Sanko ya kasance wani cuta ne dake addaban wasu sa shi na mutane, wadda hakan na taba kyawun na miji ko mace. Bisa dalilin hakan mutane da dama basu sha’awar ganin sanko balle samunsa.
Akwai abubuwa bila adadin dake janyo samun sanko wasu daga ciki sun hada da: yawan gajiya, yawan amfani da launi a gashi domin rage furfura, yawan daukan abu mai nauyi da sauransu. Ba iya wannan kadai ba za’a iya gadon sanko daga iyaye ko kuma wani a dangi muddin yana dashi ko tana dashi.
Insha Allahu yau a Duniyan Fasaha mun taho muku da wasu hanyoyi masu sauki da za’a bi wajen magance wannan matsalar idan ana fama dashi. Wasu daga cikin hanyoyin sun hada da:
1.==> Amfani Da Albasa: Cin albasa na taimakawa wajen feso da gashi da suka zube, yana da kyau mai fama da wannan cutar ya lazimci cin danyar albasa kamar guda biyu koma fiye da haka a kowani rana. Domin samun saukin hadiya za’a iya yin kwadonta da rama ko wani ganye da ake so. Sannan za’a iya jajjaga ta ana shafawa a inda sanko yake hakan zai taimaka matuka wajen dawor da abinda aka rasa.
2.==> Lalle Da Man Kwakwa: Za’a iya hada lalle da kuma man kwakwa waje daya sannan a yawaita shafawa a wurin da gashin ya zube ko wajen sanko na kimanin minti talatin (30) koma awa guda sannan a wanke, hakan na maitakawa matuka wajen magance matsalar sanko da rashin gashi.
3.==> Bakin Soda Da Man wanke Kai: A samu bakin soda da kuma man wanke kai a hada waje daya sannan a ringa shafawa a sankon, yin haka na magance kowace matsala na fata da kuma gashi haka zalika yana taimakawa wajen haifar da gashin kai.
4.==> Gwaiduwar Kwai, Ruwan Lemun Tsami Da Man Zaitun: A hada wayen nan waje daya sannan a yawaita shafawa wajen da babu gashi kamar sau biyu a mako hakan zai taimaka wajen fitar da gashi da wuri.
5.==> Ruwan Na’a-Na’a Da Ruwan ‘Aloe Vera’: Wayanan na dauke da sinadaran bitamin A da E da kuma C, haka zalika suna taimakawa matuka wajen fitar da gashin da suka zube cikin kankanin lokaci, yana da kyau a rika hada ruwan Na’a-Na’a da ruwan Aloe Vera kadan sannan a yawaita sha na kimanin mako biyu da yardan Allah za’a samu chanji.
6.==> Ganyen Dogon Yaro: Yana da kyau a yawaita amfani da ruwan ganyen dogon yaro domin yana tsiro da gashi a yan wasu kankanin lokaci haka zalika yana taimakawa wajen rage furfura a gashi. Za’a tafasa ganyen dogon yaro ne sannan idan ya wuce sai a yawaita amfani da ruwansa wajen wanke kai.
7.==> Man ‘Castor’ Da Man Kwa-kwa: A hadasu waje daya sannan a yawaita shafawa wajen da akeso sannan a rufe wajen da leda na tsawon mintuna biyar, hakan zai taimaka matuka wajen shiga kofofin gashin.
Yana da kyau a dauki daya daga cikin jerin ababen da muka lissafo a jarraba na tsawon lokuta kafin gwada wani, kada a hada duka domin samun sakamakon gayyawa yin hakan zai iya kawo babbar illa ga lafiyar jiki. A kiyaye!
Masha allah
ReplyDelete