 akan cewar yaya za’ayi a cire tabon fuska wasu sukance wanda na bayar kwana kin baya sun gwada amma baya musu aiki shine na yanke shawarar rubuta wani wanda insha Allahu za’a dace.

Idan kana ko kina fama da tabon fuska wanda hakan na faruwa ne saboda mutuwar kuraje dasuka fito a baya, ko kuma ka/ki na fama da tattarewar fatar fuska wanda fata takan yayyakushe kota tattare saboda yawan shiga rana kokuma bisa wani dalili da ba sai na tsaya lissafowa ba. insha Allah yau zan baku maganin wanda da iznin Allah zai magance maka matsalar da ka/kike fama dashi na tabo ko kuma na tattarewar fata.
 ina son mutane su gane cewar hada magani uku, biyu ko fiye da haka daga kunshi daban daban baya iya zama gyara sai dai ya kaika izuwa ga matsala duk wani abunda nake bayar wa anan in harka gwada daya bayyi ba sai ka kyalesa ka gwada wani daban karka/ki  taba hada biyu kana yinsu a take tareda sa ran samun waraka hakan san bazayyuba sai sa a ko wai lokaci nake kokari wajen rubuta hanyoyin da za,a magance wata matsala guda biyu koma biye da haka dan wasu basu aiki a jinin wasu shawarata anan kada ka hada abu biyu ka dauki daya ka gwada in bayyi ba sai ka kyalesa ka dauka dayan kada ka hada dukka biyu.

Kowa yana so ya ga fuskarsa yayi haske ba tare da wani tabo ko kuraje ba idan aka dage da yin wannan sau daya a sati lallai za,a ga sakamako mai kyau, ba wai daga gwadawa sau daya bayyi aiki ba sai ka chanza shawarar daina yinsa ko kuma ka turo mana da sakon cewar ka gwada bayyi ba a,a abun ba haka yake ba magani ko wani iri yana daukan lokaci kafin aga sakamakonsa yana da kyau ka sanya hakuri a duk abunda kake yi.

·        Zuma babban cokali 2
·        Madarar gari babban cokali 4
·        Ruwan dumi babban cokali 2.      
   a hadasu waje daya a dama Sai ana shafawa a fuskarki banda ido da baki sai a samu mayafin ban daki (towel) mai kau a jika a cikin ruwan dumi a matse sai a shimfida a fuskar da aka shafa wanann hadin.  a bari yayi minti goma sai a goge sannan a wanke fuskarki zatayi haske, laushi, duk wani tattarewa da tabo zai tafi kuma fuskar mutum zanyi kama da dan shekara 20. Allah ya bada sa,amawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive