Muhammad
Abba Gana
Shafin
blogger yana daya daga cikin sanannun kuma manyan shafuka a yanar gizo wadda suke
taimakawa wajen rubutun ra’ayin kai, shafin blogger yana bayar da damar isar da
sakonni ta hanyar rubutu, hoto ko kuma hoto mai motsi wadda aka fi sani da
video a turance. A makonni da suka gabata munyi jawabi a bangarori daban daban
daya kama da:
- Meneneblogger da kuma amfaninsa
- Yaddaake bude shafi a blogger cikin sauki
- Yaddaake shiga shafin blogger
- Yaddaake chanza kallar rubutu a blogger da kuma
- Yaddaake saka rubutu (post) a shafin blogger
A
yau kuma Insha Allahu da izinin Allah zamu tattaunane akan yadda ake sa hoto
cikin rubuta wadda ke taimakawa wajen kara armashi ga rubutu sannan kuma yana
kara manufa ga rubutu.
Sa
hoto a blogger ba wani abune mai tsauri ba ko kuma abunne da zai dauki tsawon
lokaci ba, matakan masu saukin gaskene kuma kai tsaye.
Matakai Da Za’a bi Wajen Sa Hoto A Post A Shafin Blogger
1.==> Da
fari dai dole sai mutum ya shiga account nasa na blogger kafin yaje mataki na
gaba.
2.==>
Mutum zai je wajen da ake saka rubutu wato wajen post da mukayi bayani a nan sannan ya zabi daidai wajen da yake son sa hoton zai iya zama a farkon rubutu,
tsakiyar rubutu ko kuma a karshen rubutu ya dangana da yadda mutum yake so amma
a nawa shawaran zan iya cewa sawa a farkon rubutu shi yafi domin hakan zai
baiwa makaranta damar gane inda marubucin ko marubuciyar ta/ya dosa.
Idan
kuma ya kasance akwai hotuna da dama da ake son sawa, shawarana a nan shine ko
wani rubutu (post) na musamman ya kasance yana da hoto a farkon sa kamar yadda
muke yi anan Duniyan Fasaha idan akayi la’akari.
Sai
kuma sauran hotunan su biyo daga baya hakan zai taimaka matuka wajen fidda
rubutu sosai. Kuma zasu iya kasance a tsakiya ko kuma a karshen rubutu ya
dangana da manufar rubutun.
3.==>
Domin saka hoto a wajen rubutu a shafin blogger sai a danna wannan dan karamin
abun wadda ke dauke da tambarin hoto.
4.==>
Akwai hanyoyi daban daban wajen saka shi hoto a blogger amma a wannan rubutun
zamu takai tane ana farin wato ta hanyar daurawa.
Domin
daura hoto daga cikin wayar salula ko kuma cikin kwanfuta sai a danna inda aka
rubuta “CHOOSE FILES” sai a zabi hoton da ake son daurawa bayan ya fito sai a danna kan hoton
sannan a latsa “ADD
SELECTED” hakan zai bayar da dama hoton ya shiga inda ake rubutun.
In
dai yadda ake son daura hoton yayi kuma abinda ake son rubutawa ya kare sai a
danna mabullin “PUBLISH” domin tabbatarwa.
Amma kuma in har rubutun bai kare ba
za’a iya bari sai an kammala kafin a danna, sannan kuma hoton da aka daura yana
nan daram face an gogesa domin muddin mutum ya latsa mabullin “PUBLISH” din tamkar
an gama komai ne.
Yadda Za’a Goge Hoton Da Aka Sa A Post A Shafin Blogger
1.==>
Da fari mutum zai danna hoton da yake son gogewa
2.==>
Wasu zabi zasu fito masa sai mutum ya latsa inda aka sa "REMOVE".
3.==>
Shikenan Hoton zai tafi muddin an bi matakan dana zayyano a baya.
Wannan shine cikakken matakan da ake
bi wajen saka hoto a cikin rubutu a shafin blogger da kuma yadda ake gogesa
cikin sauki. Dafatan wannan rubutun ya taimaka matuka ga masu amfanin da shafin
blogger. Shin an gwada hanyoyin da muka zayyano daya gabata kuma baya aiki? Za’a
iya tuntubanmu tanan domin Karin bayani ko taimako. A huta Lafiya!
-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:
Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan
Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
No comments:
Post a Comment