"ILOLIN
SHAFE-SHAFEN BLICING GA MATA BY MUHAMMAD ABBA GANA"
Shafe-shafe yana da illoli
masu tarin yawa musamman ga ’ya mace.
1. Na farko yana canjawa mace launin
fatarta. Fatar da ba a yiwa shafe-shafe, ita take bada kariya
daga cututtuka da sauran kwayoyin da suke yiwa fata barazana. Fata ta asali
tana ba mace garkuwa daga zafin rana.
Bayan
mace tayi bilicin zata kasance cikin yawan laulayi, bazata iya yawo a rana ba
domin zataji kamar ana kwara mata ruwan zafi, saboda tarasa fatarta ta asali
datake bata garkuwa daga zafin rana.
2. Abu
na biyu shi ne, mai bilicin bazata sami kariya daga cutar daji ba wato
(Cancer), wadda cuta ce mai ban tsoro da wuyar sha’ani, ba kasafai aka fiya
samun maganinta ba.
Cuta
ce wadda take kama sassan jikin mutum, yawanci akan yanke gabobi ko wuraren
data kama. Duk wannan yasamo asali ne a sakamakon bilicin.
3. Mai
bilicin za ta rasa kuzari, Idan kafin ta fara bilicin tana iya yin aiki na
tsawon sa’a uku bata gaji ba, to yanzu ba lallai bane ta iya na sa’o’I biyu, hakan
ya haifar mata da nakasu, maimakon a nemo kiba sai aka iske rama.
4. Ba
a nan kadai illar shafe-shafe ta tsaya ba, akwai illoli masu tarin yawa da kuma
tsoratarwa. Misali bilicin na jawo gyambon ciki abin da aka fi sani da olsa
(ulcer) wanda mafi yawanci akan dauketa a matsayin rashin cin abinci ke kawota.
Daga ciki akwai kassara dukkan wasu sassan jikinki masu amfani walau wadanda
ake gani a zahirance da kuma wadanda ba mu iya gani, kamar irinsu:
·
Hanta.
·
Qoda.
·
Hunhu da sauransu.
Wadannan duk suna tagayyara
ne sakamakon illar bilicin. Da fatan za'a kiyaye.
No comments:
Post a Comment