Assalamu
Alaikum barkanmu da war haka barkanmu da sake saduwa da ku a cikin sabon shirin
namu wadda ke zuwa muku kai tsaye daga mujjalar Duniyan Fasaha. Zaiyu kana daya
daga cikin wayanda suke fuskanta kalu bale wajen rashin tashiwar kwanfuta a kan
lokacin daya kamata wadda ake masa lakani da slow booting a turanche.
A
hakikanin gaskiya akwai matsaloli bila adadin dake sa rashin tashiwar kwanfuta
a kayataccen lokacin daya kamata, wayan nan matsalolin sun hada da yawan wucin
gadin fayil (Temporary files) ko kuma kwanfuta yana dauke da virus.
ko
ma me ya haddasa rashin tashiwar sa akan lokaci insha Allahu yau zamu tattauna
ne a kan yan wasu hanyoyi da za’abi wadda zai taimaka matuka wajen shawo kan wannan
matsalar. Domin shawo kan wannan matsalar ga wasu matakai da za’a bi kamar
haka:
==>
Mataki na Farko: Dole a tayar da ita kwanfuta ya kasance
yana kunne.’
==>
Mataki na Biyu: za’a latsa kan Windows menu sannan za’a bincika
“Run” ko kuma za’a iya yin hakan ta hanyar dannan WINDOW BUTTON da kuma R (WIN
+ R) a lokaci guda. Zai bude wani dan karamin akwati wadda ke bada damar duba
abu ta hanyar nema wato searching a turance.
==>
Mataki na Uku: Bayan dan karamin akwatin (popup window)
ya budu
sai a rubuta “Msconfig” sannan a latsa ma dannin enter a keyboard, ko
kuma a latsa “Ok” wadda ke rubuce a karkashin karamin akwatin
Wadda hakan zai
bada damar kai mutum izuwa ga wani shafi.
==>
Mataki na Hudu: za’a danna na hudu a cikin jerin ababen da
aka lissafo ko kuma na kusa da karshe wadda ke dauke da “Startup” a rubuce,
bayan
an danna; ga masu amfani da windows 7 zai kawo jerin sunayen Mahajan da suke
buduwa yayin da kwanfuta ke kokarin tashi.
Ga
masu amfani da windows 8 ko kuma windows 10 zai kawo dan wani gajeren sako
dauke da mahada (link) a rubuce “Open Task Manager” sai a latsa kai
hakan
zai bada damar kawo jerin sunayen Mahajan da suke buduwa yayin da kwanfuta ke
kokarin tashi.
Abinda
mutum zaiyi anan shine ya rage adadin mahajar da suke buduwa yayin da kwanfuta
ke kokarin tashi za’a yi hakan ne a window 7 ta hanyar cire alamar maki dake
dauke a kusa da kowani mahaja da ke kunna kansa.
Misali: na dakatar da
mahajar Adobe Reader daga tashi wadda amfanin sa shine bude PDF file haka
zalika na dakatar da mahajar Wondershare daga tashi domin ina aiki dashi ne
yayin da zanyi aiki wani hoto mai motsi wato video a turache.
Ga
masu amfani da window 8 ko kuma window 10 za’a iya dakatar da mahajar daga
tashi ta hanyar zaban mahajar sai a latsa madannin dama (right click) sannan a
zabi “Disable” daga jerin zabin da aka bayar.
Abin Kula: Lallai mutum yasan abinda zai dakatar daga
cikin jerin sunayen mahajar da suka fito, abinda nake nufin anan shine idan
adadin na mutum ya ninka nawa da ake gani anan zai iye chire wasu wadda ya
tabbatar shine ya saka a cikin kwanfutansa domin akwai wasu mahajar da ke zuwa
tare da ita kwanfutan sabili da rashin tashiwar wayannan mahajar kan janyo
matsala babba ta bangaren lafiyar ita kwanfutan.
==>
Mataki Na Biyar: Bayan mutum ya kammala cire mahajar da ya
tabbar tashiwarsu bashi da wani inganci sai ya latsa madannin “Apply” wadda ke rubuce
a dan kasa kusa da karshe
sannan ya sake dannan madanni da ke dauke da “Ok”
wadda shine farko a layin dake karshen shafin.
Kwanfutan zai bayar da shawarar sake
yi (a Kashe sannan a sake kunnawa) wato “Reboot” a turance sai ayi hakan.
Insha
Allahu za’a sami chanji muddin an bi matakan dana zayyano daidai. Allah ya
taimake mu gaba daya Ameen!
No comments:
Post a Comment