A wasu sa’in mutum yakan so chanza kallar
rubutunsa don ado ko kuma dan banbanta kalma tsakaninsa da suran. Ko ma dai me
manufar mutum yake insha Allahu a wannan makon zamu tattauna ne game da yadda
ake canza kallar rubutu a blogger wato wajen rubutun shafi a yanar gizo.
A hakikanin gaskiya chanza kallar
rubutu a shafin blogger ba wani abune mai matukar wahala ba ko kuwa yana
bukatar wasu matakai masu tsauri ba. A’a sam bai da wani wahala face duk sa’in
da mutum yake son canza kalar rubutu sai ya bi yan wasu matakai masu saukin
gaske.
Matakai
da ake bi wajen canza kallar rubutu a shafin Blogger
1.==>
Da fari mutum zai ziyarci wajen da ake posting ma’ana wajen da ake saka abunda
aka rubuta wanda mukayi bayani dalla dalla a makon daya gabata Yadda ake sa rubutu (post) a Blogger cikin
sauki.
2.==> Yayin
da mutum ya kammala rubuta abunda yake son sawa sai ya zabi kalaman dayake son
chanza wa kallar ta hanyar yin highlighting nasu sannan ya danna mabullin Kalmar 'A' wadda yake dan sama ta bangaren hannunsa na dama sannan mutum ya zabi kallar
da yake so.
Za’a
iya bin wannan matakan koda kuwa an sa kallar ana kuma son sauyawa.
Wannan
shine takaitacciyar hanya da ake bi wajen chanza kalar rubutu a shafin blogger
dafatan wannan ya taimaka matuka, a kasance tare da shafin Duniyan Fasaha dan
samun sabin abubuwa da zasu amfaneku a yau da kullum. Naku a yau da kullum
Jikan Marubuta Muhammad Abba Gana. Bissalam!!
-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:
Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan
Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
masha allah
ReplyDelete