Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Yadda Ake Siyan Token Domin Duba Sakamakon Jarabawar NECO

Yadda Ake Siyan Token Domin Duba Sakamakon Jarabawar NECO


Hukumar shirya jarabawar NECO ta kasa ta fitar da sabon sanarwar cewa ta bude sabon shafinta wadda zai taimaka wa dalibai na kasa baki daya wajen duba sakamakonsu na karshen zango. Wannan sabon shafin ya sha babban da wadda ya gabata, a shekarun baya idan mutum yana bukatan yaga sakamakonsa na jarabawar NECO to fa dole lallai sai ya siya katin gogewa wadda aka fi sani da scratch card a turanche.   

Karanta: YADDA AKE DUBA SAKAMAKON JARABAWAR JAMB NA SHEKARAN DUBU BIYU DA SHA TARA 2019


Amma da sabon shafin nan abinda mutum ke bukata shine token, token ya maye gurbin katin goggewa (scratch card) da kuma numbobin sirri (Pin). Hukumar ta kara da cewar tayi hakan ne domin kara inganci sannan kuma da sawwake wa dalibai wajen duba sakamakon su. Kama daga yanzu www.neco.gov.ng shine babban shafin hukumar shirya jarabawar neco sannan duk sakamakon jarabawa za’a iya samu a cikin shafin ta na kowani shekara.

Karanta: Cikkaken Bayani Yadda Ake Samun Kudi A Yanar Gizo (Internet) Cikin Sauki


Kama daga yanzu za’a iya ganin sakamakon jarabawar NECO ta hanyar siyar token wadda za’a iya samu daga shafinta sannan kuma za’a iya rabawa dalibai, makarantu, ko kuma kamfanoni wayanda suke da niyar ganin sakamakon jarabawar dalibai.

Yadda Ake Siyan Token A Yanar Gizo


Matakin Farko: Mutum zai ziyarci shafin hukumar shirya jarabawar NECO ko kuma ta hanyar danna wannan addreshin https://result.neco.gov.ng/register

Mataki Na Biyu: Mutum zai saka cikakken sunan sa a shafi na farko, sannan number wayarsa a shafi na biyu, sai kuma email addreshin sa an uku, sai mutum ya zabi numbobin sirri da yake son sawa sannan ya maimaita a shafi na karshe. Bayan mutum ya tabbatar da abinda yasa daidaine kuma zai iya tunawa sai ya latsa madannin “Register”

Yadda Ake Siyan Token Domin Duba Sakamakon Jarabawar NECO


Mataki Na Uku: Hukumar NECO zata turawa mutum sako a addreshinsa na email da yayi amfani dashi yayin rajister.  

Mataki Na Hudu: Mutum zai bude sakon sannan ya danna mabulin “Verify” domin jaddadawa.

Mataki Na Biyar: Mutum zai ziyarchi shafin NECO wajen shiga ko kuma ta hanyar latsa nan https://result.neco.gov.ng/login

Mataki Na Shida: Mutum zai saka email addreshinsa ko kuma numbern wayarsa a shafi na farko sannan kuma ya sanya numbobin sirrinsa daya zaba yayin rajister a shafi na biyu sannan ya latsa mabullin “Login”

Karanta: Yadda ake shiga Email wato na Gmail cikin Sauki


Yadda Ake Siyan Token Domin Duba Sakamakon Jarabawar NECO


Mataki Na Bakwai: Mutum zai nema inda aka rubuta “Purchase Token” sannan ya latsa kai yin haka zai bawa mutum damar wucewa zuwa gaba. Abin Kula: za’a iya amfani da ko wani token a kan sakamako guda daya kacal sannan duk wani token akwai wasu adadi na amfani dashi.

Karanta: Ya Password din ka yake? Ya kuma ya kamata a ce yake?


Mataki Na Takwas: Mutum zai zabi a dadin da yake son siya sannan ya danna mabullin “Pay Now” Abin kula: ko wani token guda naira dari biyar ne da kuma kudin sabis naira (50) wadda ya kama naira dari biyar da hamsin kenan (550).

Mataki Na tara (karshe): Mutum zai latsa ma bullin “Pay” domin biya ta dandalin Remita ta hanyar amfani da banki ko kuma katin banki.

Karanta: Yadda Za’a Duba Ko Katin Kasa (National I.D) Ya Fito


Wannan shine cikakken bayani ta yadda ake siyan token domin duba sakamakon jarabawar NECO ta hanyar amfani da sabon shafinsu. Shin ana fuskantan wani kalubale yayin siyan token na NECO? za’a iya tuntubanmu kai tsaye ko kuma kamfanin Be With Me Technology domin samun taimakon agajin gaggawa a ko wani lokaci.           


Karanta: Yadda Ake Duba Sakamakon Jarabawar NECO Na Shekaran 2019mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *