Kodewar fata na aukuwa ne a lokacin da mutum
ya kasance yana yawan shiga cikin rana domin neman halaliyarsa ko kuma don yini
a rana. Idan hakan ta kasance, sai fatar ta zama baka. Wannan abu ya fi aukuwa
ne a fuska. Sai a ga fuskar gefe daya ta yi baki daya gefen kuma da dan haske.
Wannan abu ba a sanin lokacin da suke faruwa. Shi ya sa a yau na kawo muku
hanyoyin da za a bi don neman kariya daga wadannan kunar ranar ko kuma kodewar
fata.
Ruwan
dankalin turawa; a fere
dankalin turawa sannan a wanke sai a kankare a matse ruwan sannan a rika
shafawa a fuska musamman inda fatar ta kode. Yin haka na magance matsalar fatar
sannan kuma yana kare sake aukuwar hakan.
Madara; a samu madara a sanya a gidan sanyi har sai
ta yi sanyi sosai sannan a samu tawul karami a rika tsomawa ana goge fuskar da
shi. Madara na sanya hasken fata sannan kuma tana warkar da wannan kodewar
fatar.
Ruwa; a yawaita shan ruwa sosai idan ana dauke da
wannan matsalar sannan za a iya sanya ruwan ya yi kankara sannan a rika shafa
wannan kankarar a inda fatar ta kode.
Gurji; a samu gurji sannan a yanka sannan a sanya a
gidan sanyi har sai ya yi kankara sannan a rika shafawa a wannan wajen da fatar
ta kode ko kuma a rika daurawa wurin har sai ya narke.
Koren
ganyen shayi; za a iya
tafasa koren ganyen shayi hade da na’ana. Bayan sun tafasa sannan a bari hadin
ya jiku kamar na tsawon sa’a daya sannan a sanya a gidan sanyi, sannan a wanke
fuskar da hadin ko kuma a samu auduga ana shafawa a inda fatar fuskar ta kode.
Ganyen
‘aloe bera’; a samu
wannan ganyen sannan a matse ruwan da ke ciki a rika shafawa a fuskar a kullum
har sai kodewar ta yi sauki. Wannan ganye na da matukar mahimmanci a fatar mu
don haka yana da kyau a kowane gida a shuka.
Ruwan
tuffa; za a iya samun wannan
ruwan ne bayan an kankare sannan a matse. Sai a rika shafawa a fuska har sai ya
bushe. Haka za a rika yi a kullum.
Masu karatu kada su hada duka wannan hadin su
ce za su yi shi a lokaci guda. Sai dai su zabi daya daga cikinsu. Hada wadannan
ababen da na lissafo na iya haifar da wata cutar fatar fuska. Da fatan za a
kiyaye.
No comments:
Post a Comment