Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Cikakken bayani yadda kayan kwalliyan zamani ke haifarwa fata mummunan matsala

Cikakken bayani yadda kayan kwalliyan zamani ke haifarwa fata mummunan matsala 

Babu shakka kayan kwalliya na taimakawa matuka wajen bunkasawa da kuma kara fito da kyanki. Kai kayan kwalliya irin na zamani ba kayata kyau ba ma har kawar da muni suke yi. Zan iya cewa irin kayan kwalliyan da ake da shi yanzu da wadanda ake kirkira a kullum, amshin addua ne ga masoya kwalliya a duk fadin duniya.

KARANTA: "ILOLIN SHAFE-SHAFEN BLICING GA MATA"


Sai dai akwai matsala. Sau daya yadda muke amfani da kayan kwalliyan kan iya haifarwa fatarmu matsalar da kayan kwalliyan ko dubu nawa ba za su iya rufewa ba. Insha Allahu yau Duniyan Fasaha ta kawo muku hanyoyi guda uku (3) da ake amfani da kayan kwalliya wadanda fata da ace tana da baki da ta koka:

1.==> Kwana da kwalliya a fuska: A lokacin da muke barci ne jikinmu ke aiki tukuru wajen kawo karshen matsalolin da sassan jikinmu ke fuskanta, ba’a bar fata a baya ba. A yayin da muka kwanta barci da kwalliya, hakan baya samuwa domin kuwa kayan kwalliya na yin kane kane a cikin kofofin fata su hana ruwa gudu. A dan haka sinadaran da zasu karawa fatarmu inganci, kyawu da sheki ko dai daga wani mai da muka shafa akan fatar ko kuma wanda jikinmu ya sarrafa daga abinci ba zasu iya yin amfaninsu ba yadda ya kamata.

Karanta: Yadda za’a magance matsalolin fata a sanyi


Idan mutum mai saurin samun kuraje ne, hakan yakan kawo su da gaggawa, idan ma ba kya yin kuraje to tabbas za ki tashi daga barci kiga fatarki ta rasa shekinta da kyawunta. Ci gaba da yin hakan zai tabbatar da lalacewar fatarki a nan gaba. Ki tabbatar kin wanke kayan kwalliya tsaf daga fatarki, daga su har kamu kamunsu kafin ki yi barci da daddare dukkuwa irin gajiyar da kika yi.

2.==> Amfani da kayan kwaliyan da irinsu bai dace da irin fata ba: Idan fatarki tana da maiko, ki ka je kika sayi kayan kwalliya masu tushe mai maiko, toh kinyi amfani da kudinki kin jibgawa kanki aiki, gani da yadda suke da matukar tsada ma a yanzu ya sa ya cancanta ayi maki jaje. Dalili kuwa shine maimakon ki kara kyau, da kin shafa sai fuska ta cika da maiko.

Banda toshe kofofin fata da kayan kwalliyan sukayi, ga kuma maiko ya zo ya kara na shi akai. Hakan yana haifar dawa fata matsala matuka.

Haka kuma idan kina da busasshiyar fata kika fara amfani da kayan kwalliya marasa maiko, nanma fa akwai matsala domin kuwa fatarki zata yi ta bushewa har ta fara yamushewa ta zama kamar ta tsohuwa. Banda hakan ma, wani lokaci irin sinadaran da ke cikin kayan kwalliya masu hatsari ne ga lafiyar fata, shi yasa za gi ga yawanci an rubuta cewa ki dan gwada kadan a matse matsin gwiwar hannunki na tsahon awanni kafin ki fara amfani da shi. Amma da yawanmu bama yin hakan. Sai an gama shan kyau, fata kuma ta zo ta zama kamar taswirar Nijeriya, a zo ana cewa an samu ‘skin reaction’ da ba’a san dalilin sa ba.

3.==> Amfani da kayan kwalliyan da suka tsufa: Brushes din da ake amfani da su wajen yin kwalliya da bakin kayan kwalliya na matsawa irin su foundation gurin taruwar kwayoyin cuta suke zama. Shi yasa aka shawarci ma’abota kwalliya da su tabbatar cewa ko da yaushe sun ajiyesu a guri mai tsabta, sun kuma tabbatar da ba’a hada amfani da su da kowa ba.

Karanta: Yadda za a magance kodewar fata


Ban da haka ana so a daina amfani da mascara guda daya bayan wata 3, shi kuma foundation bayan shekara daya. Idan basu kare ba kawai zubar da su ake. Brushes kuma za’a iya wanke su a cikin ruwan zafi domin kashe kwayoyin cutar lokaci lokaci. Ajiye kayan kwalliyan nan a cikin jaka daya su hada datti su hada datti ba alkahairi bane ga fatarki, wani lokacin ma har kaisu baki ake yi wanda anan ma zasu iya kwaso matsala daga yawun baki. Ya kamata dai a kiyaye, domin ni fa na fi son naga kowa tsaf tsaf, fata na sheki kamar wancan abun da na manta sunashi.


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *