Ababen da ke magance matsalar qurajen fuska da fata
Assalamu alaikum masu karatu tare da fatan
ana lafiya? Bari in yi muku wata tambaya. Shin mene ne wadannan abubuwan da ke
magance matsalolin fata?
Lallai wadannan abubuwa ne, wanda a kullum
mukan yi amfani da su a dakin girki ko kuma amfani da su a abinci. Idan aka
koyi yadda ake amfani da su a fata, domin magance matsalolin fata, lallai ba
sai an kashe kudi da dama ba wajen sayen magani.
Ina son in gargadi masu karatu da su gane
cewa a cikin abubuwan da zan lissafo, daya kawai ake so a riqa amfani da shi
wanda ta dace da fatar mutum. Amfani da su gaba daya na qara haifar da wata
matsalar fata. Yana da kyau a gwada amfani da su tsawon watanni biyu zuwa uku.
==> Domin
magance matsalar fata mai yawan saba ko masu samun barewar fata daga fuskarsu
ko wata bangare a fatar jiki, sai a samu suga mai launin qasa da zuma da
madara kadan yadda sugan ba zai narke ba, sai a shiga dirzawa a fuska ko wani
bangaren da matsalar ta shafa.
==>
Qarin haske: idan
fuska ta kasance tana yin baqi a sakamakon yawan fita rana ko kuma canjin
yanayi, yana da kyau a kwaba ayaba, sannan a hada da zuma da kuma lemun tsami
sai a riqa shafawa a qalla sau biyu a rana na tsawon mintuna ashirin kafin a
kwanta barci.
==>
Sheqin fata: samin
fatar fuska mai sheqi, sai an dage da cin kankana da kuma kwabata da cokali
sannan a riqa shafawa a fuska ko jiki na tsawon mintuna talatin a qalla sau
biyu a rana sannan a wanke.
==>
Tsagewar lebe: Iidan
lebe na yawan tsagewa ko kuma bushewa, sai a samu man kwakwa da siga sai a dan
diga man kwakwa da sukari kadan, sannan a shiga dirza sukari a lebe na tsawon
mintuna biyu zuwa uku, sannan a wanke. A kasance yawan shafa man kwakwa a
leben.
==>
Gautsin fata: gautsin
fata na hana fata sheqi. Don haka, yana da kyau a kasance amfani da fiya da
ruwan lemun zaqi. A kwabasu waje daya sannan a riqa shafawa a waje mai gautsin
domin magance matsalar.
==>
Fesowar quraje: a kasance
ana amfani da ruwan qwai ban da gunduwar sannan a riqa shafawa a fatar fuska a kullum
na tsawon mintuna ashirin zuwa ashirin da biyar kafin a wanke sau biyu a rana
domin samun biyan buqata.
No comments:
Post a Comment