Lokaci zuwa lokaci mukanyi ababe da dama, a
ranmu mukan ji daidai ne wadda kuma a hakikanin gaskiya ba daidai bane wasu
lokacin son raine wasu lokutan kuma rashin sani ne. A mafi yawancin lokutan
mukan biyewa ra’ayinmu ne ko kuma ita zuciyarmu wadda hakan kan zama mana
matsala a nan gaba ko kuma ta sanya mu cikin kunchi da la haula.
A zamanin da muka tsinci kanmu a yanzu na Fasaha,
mutane da dama musamman masu amfani da wayar taba ka latsa wadda aka fi sani da
android a turance, za ka same su suna amfani da wata mahajar waya (Application)
da ake kira da Launcher a turance.
Karanta: Waya na nuna alamar shigowar kira amma baya nuna wajen daukawa – Yadda za’a magance matsalar cikin sauki
Shi Wannan mahajar wadda aka fi sani da
application a turance ana amfani ne da shi domin kayata cikin fuskar waya da
kuma canza masa wasu daga cikin siffofin ko kuma sura da take fitowa da su
misali: yanayin yadda hoton saman screen din wayar yake, kallar rubutu, surar mahajar
waya, launi da dai sauransu.
Duk da cewar wadannan mahajar (applications)
suna da amfani ta wani bangaren misali wajen kayata waya, akwai wasu illoli da
dama tattare da shi wadda ke taba lafiyar waya irin su uwar wato kwakwalwa, wadda
kuma ba kowa ne yasan da wadannan illolin ba wasu kuma sun sani amma saboda
biyewa ra’ayi zuci suna kan amfani dashi.
A cikin wannan kasidar namu insha Allahu yau
Duniyan Fasaha bisa la’akari da tayi zamu kai hangene ne izuwa ga illolin shi
Launcher da kuma yadda yake taba lafiyar waya ta hanyar nuna wasu alamomi.
1. Kwayar
Cutar Na’ura (VIRUS): Sanin
kowa ne akwai masu kawo barna a bangaren fasaha wadda aka fi sani da hackers a
turanche wadanda kullum burinsu shine suga sun lalata abubuwan mutane ta hanyar
yada virus cikin fasaha wacce zata ita haddasa matsala ga kwamfutoci, ATM, wayoyin
salula, memory da dai sauran abubuwan fasaha na zamani.
Karanta: Dalilin da ke sa waya taqi cika da wuri wajen charge ko kuma ta sauka da wuri
Sukanyi
Nazari sosai sannan su zayyano abubuwan da mutane suka fi shagala akai ta
hanyar yin download dinsa, sai su dauki manyan daga ciki sannan sai su gurbata
shi da virus ko kuma trojan ta yadda duk wadda yayi download wannan abun ko
kuma aka tura masa to shikenan wayarsa ko kwanfutarsa ta auri matsala wato
wannan virus din. Sannin kowa ne akwai illoli da dama tattare da ita virus
wadda ke haddsawa kama daga lalata wayar salula, chanza tunanin wayar salula,
sanya masa muga yen dabi’u da makamantansu.
2. Talla
(Adverts): Duk sa’an da mutum ya
saukar da wannan mahajar (application) ko kuma aka tura masa idan yazo da
rashin sa’a mutum zai fahimci cewar daga lokaci zuwa lokaci akwai wasu talla da
waya zai ringa nunawa mutum ya rasa ta ina wayannan abubuwan sukazo, a mafi
yawancin lokutan yakan iya dakatar da mutum daga wasu ayyuka da yake son yi
wanda hakan ya faru ne bisa dalilin saukar da wannan mahajar (application)
yakan dauki lokaci mai tsaho kafin mutum ya magance wannan matsalar.
3. Shan
Chaji (Consuming Battery Life): Da yawa daga cikin mahajar (Application) launcher suna zuwa da nauyin
tsiya wadda hakan yakan dauki lokaci kafin ya fara aiki dai dai, haka zalika
idan ya fara aiki yana yi a kowani lokaci a kwakwalwar waya wadda aka fi sani
da Running in Background a turance wadda hakan na bukatan wuta wajen gudanar
dashi. Hakan ke sanyashi amfani da battery din waya ba tare da neman izinin mai
shi ba.
Wasu
lokutan za’a ga cewar wayar na daukan zafi, duk da cewar akwai masu abubuwa
dake sa waya zafi amma wannan na daya daga cikin manyan ababen dake sa ita
wayar zafi sabili da yana aiki tukura a kan waya ba tare da numfasawa ba.
Karanta: YADDA ZAKA MAGANCE SHANYEWAR MB AKAN WAYAR KA NA ANDROID
4. Tsayawa
lokaci Zuwa Lokaci (Hooking): A duk lokacin da mutum ya dora mahajar Launcher sannan kuma nauyinsa ya
kasance sama da wadda wayar salula ke zuwa dashi ko yazo dashi za’a ga alamar cewa
a duk lokacin da mutum ya danna madannin home (na tsakiyar wayarka wanda ake minimizing
da shi) za’a lura da cewar ya nuno duk wasu launchers din da ke cikin wayar sun
fito domin mutum ya zabi wacce yake bukata.
A nan abin
da ke faruwa shine, wayar zata rasa wane salo zata yi amfani dashi, domin ko
wace mahajar launcher akwai yanayin yadda aka tsara shi. Wannan kan iya jaza
wayar ta rikice ko kuma ta rasa ma hankalin gaba daya, sanadiyyar hakan sai ka
ga waya tayi hooking, ma’ana ta tsaya cak, ta ki gaba ta ki komawa baya har
zuwa wani lokaci.
Wani
lokacin ma wayar ta kan dauke ne baki daya sai kuma ta kunna kanta ko kuma wasu
lokutan sai an kunnata. Idan mutum nasa yazo da rashin sa’a zai tsaya ne chak
sai mutuum ya cire battery ya kuma dawor da ita. Wannan kan iya sanya wani banagare
na wayar ya sami babbar matsala bisa mutuwa ba tare da ka’ida ba.
Dukkan wayannan illoli guda hudu da mukayi
jawabi akansu na tattare da amfani da mahajar Launcher wadda wasu lokutan kan
iya kawo babbar matsala ga lafiyar wayar
salula, wadda hakan yakan iya kamawa lallai sai anyi wa wayar flashing domin
komawa hayacinsa.
Karanta: Madannai uku na wayarka Android sun daina aiki? Ga cikakken bayani yanda zakayi aiki ba tare dasu ba
Babban Shawara anan shine, idan lallai ana
bukatar yin amfani da mahajar Launcher, to a tabbatar da cewar bata wuce guda
daya ba a cikin wayar salula, domin tara mahajar lauchers kamar kasuwan kifi a
waya guda ba abin ado bane face ya janyowa mutum matsala babba. Idan kuma mutum
ya kasance kamar kawu nane mai taran aradu da kai to babu shakka zai iya saka
adadin son ransa. Domin tabbatar da cewar
Launcher bata dauke da Virus, ayi downloading dinsa kai tsaye daga Google Play
Store.
No comments:
Post a Comment