Kowane
bangare na jikin bil adam yana neman kulawa na musamman domin kara masa kargo
da kuma inganchi amma akwai wasu wajajen da suke bukatar kulawa na matuka,
gashi na daya daga cikin wayan nan waja je, komin karanchin sa komai yawansa
gashi yana bukatar wankewa lokaci zuwa lokaci ba w yadda wasu suka kasance
sunayi ba, da sabulun wankin gashi wanda ya dace da irin gashin da kike dashi
(za a ga bayanin haka a rubuce a jikin sabulun) Duk da cewa mata ba su fiye son
karanta jikin ba haka zalika wasu basu fiye wanke gashinsu ba saboda gudun kada
ya zube, amma akwai bukatar akalla yaga ruwa ko sau daya a cikin makonni biyu.
Tun
kafin a wanke gashin, idan akwai amosani, ya kamata a kankare shi sosai, haka
zalika masu kazzuwa da kuma kaska yana da kyau a sami magani don kada sai an wanke
ya rika tasowa yana bata gashin. Sannan akwai bukatar a nemi maganin amosani,
kaska na musamman.
Bayan
wanke gashi sai a bar shi ya ya sha iska na yan masu mintuba, ba a son taje
jikakken gashi domin yin hakan yakan haifar da wata matsala, sannan sai a shafa
masa mai wanda ya yi dai dai da gashin. Idan kitso kika fi so, bayan kin wanke
kin shafa masa mai sai ki rangada wanda kike so akan lokaci ba sai yayi tsami
ba.
Wato a barsa bayan an wanke har tsawon mako guda ko fiye da haka ba tare da
anyi kison ba haka zalika kada ya wuce makonni biyu ba tare da kin kwance ba.
Idan kuwa baki son kitso, a kullum dole ne ki zauna ki taje gashin tare da
shafa masa mai daya kamata, sannan sai ki daure shi da madaurin gashi (Ribbon)
dai dai yadda kike so.
Idan
da hali, Zai yi kyau duk bayan wata daya kije salun ki yi masa abin da ake kira
steaming, wannan ne zai hana shi zubewa. Idan kuma ke mai sha’awar yi wa gashi
shamfo ce (retourching) shi ma akwai bukatar ki rika maimaitawa a duk bayan
watanni biyu. Idan kuma gashinki mai karfi ne za ki rika yi kamar sau daya a
wata.
Yawan
yin shamfo a cikin kwanakin da suka gaza wata guda, masana sun ce akwai yiwuwar
zubewar gashi saboda yawan kone shi da ake yi. Bayan duk kin gama wadannan
akwai turaren gashi da za ki rika feshe gashin ki da shi, don ya rika sa shi
kamshi na musamman kuma ya kamata ki sani cewa mayukan da ya yi wa wata aiki ba
lalle ya yi miki ba, kowa da kalar sa haka zalika kowa da kallar fatarsa don
haka ki kula sosai wajen zabar wanda zai dace da naki gashin.
No comments:
Post a Comment