Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Wasu Abubuwa Da Mukeyi Wadda Ke Bude Kofofin Satar Account Namu Na Facebook

Wasu Abubuwa Da Mukeyi Wadda Ke Bude Kofofin Satar Account Namu Na Facebook

Satar account a facebook wadda aka fi sani da hacking a turance ya zama tamkar ruwan dare domin kuwa yana da matukar wiya ayi kwana biyu ba tare da ganin wasu alamun sacewar account ba, idan ba’a yi wa mutum ba za’ayi ma dan uwansa ko kuma wani daga cikin abokai da ake dasu a facebook. Sau da dama mutane su kanyi korafin wannan matsalar wasu kuma su kanyi tambaya shin kamfanin facebook na sane kuwa da wannan matsalar da ake fama da ita?

Idan suna sane da shi maisa ba su daukan matakai wajen magance ta? Kuna tare da jikan marubuta Muhammad Abba Gana daga mujallar Duniyan Fasaha kuma Insha Allahu a wannan makon zanyi cikakken bayani akan wannan matsala sai de yau a dan dakanceni domin kuwa rubutun zaiyi matukar tsayi, yin hakan ne kawai zai bada damar fahimtar gurbatattun hanyoyin. 

 

Karanta: Cikkaken Bayani Yadda Ake Samun Kudi A Yanar Gizo (Internet) Cikin Sauki

 

Kashi chasa’in bisa dari na wannan matsalar na faruwa ne bisa wasu abubuwa da muke aikatawa ba tare da cikakken sanin illolin da ke tattare da ita ba, sannan mukan jingina matsalar ga ita kamfanin facebook. Ba tare da bata lokacin ba bari muje ga wasu daga cikin manyan matsalolin da mukeyi;

1.==> Amfani Da Numbobin Sirrin Masu Sauki (Lose Password): Wannan yana daya daga cikin abubuwan da mukeyi a yau da kullum domin gujewa mantuwa, mukan sanya wasu lambobin sirrin irin su 12345, 123456789, 0000, ko kuma lambar wayarmu domin sawwa kema kanmu, yin hakan ke ba masu tsageru damar satar account namu cikin sauki domin kuma a duk lokacin da suka yunkura wajen satar account akwai matakai bila adadin da suke amfani da ita  misali irin amfani da wasu manhaja da kuma kwanfuta amma da farko sukan fara amfani da wanann salon domin kuwa sun san cewar mafi yawancin aqasarin mutane numbobin sirrinsu baya wuce hakan.

Yana da kyau a san cewar lambar waya na fitowa a profile na mutum a lokacin daya bude account a dandalin sada zumunta na facebook fa ce ya san yadda ake boyewa muddin ba’a boyeba zasu iya ganin lambar sannan kuwa zasu iya jarrabawa domin cin ma manufa. 

 

Karanta: Yadda Za’a Duba Ko Katin Kasa (National I.D) Ya Fito

 

Domin gujewa wannan matsalar za’a iya boye lambar waya da aka daura a account amma abinda ya dace anan shine a saka lambobin sirrin mai tsaurin gaske misali “09039Abbagana@Abba453@DuniyanFAsaha!#” yin hakan zai taimaka matuka domin kuma ko ita kwanfuta bazata iya chanko wani abu maka mancin haka ba.

2.==> Amfani Da Adireshin Da Bana Kamfanin Facebook Ba: A koda yaushe kamfanin sada zumunta ta facebook na yawan tsawatarwa a kan wannan matsalar amma saboda karanchin ilimin yanar gizo da muke fama da ita mutane da dama sukan tsinchi kansu cikin wannan tarkon. Yana da matukar amfani mu san da cewar addreshin facebook shine www.facebook.com ko www.fb.com sune kadai ingantaccen addreshin da ake amfani da shi wajen shigan account amma saboda sabbin fasahohi kamfanin facebook ta samo wasu karin addreshin irinsu “web.facebook.com” da kuma “m.facebook.com” sannan suna aiki ne bisa na’ura da ake amfani da ita.

Yana da kyau mu lura da wasu addereshin da ake turo mana a whatsapp ko wasu dandalin sada zumunta da muke amfani dasu. Wasu daga cikinsu ba addreshin kamfanin facebook bane wasu ana kiransu sub-domin ne misali www.facebook.com/guidetricks.com duk sanda aka ci karo da wani addreshi maka manchin haka wato an saka facebook tare da Karin wani addreshi na musamman a gaba to kada a kuskura ayi amfani da shi wajen shigan dandalin sada zumunta na facebook domin kuwa duk lokacin da aka latsa wannan addreshin zai kai mutum zuwa wani shafine na daban amma yana matukar kama dana kamfanin facebook sannan zasu bukachi email addreshi, lambar waya da kuma lambobin sirrin muddin ana sawa boom! Ka basu damar chin karensu babu babbaka. Yana da kyau mu ringa lura da addreshin da muke amfani dasu domin kaucewa matsalolin.   

3.==> Amfani Da Lambar Sirri Iri Daya: Yana da kyau a duk lokacin da zamu bude account a wani shafi na musamman ya kasance mun sanya lambobin sirri na daban domin kuwa wasu lokutan akan iya samu matsala a wani shafin, idan wanann shafin ya daina aiki ko kuma wani rashin sa’a ya auku idan wayan nan gurbatattun mutanen suka samu damar sanya hannunsu akan bayanai naka a wannan shafin daya sami matsala zasu iya amfani dashi a wasu shafukan irin su facebook domin dauke account din saboda a kowani lokaci tunaninsu lambar sirrinka zai iya kasance abu daya hakan ke basu karfin gwiwa wajen jarrabawa.

4.==> Buga Wasu Wasanni A Facebook: Sau da dama nakan ga mutane suna buga wasu wasanin irinsu “Yadda suran yaronka zai kasance shekaru masu zuwa”, “Shekarun da zakayi aure ko kuma zakayi arziki”, “Yadda fuskar mijinki zai kasance ko kuma yadda fuskar matarka zata kasance bayan kayi aure a shekaru biyu masu zuwa” ba tare da sanin illolin dake tattare da wayan nan shafukan ba. 

 

Karanta: Yadda Za’a Cire Tallar Manhaja Da Suke Fitowa A Menu Na Salulan Android

 

A duk lokacin da mutum ya ziyarci shafukan da suke dauke da ire iren wasannin nan sukan bukaci mutum ya tura zuwa account nasa dake facebook kuma za’a iya yin hakan ne ta hanyar shiga account na facebook daga wannan shafin. Abinda ke faruwa anan shine duk lokacin da mutum ya shiga account nasa daga wannan shafin da yake buga wasan; shafukan suna daukan bayanan mutum sannan kuma zasu iya amfani dashi a duk lokacin da bukatan hakan ya taso. Saisa yana da kyau a daina buga ire ire wayan nan wasannin domin kuwa basu da wata ma’ana, fa’ida sannan kuma basu dauke da alkairi ko kadan.

5.==> Shiga Account Da Wani Na’ura: A wasu lokutan mukan tsinchi kanmu a wani yanayi na dole da sai mun shiga account namu na dandalin sada zumunta na facebook ta hanyar amfani da wayar wani ko wata ko kuma ta hanyar amfani da kwanfuta a café kona wajen aiki. A duk sa’an da muka shiga account namu da wani na’ura kundin bayanai namu na zama a cikin wannan na’uran, duk lokacin da wani yayi niyan aikata wani abu tare da account namu zai samu cikin sauki, muddin mutum bayyi logout ba akwai manhajoji bila adadin wadda zasu iya taimaka wajen nemo lambobin sirrin da akayi amfani dasu wajen shigan account din. Saisa yana da matukar amfani mu ringa fita (logout) daga duk wani na’ura da mukayi amfani dashi muddin ba namu bane.

6.==> Amfani Da Kowacce Browser: Tabbas akwai browsers bila adadin wadda aka kirkira haka zalika ko wani waye war gari ana kara fitar da wasu sabbi. Yana da kyau mu san cewar duk wani browser da muke amfani dashi a wasu lokutan sukan zama tamkar kana tafiya tsirara ne domin kuwa duk wani abu da ka aikata ana kallonka; duk wani lambar sirri da ka saka ana iya daukawa ba tare da sanin ka ba. Shawarar anan itace ayi taka tsantsan da wasu manhaja da muke amfani dasu wadda bamu san asalin su ba, zamu iya amfani da wasu sanannu kamar chrome, opera, uc browser, Firefox ko Mozilla Fire da dai makamantan su.

 

Karanta: Yadda Za’a Fita Daga Duk Wani Tsari Na Mtn Da Suke Cire Kudi

 

Wasu kenan daga cikin manyan abubuwa da mukeyi wadda ke bude kofofin satar account namu na facebook shin akwai wata hanya mai matukar hatsari wadda aka sani bamuyi bayani anan ba? za’a iya turo mana ta hanyoyin sada zumuntanmu na facebook, twitter, instagram, youtube da kuma whatsapp. Haka zalika za’a iya tuntubanmu ta email addreshinmu. Allah shi karemu dukka. Ameen!!



mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *