Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Cikkanen Bayani Game Da Amfanin gurji a fatan Dan Adam

Cikkanen Bayani Game Da Amfanin gurji a fatan Dan Adam

Gurji ba abunci kadai bane, Gurji ba abun abinci bane ko kuma abun marmari kadai ba shi gurji masana kimiyya sunce gurji yana dauke da sinadaran magance gautsin fata sannan yana taimakawa wajen sanya fata sheki da laushi cikin sauki sannan kuma a yan kankanin lokaci.

Karanta: Cikkakkun Hanyoyi shabiyar (15) da za ki bi wajen lura da fatarki Cikin Sauki


Kashi casa’in da biyar bisa dari na gurji na dauke da ruwa don haka yana da kyau a kasance wajen cin gurji lokaci zuwa lokaci domin samun cikakken lafiyar jiki da kuma maikon da ke toshe magudar gumi misa wasu dalilai wayanda mukayi bayani a baya wadda hakan yakan haifar da fesowar kuraje wadda daga bisani in ba’ayi sa’a ba sai su koma tabo wadda sai an dage matuka kafin a rabu da su.

Karanta: "ILOLIN SHAFE-SHAFEN BLICING GA MATA"


Wannan kayan lambun na taimakawa wajen rage kiba ga mace ko na miji idan har an kasance cin sa shi kadai da kuma rage cin abinci masu nauyi wadanda ke gina jiki. Insha Allahu yau a mujallar Duniyan Fasaha zamuyi bayanin amfanonin shida (6) da gurji keyi a fatan jikin dan adam ba ina cewa iya karsaba a’a akwai wasu da dama amma na tsamo shida wayanda sune manya daga cikinsu sun hada da:   

1.==> Domin rage kiba ko tumbi: In an kasance an zama tamkar bujumi mai ciki sai a samu gurji sannan a fere bawonsa sannan a yayyanka shi kanana sannan a zuba a na’urar markade a markada shi sosai sai a tace ruwansa sannan a zuba cokali biyu na zuma a ciki sannan a zuba a kwalba a jijjiga kwalbar sosai . Sannan a hada da ruwan lemun tsami da citta sai a rika sha yana rage kiba da tumbi.

2.==> kurajen fuska: In fuska ya bace sai a markada gurji da ruwa zalla bayan an fere bawonsa sannan a samu auduga a rika shafawa a fuska sau biyu a rana ko sau uku in ya samu domin magance kurajen fuska da kuma sanya sulbin fata.

Karanta: Abinci Kala 6 Da Ke Tsayar Da Gudawa Cikin kankanin Lokaci


3.==> Hasken fata; Ana so a kara hasken fata? a markada gurji sannan a matse ruwan lemun tsami a cikin sai a rika shafawa a fuska da wuya kamar sau biyu a rana ya yi a kalla mintuna goma sha biyar zuwa ashirin kafin a wanke a kullum ban bada shawarar a kwanta dashi ba domin yin hakan zai iya kawo wata matsala.

4.==> Kodewar fata: Fata duk yabi ya kode saboda yawan shiga rana kodai makamancin haka? A markada gurji sannan a zuba kindirmo da garin alkama cokula biyu sannan a kwaba sosai a rika shafawa a inda fatar ta kode sakamakon kunar rana ko yawan shiga rana. A bari a fuska na tsawon mintuna goma sha biyar kafin a wanke shima dai bandai bada shawaran kwanciya dashi ba.

5.==> Yankunewar fata: Mutum dan shekara sha wani abu amma yabi ya zama tamkar tsoho dan shekara dari da wani abu? a markada ruwan gurjin sannan a samu kwai a cire kwanduwar ayi amfani da farin ruwan a ciki sannan a matse lemun tsami a kwaba a rika shafawa a wajajen da fatar ta yankune. Sannan a bari na tsawon mintuna talatin kafin a wanke. Ana so a rika yin wannan hadin kamar sau biyu a rana a kullum. Insha Allahu za’a ga chanji cikin yan wasu kwanaki.

Karanta: MAGANIN CIWON MARA LOKACIN AL'ADA


6.==> Domin samun gashi mai tsayi: Uwar daki ko Yan mata ana so a nuna musu akwai alkairi? a markada gurji da ruwa sannan a tsaga gashin kai a shafa a fatar har a cikin gashin kai ya ji sosai. Sannan a samu leda a rufe kan na tsawon mintuna talatin kafin a wanke da man wanke gashi. Yin hakan na dada tsayin gashi a kai.


Wayannan sune cikekken bayani game da amfanin Gurji a fatan dan adam, shin akwai wani babban amfanin gurji da ban Ambato a cikin wannan kasidar ba? Za’a iya taimaka mana ta hanyar rubutawa a kasa (wajen comment) ko kuma ta hanyar rubuto mana ta hanyoyin da za’a iya samun mu. 

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Za'a iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan
Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *