Amfanin Nonon Akuya Guda 8 A Jikin Bil Adama
Premium Times ta rawaito cewa hukumar bada
shawara akan bunkasa ayyukkan noma na Najeriya NIFAAS ta yi kira ga mutane da
su yawaita shan nonon akuya saboda kara lafiyar jiki da yake yi.
Hukumar ta bayyana cewa Nonon Akuya yafi na
saniya amfani a jiki.
Amfanin 8 da nonon akuya ke yi a jikin dan
Adam sune:
1.==> Nonon akuya na dauke da sinadarin ‘Protein’
da yafi na nonon Saniya. Yana taimaka wa jiki girma yadda ya kamata musammam ga
yara masu tasowa.
2.==> Yana dauke da sinadarin ‘Amino Acids’ da ke
kara garkuwan jikin mutum.
3.==> Yana dauke da ‘Vitamin A’ da ke kara karfin
ido.
4.==> Yana dauke da ‘Potassium’ da ke kare mutum
daga kamuwa da cutar shanyewar gefen jiki, kara karfin kashi, kare mutum daga
kamuwa da cutar hawan jini da makamantan su.
5.==> Yana dauke da ‘Phosphorous’ wanda ke taimakawa
wajen fitar da ababen da jiki ba ya bukata kamar zufa, fitsari da bayan gida.
6.==> Nonon akuya na da saurin nika abinci a cikin
mutum.
7.==> Yana dauke da ‘Magnesium’ da ke taimakawa
mutane dake fama da rashin barci.
8.==> Yana dauke da sinadarin ‘Manganese’ da ke
kara karfin kashi.
No comments:
Post a Comment