Yadda ake ‘pan cake’ din ayaba
Akwai hanyoyi da dama na sarrafa ‘pan cake.’
Kowace mace na da irin nata yanayin sarrafa girki, shi ya sa a kullum nake kara
tunatar da mu a kan cewa yana da kyau mace ta kasance mai sarrafa sabon abu a
kullum. Koda tuwo ne, yana da kyau a kasance ana canja na’ukan miya domin kara
wa abinci armashi da kuma kin fita ran masu ci. A yau na kawo muku yadda ake
sarrafa ‘pan cake’ din ayaba. A ci dadi lafiya.
Abubuwan
da za a bukata
·
Ayaba
·
kwai biyu
·
Madara
·
Bata
·
Sukari
·
Fulawa
Hadi
A samu na’urar markada kayan miya (blender),
sannan a yayyanka ayabar a ciki. Bayan haka, sai a fasa kwai biyu a ciki,
sannan a zuba bata (butter) kamar cokali uku zuwa hudu. Daga nan sai a zuba
madarar ruwa ko a kwaba da madarar gari da ruwa sannan a zuba. A zuba sukari da
garin fulawa kadan, sai a rufe na’urar a markada su, har sai sun yi laushi
sannan a sha.
A dora tukunya mara kama girki a wuta
(nonstick) bayan ta yi zafi, sai a rika debo kullun ayaba ana zuba shi ta irin
yanayin da ake so. Idan ya dan nuna, sai a juya dayan gefen domin shi ma ya
gasu. Sannan a kwashe. Za a iya cin wannan hadin da zuma ko da miya. Wannan
abincin an fi yin sa ne a matsayin abincin karyawa.
yayi kau
ReplyDelete