Uwar Gida idan babu ke babu cikkane gida haka
zalika rashinki tamkar rashin wani bangarene na jiki, Assalamu Alaikum barkanmu
da war haka barkanmu da sake saduwa daku A cikin shirin namu na Girke-Girke
wadda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha.
A makonin da su ka gaba mun kawo muku saloli
daban daban na yadda ake hada abincin zamani haka zalika yau mun kawo muku wata
sabuwar hanya ta yadda ake hada soyayyar taliya da kaza cikin sauki.
Kowace mace tana da irin nata dabarun wajen
sarrafa girki haka zalika ko wace mace da yadda abincin ta ke dandano ko daya
ke wasu lokutan ya dan gana da ababen da akayi amfani dasu wajen hada girkin.
Yana da kyau mata su rika canza yanayin yadda
suke sarrafa girki domin shi harshe a kullum yana son dandano daban-daban. Yana
da kyau mace a kullum ta kasance kwararriya a wajen sarrafa girki ta bangarori
daban-daban domin yin hakan yakan kara dankon soyayya da kuma kauna daga shi
mai gida haka zalika ta wajen yara.
Duk yadda kike da kyau, komin yadda kike
nunawa mai gida kauna idan har baki iya girki da zai motsa kunnuwansa ba to
wasu lokutan zai iya tsinci kansa a duniyar rashin kaunarki wadda zai iya kaiwa
da ya nuna miki Zahiri.
Domin girka Soyayyar Taliya da Kaza ga ababen
da ake bukata kamar haka:
- Taliya
- Tumatir
- Nama
- Kaza
- Karas
- Koren wake
- ‘peas’
- Magi
- Kori
- Tafarnuwa
- Citta da kuma
- Albasa
Matakan Da za’abi wajen hadawa:
Da fari za’a yayyankan albasa da tumatiri a
aje a gefe guda sannan a dora ruwa kan wuta, bayan ya tafasa sosai sai a zuba
taliya da gishiri kadan a lokaci guda cikin ruwan. Idan taliyar ta yi tafasa
daya sai a tsame a ajiye a gefe guda. Sannan adora man gyada a wuta bayan ya
soyu sai a zuba yankakkiyar albasa da yankakken tumatir da jajjagaggen attarugu
a ciki.
A tafasa nama, a tsamesa daga cikin ruwa
sannan a yayyanka shi kanana sai a zuba. A zuba magi, kori da garin tafarnuwa
da citta sannan a dauko wannan taliyar a zuba ta a ciki a gauraya. A zuba ruwa
kadan sannan a rufe bayan mintuna biyar zuwa takwas sai a sauke daga wuta.
Abu na gaba da za’ayi anan shine a tafasa
kaza ta yi laushi hade da magi da kayan kanshi sannan a soya da man gyada. A
soya tumatir da attarugu da albasa. A zuba magi da citta da tafarnuwa. Bayan an
tabbatar sun soyu sannan a dauko kazan a cakuda shi a ciki sannan a dora a kan
wannan soyayyar taliyar.
Wannan shine cikakken bayani yadda ake hada Soyayyar
Taliya Da kaza. Dafatan girkin ya kayatar. A ci lafiya!!
No comments:
Post a Comment