Muhammad Abba Gana
Mutane da dama sukanyi tambaya shin da gaske
ne an sake Sakamakon Jarabawara NECO Na Shekaran 2019? Kwarai kuwa da
gaskene. Hukumar shirya jarabawar NECO ta kasa ta fitar da sanarwar cewa ta
sake sakamakon jarabawar dalibai na dubu biyu da sha tara (2019) ta kara da
cewar kashi saba’in da daya (71%) bisa dari na daliban da suka rubuta sun sami
credit a harshen turanci (English) da kuma lissafi (Mathematics).
Karanta: Yadda Ake Siyan Token Domin Duba Sakamakon Jarabawar NECO
Sake sakamakon jarabawar NECO na shekaran
dubu biyu da sha tara labarine mai dadi ga daliban da suke jira domin daurawa a
account nasu na JAMB domin samun damar shiga makarantu na jami’a. yanzu mutum
na da damar ganin sakamakon sa sannan kuma ya kan iya daurawa a account nasa na
siradin duniya wato JAMB kafin su fara raba admission zuwa jami’a na shekaran
dubu biyu da sha tara (2019).
Na samu sakonni daga mutane da dama akan
cewar shin ta yaya za’a duba sakamakon jarabawar NECO ta hanyar amfani da katin
gogewa (Scratch card) ko kuma ta hanyar amfani da numbobin sirri (Pin) wasu
kuma sukanyi korafin cewar basu ga shekaran dubu biyu da sha tara (2019) a
babban shafinta ba. A hakikanin gaskiya Hukumar shirya jarabawar NECO ta kasa
ta chanza shafinta na duba sakamakon jarabawa haka zalika ta sauya mata kan
duba sakamako. A yanzu Token (Numbobi Masu Zamar Kansu) ya maye gurbin shi
Katin Gogewa (Scratch Card) da kuma Numbobin Sirri (Pin) bisa wasu dalilai.
Karanta: YADDA AKE DUBA SAKAMAKON JARABAWAR JAMB NA SHEKARAN DUBU BIYU DA SHA TARA 2019
Yadda Za’a Duba Sakamakon Jarabawar NECO
Mutum yana bukatan ya siya Numbobi Masu Zamar
Kansu (Token) kafin ya samu damar duba sakamakonsa a yanar gizo na shekaran dubu
biyu da sha tara (2019). Za’a iya karanta cikken bayani yadda ake siyan NumbobiMasu Zamar Kansu (Token) a nan. Bayan mutum ya bude account a shafin NECO sannan
kuma ya siya Numbobi Masu Zamar Kansu wato (Token) nasa kamar yadda na zayyano
ba tare da karya daya daga cikin dokokin su ba.
Matakan Da Ake Bi Wajen Duba Sakamakon Jarabawar Neco
Mataki Na Biyu: Sannan za’a zabi shekaran jarabawa Misali:
2019.
Mataki Na Uku: Za’a zabi wani irin jarabawane Misali:
SSCE Internal (JUN/JUL).
Mataki Na Hudu: Za’a saka “Registration Number” da kuma
Numbobi Masu Zamar Kansu wato (Token) da aka siya a dai dai inda aka bukaci
hakan.
Mataki Na Biyar (Karshe): Sai a latsa madannin “CHECK RESULT”
Muddin anbi matakan dana zayyano daidai a
baya mutum zaiga sakamakon jarabawarsa wula-wula na ko wani subject daya
rubuta.
Yadda Ake Fitar Da (Printing) Sakamakon Jarabawar NECO
Domin fitar da (Printing) sakamokon jarabawar
NECO na shekaran Dubu Biyu Da Sha Tara (2019) dole sai mutum ya duba sakamakon
sa da fari kamar yadda nayi jawabi a baya. Bayan mutum ya bude sakamakonsa a
shafin NECO zai ga tambari na alamar firinta (Print Icon), sai a latsa
kai ko kuma ta hanyar amfani da CTRL + P a kwanfuta.
Shugaban Hukumar shirya jarabawar NECO na
kasa Mal. Abubukar Gana yace cikin dalibai 1,151,016 da suka rubuta
Jarawa a shekaran dubu biyu da sha tara (2019). dalibai 829,787 ne kadai
suka samu nasarar samun credit a harshen turanci (English) da kuma lissafi
(Mathematics) wadda dole ne sai mutum ya samu kafin ya fara shun shunan jami’a.
Karanta: Yanda Ake bude blog cikin sauki
Ya kara da cewar dalibai 40,630 ne
suka tsinci kansu cikin haramcecciyar dabi’a ta hanyar yin sata a cikin Jarabawa
wadda adadin ya ninka na shekaran data gabata wato shekaran dubu biyu da sha
takwas (2018).
Shin ana fuskantan wani kalubale yayin duba sakamakon
jarabawan NECO na shekaran dubu biyu da sha tara (2019)? za’a iya tuntubanmu
kai tsaye ko kuma kamfanin Be With Me Technology domin samun taimakon agajin
gaggawa a ko wani lokaci.
No comments:
Post a Comment