Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

MIYAR ZOGALE

MIYAR ZOGALE 
Kamar yadda mukayi bayani a baya zogale na taimakawa lafiyar jiki matuka ta hanyoyi daban daban ta hanyar shan sa ko kuma ta hanyar cin miyarsa. Insha Allahu yau kuma Duniyan Fasaha ta kawo muku bayani ne akan yadda ke tsara miyan zogale cikin sauki wadda zai so sa kunne mai gida sannan kuma ya sa yara santi. A sha karatu lafiya.

Karanta: Yadda ake jus din gurji mai zobo


Abubuwan Da Ake Bukata


 • Tattasai
 • Attarugu
 • Albasa
 • Zogale
 • Maggie
 • Gishiri
 • Garlic thyme
 • Seasoning spices
 • Nama
 • Kifi busashshe
 • Man ja or man gyada
 • Gyada


Yadda Za’a Hada Miyar Zogale


Da fari zaki tafasa nama ki sanya thyme da maggie da albasa bayan ya tafasa saiki sanya mai a tukunya ki soyashi da albasa saiki zuba kayan miyarki ki kuma sanya naman da kika tafasa tare da ruwan da kika tafasa naman.

Karanta: Yadda ake masa


Saiki zuba gyadar ki wadda kin riga kin gyarata kin daka ta da busashshen kifin ki shima bayan ki gyara abunki saiki sanya curry da maggie gishiri saiki barshi yayi kamar mintuna goma (10) saiki zuba zogalen ki bayan kin gyarashi.

Abinda ya Gabata: Yadda ake girka ‘sweet and sour shrimps’


Anaso ki zuba zogalen da yawa domin anfiso miyar tayi kauri saiki barshi kan wuta yayi a kalla kamar mintuna sha biyar (15) shikenan saiki sauke. Miyarki yayi dai dai kuma a shirye yake wajen ci.


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *