Muhammad Abba Gana
Kowani ciwo yana da magani hakan take; mata
da dama sukan koka wajen yadda maran su ke ciwo lokacin al’ada, hakan yana
faruwane bisa wasu dalilai. Insha Allahu yau Duniyan Fasaha ta kawo muku wata hanya
da zaku bi wadda da izinin Allah za’a dace.
Karanta: Cikakken bayani yadda kayan kwalliyan zamani ke haifarwa fata mummunan matsala
1.
==> A samu Tsohuwar
Tsamiya a jika aruwa tare da bushashiyar gauta arika shan ruwan tun kwana biyu
kafin zuwa haila, har lokacin da hailar zata fara zuba. Wannan Mataye da dama
sun jarraba kuma sun dace.
2.
==> MAN ZAITUN: A sami
man zaitun sai a Karanta ayoyin Alqur'ani acikinsa sannan Mace ta rika shan
cokali guda safe da yamma kullum har zuwa lokacin zuwan Jinin al'adarta.
Kuma zata rika shafawa ajikinta har Mararta
(Amma banda al'aurarta saboda ayoyin da aka tofa). Shima wannan idan anyi shi
za'a dace. Koda Aljanu ne suke rike mata Marar, ko suke sanya mata ciwon jikin
to zata samu waraka.
3.
==> KUSTUL HINDI: Idan an
jikashi a ruwa ana shansa safe da yamma shima yakan Magance matsalar ciwon mara
ko rashin zuwan jinin sosai, ko kuma rikicewar jinin Al'ada. Kuma koda ajiyar
Aljanu ne a marar mace ko mahaifarta, in sha Allahu zata samu waraka.
Karanta: Yadda za a magance kodewar fata
Da fatan Allah shi amshi dukkan abinda muke
roka ma junanmu. Allah yasa mu dace. Ameen!
-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:
Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan
Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
No comments:
Post a Comment