Tare Da
Muhammad Abba Gana
Shin yaya zaki lura da fata cikinkin sauki? Babu shakka ba wata haifaffiyar ya mace da ba ta so a ce fatarta tana sheki, yalki da kuma kyan gani; babu kuma macen da take so a ce fatarta ba ta da kyau ko daukar hankali. Amma kuma wace matakai za’a bi wajen lura da fatar cikin sauki yakan zama matsala.
Muhammad Abba Gana
Shin yaya zaki lura da fata cikinkin sauki? Babu shakka ba wata haifaffiyar ya mace da ba ta so a ce fatarta tana sheki, yalki da kuma kyan gani; babu kuma macen da take so a ce fatarta ba ta da kyau ko daukar hankali. Amma kuma wace matakai za’a bi wajen lura da fatar cikin sauki yakan zama matsala.
Hakan ya sanya mata da yawa ke kashe makudan
kudade wajen lura da fatar jikinsu ko ta fuska ta hanyar amfani da magunguna
asibiti. Da yawa daga cikin mata kuma sun fada tasku sakamakon amfanin da
mayukan da suke da sinadarai, wanda a maimakon kwalliya ta biya kudin sabulu
sai su buge da da-na-sani. Wannan dalilin ya sanya Duniyan Fasaha ta taho miki
da Cikkakun hanyoyin sha biyar (15) da za ki bi wajen lura da fatarki ba tare
da tararradin ko fatarki za ta gamu da wata matsala ba. Ga hanyoyin kamar haka:
Cikkakkun Hanyoyi shabiyar (15) da za ki bi wajen lura da fatarki Cikin Sauki
1.==> Ki
samu kurkum sai ki daka, daga nan sai ki hada da dakakkiyar alkama, sannan
ki hada da man zaitun. Daga nan sai ki shafa a fuskarki ko a jikinki. Bayan awa
biyu ko uku sai ki wanke fuskarki ko jikinki da ruwa mai dumi. Hakan yana cire
kwayoyin cutar da ke makale a kofofin fata.
2.==> Shan
ruwa mai yawa. Amfanin shan ruwa ga jikin dan adam yana
da yawan gaske. Duk da cewa a lokacin sanyi mutane ba su fiye son shan ruwa ba,
amma hakan babbar hanya ce wajen taimaka wa fatarsu ta kasance tana sheki
tsawon lokacin hunturu. An so mutum ya sha ruwa kimanin lita biyu zuwa uku a
rana. Sai dai wannan bai hada da shan shayi ba, a maimakon haka an so mutum ya
yawaita shan lemo.
3.==> Ki
samu karas sai ki markada, daga nan sai ki shafa a fuskarki ko jikinki.
Bayan awa biyu sai ki wanke da ruwa mai dumi. Yin hakan zai sanya jikinki ya
rika haske da kuma daukar hankalin duk wanda ya kalle ki.
4.==> Man
kadanya: tun yanzu ne yakamata a fara amfani da man kadanya a fata. Yin
hakan kamar rigakafi ne domin magance matsalolin fata. Idan fata ta fara
datsewa sakamakon sanyi, dole ne a yawaita shafawa domin man kadanya na dauke
da sinadarai masu warkar da cututtukan fata.
5.==> Ana
so a rika yawaita goge jiki ‘scrubbing’ wannan shi zai sa duk
wata matacciya da busasshiyar fata ta fita tare da ba wa sabuwar fata wuri don
tofowa.
6.==> Ki
samu lemon zaki sai ki yayyanka, daga nan sai ki markada. Bayan nan sai ki
shafa a fuska ko a jikinki. Wannan zai sanya miki laushin fata.
7.==> Shafa
mai akan lokaci, mun san yadda jiki yake saurin bushewa
saboda kadawar iska. A duk lokacin da aka yi wanka yana da kyau a shafa ma tun
a bandaki lokacin da dan ragowar danshi a jikin fatar.
8.==> A
zabi mai da ya dace da lokacin sanyi, ma’ana mai wanda ke da
maiko wanda zai sa fata ta kasance cikin danshi na tsawon lokaci. Duk wani mai
da zai zama ya sa fata tauri ba shi da amfani a wannan lokaci na sanyi. A
wannan lokaci amfani da man kadanya ko man zaitun yana taimakawa fata kwarai da
gaske.
9.==> ki
gauraya ruwan Rose Water da kuma ruwan lemon tsami. Ki shafa a fuskarki ko
jikinki. Yin hakan zai cire tabon da yake fata ko fuska, sannan yin hakan zai
sanya fata ta yi laushi da danshi.
10.==> Kaushin
fata: idan an kasance ana da kaushin fata, dole ne a dunga sanya man
‘glycerin’ a cikin man shafawa. Koda alwala akayi yana da kyau a yawanta shafa
man domin samun saukin lamarin.
11.==> ki
samu madarar shanu wacce ba a dafa ba, sai ki samu gishiri da kuma cokali
biyu na ruwan lemon tsami ko ruwan jus din lemon tsami, sannan ki gauraya
sosai. Bayan nan sai ki samu auduga ko tsumma mai tsabta sannan ki rika dongala
kina gogawa a jikinki ko a fuskarki. Bayan nan, sai ki wanke jikinki ko
fuskarki da ruwa mai dumi. Hakan zai cire miki dukkan dattin da ke makale a
kofofin fatarki.
12.==> Sulbin
fatar fuska; a samu ayaba sannan a kwaba ta tare da kindirmo sannan a rika
shafawa a fatar fuska a bari na tsawon mintuna ashirin sannan a wanke da ruwan
dumi a bari fuskar ta bushe da kanta kafin a shafa mata man fuska.
13.==> Ki
samu kukumba sai ki yayyanka ta, daga nan sai ki nika ta, sannan ki ajiye
ta gefe guda. Hada ruwan Rose Water da ruwan lemon tsami ko jus din lemon
tsami. Bayan nan sai ki hada su waje guda da kukumbar, sai gauraya sosai. Bayan
kin yi haka sai ki shafa a fuskarki ko sauran fatar jikinki, sannan ki kwanta
har zuwa wayewar gari. A lokacin da kika zo wankewa, sai ki samu ruwa mai dumi.
Hakan zai kara wa fatarki lafiya da kuma sheki.
14.==> Fason
kafa: yana da kyau a rika sanya takalma masu laushi ba masu tauri sosai
wadanda zasu rika illata fatar ba. Idan an kasance ana da fason kafa, sai a
rika tsoma kafar a ruwan dumi da gishiri na mintuna goma sannan a rika gogewa
da dutsen goge kafa sannan a shafa man ‘glycerin’ sannan a sanya safa kafin a
kwanta a kullum domin samun saukin matsalar.
15.==> Karyewar
gashi: kada a rabu da man zaitun a koda yaushe. A kasance ana sanya shi a
gashi da zarar anji fatar kai ta fara bushewa. Yawaitar sanya man zaitun ko
kuma man kwakwa na hana gashin kai zubewa.
Shin
kina da wasu hanyoyi da kike ganin zai taimaka wajen kula da jiki da ban zayyano
a cikin wannan rubutun ba? Taimaka mana ta hanyar rubutawa a comment box dake
kasa. Ko kuma ta hanyar tuntubanmu dan bada gudumawa.
No comments:
Post a Comment