Tare da Muhammad Abba Gana {Jikan Marubuta}
Duk
da cewar layukan sadarwa da muke aiki da su a wasu lokutan sukan mana zanba ta
hanyar cire mana kudade ba tare da kwakkwaran dalili ba haka zalika a wasu
lokutan mukan kuma iya taimaka musu kwarai da gaske ta hanyar shiga wani tsari
ba tare da sanin ingancinsa ba balle sanin rashin ingancin.
Sau
da dama mutane kan yi korafin cewar sun saka kati a layinsu na sadarwar MTN sai
de kafin suyi wani amfani dashi sai su tarar anyi wuff da katin ba tare da wata
shaidar an cire ba balle mutum yayi tunanin ya shiga wani tsari.
Saboda
wannan matsalar mutane da dama sun daina amfani da kamfanin sadarwar MTN kuma a
mafi yawancin lokutan hakan na faruwa ne saboda shiga tsarin MTN PLAY ko kuma
MTN CALLER TONE wadda ko wanne yana mai zamar kansa ne.
Ba
ina nufin su kadai ne tsarin da mutum zai shiga ya zamana ko da yaushe yana
cikin jerin masu bada sadaqa fisabilillahi ba tare daya shirya ba ga kamfanin
sadarwar MTN sai de sune wasu daga cikin mafi yawancin tsaruka da mutane ke
yawan shiga daga lokaci zuwa lokaci.
Layukan
sadarwa suna amfani da wayan nan tsarin ne wajen zalintar al’ummar kasa duk da
cewar fadar gwamnatin tarayya da masu hannu da shuni suna kokarin ganin cewar
an magance wannan matsalar.
A
hakikanin gaskiya wadannan tsarukan suna wahalar fita, wasuma sun gaji da kiran
kamfanin sadarwar saboda kokawa ga matsalar daya adda besu haka zalika wasu ma
sun gaji da tuntuban masana na kusa domin magance wannan matsalar.
Insha
Allahu yau a Duniyan Fasaha zamu
tattauna ne game da hanyoyi da za’a bi wajen magance wannan matsalar cikin
sauki amma kafin mu tattauna akan yadda za’a magance matsalar bari mu fara da
duba wasu daga cikin matsalolin da kuma yadda ake iya shigansu bisa kuskure ko
kuma tare da sani. Wasu daga cikin tsarukan sun hada da:
=>> MTN PLAY
=>> MTN
CALLER TONE
=>> MTN DATA
RENEWAL
=>> GAMING
=>> RELIGIOUS
SERVICES
=>> MTN
BACKUP
==>
MTN PLAY: Wannan yana daya daga cikin manyan tsaruka dake da
sassa daban-daban domin kuwa ya kasance tamkar uwa, wasu daga cikin sassan sun
hada da:-
* Labarun Wasanni: Wanna ya hada da club da
kake/kike bibiya ko kuma wadda ba ka/ki bibiya ya dangana da abinda aka zaba.
* Labarun Siyasa
* Labarun Barkwanci
* Labarun yau da kullum wadda ya kunshi;
kasuwa, yanayi, farashi da dai maka mancin haka.
* Labaru na Musamman: Daga tashoshin watsa
labarai kamar CNN, BBC, ALJAZEERA, NAIJA da sauran tashoshin.
* Labarun koyon harsuna kamar Turanci,
Hausa, Igbo, Yoruba, Pigin da dai sauran su.
* Akwai wani bangare na mussanman wadda ya
kunshi Karin Magana, labaran soyayya, kalaman soyayya da dai sauransu.
=>
MTN CALLERTONE: Wannan bangarene na musamman daya kunshi
sauti kama daga wakokin siyasa, soyayya, rayuwa da dai makamancin haka, wadda
mutum zai iya daurawa ga layin sa duk lokacin da ake kokarin kiransa mai makon
aji karar agogo na bugawa sai aji wannan sautin da mutum ya zaba.
Ba lallai sai mutum ya zaba ba, a wasu
lokutan sukan turo da Karamin akwati a fuskan waya dauke da sako muddin mutum
ya danna madannin “Ok” ko kuma “Accept” ma’ana ka yadda kenan bisa kuskure ko
sani shikenan ka shiga tsarin zasu zaba maka wakan daya dace da kai sannan
wannan wakan ne zai maye gurbin agogon kiranka.
==>
MTN DATA RENEWAL: Wannan tsarin yasha ban-ban da wadda mukayi
bayi a baya a wannan bangaren kuma yana aiki ne da siyan data. A duk lokacin da
mutum ya siya data a layin sadarwansa sukan bada zabi wajen yanke shawaran mai
zai auku idan wannan data yakare ko kuma wa’adin sa ya cika wato ya mutu a wasu
lokutan mukan zabi ya sake siya. Sai sa a duk lokacin da datan yakare sai ya
sake siyan kansa saboda mu muka bada zabin hakan.
==> GAMING:
Wannan tsarin yana yawan aiki ga wasu amfani da salulan taba ka lashe wadda
aka fi sani da smart phone a turance, a mafi yawancin wayoyin idan muka lura
zamu ga cewar akwai wasu manhaja da suke fitowa wadda ba mu muka saukar ba haka
zalika ba mu muka fitar da su ba sukanzo da kansu kuma ba’a iya ciresu face an
samu kwararre.
A wannan bangaren akan baiwa mutum damar
buga wasanin daban daban na son rai wadda mutum zayyi hakan ba tare da saukar
da manhajar ba. Yin hakan shike sa a wasu lokutan suke shanye katin sannan muyi
korafin cewar bamuyi komai dashi ba.
==> RELIGIOUS
SERVICES: Wannan tsarin na musamman ne daya kunshi abubuwa ta bangaren
addinai kama daga wa’azuzzuka, tafsirai, karatu da dai sauransu; na dukka
addinai biyu da muke dasu (Musulunci da kuma Kiristanci).
==> MTN
BACKUP: Wannan yana daga cikin tsarin da mafi yawanci mutane ke shiga musamman
lokacin da aka chanza wayar salula, layukan sadarwa sukan iya ganewa a duk
lokacin da mutum ya chanza waya ba lallai sai an siya sabo ba, a’a; a duk
lokacin da layin sadarwa sim card da ke cikin waya aka ciresa a ka kuma sanya
izuwa wani wayar, a wajen su yakan zama sabo sabili ba wajen da yake bane a da.
Amfanin wannan tsarin shine adana wasu muhimman
bayanai kama daga sakonni da kuma layukan da aka adana wadda a koda yaushe
mutum zai iya dawor dasu idan wata matsala ta auku irin faduwar waya ko kuma idan
an bude xender da ita wayar wato an sace sa.
Yadda
Za’a Magance Matsalar Cikin Sauki
Domin magance wannan matsalar akwai wasu
hanyoyi da zamu iya bi wadda su ke da matukar sauki kuma ba bukatan kashe kobo
ko sisi.
Saboda yawan korafe korafe da ake samu
kanfanin sadarwar MTN sunyi nasarar fito da wata hanya da mutum zai bi wajen
iya ganin duk wasu tsaruka da yake ciki sannan kuma zai iya fitansu a duk
lokacin da hakan ya taso.
Shi wannan hanya za’a iya ganin kusan duk
abubuwan da muka lissafo da kuma wadda bamu samu damar lissafowa ba amma banda
tsarin “MTN Data renewal” Domin shi
wannan tsarin yana aiki ne ta bangare daban.
Don sanin tsarukan da mutum ke ciki za’a
iya latsa *123# sai a kira, bayan
shafin ya budu sannan sai a zabi number na biyar wato “My Services” ta hanyar
rubuta lambar a dan karamin akwatin da aka tanadar bayan an rubuta sai a danna
madannin “Send” wadda shima an tanadar a kasan karamin akwatin.
Bayan haka sai
a zabi mataki na farko ta hanyar rubuta lamba mai dauke da “Active Services”
wadda shine na farko “1” a jerin ababen da aka lissafo,
muddin anbi matakan dai-dai
in har mutum yana cikin wani tsari za’a nuno masa dukka ko mai yawansu.
Domin fita daga tsarin da ba’a bukata
ajerin ababen da aka lissafo wa mutum sai a rubuta lambar tsarin a dan karamin
akwatin tare da latsa mabullin “Send” wadda ke kasan akwatin da aka danadar.
Misali a layina ina cikin wani tsari mai
taken “Callerfeel” wadda shine tsari kadai a yanzu wadda ke dauke da number
daya, domin ficewa daga tsarin akwai bukatan saka lambar tsarin a dan karamin
akwatin da aka tanadar sannan a latsa madannin “Send”
bayan ya bude zai kawo
jerin ababen da mutum zai iya kaddamarwa ga wannan tsarin. Na farko daga cikin
jerin ababen da aka lissafo akwai “Accept” wadda shine tabbatar da fita daga
tsarin da aka zaba wadda shine muke buka ta a yanzu, sai mu rubuta lamba daya
tare da latsa mabullin “Send”
sannan zamu sami sakon cewar mun fita daga tsarin
da muka zaba.
Abin Kula: Idan mutum ya kasance yana cikin tsari
guda dak zai iya bin matakan dana yi amfani dashi a baya wajen fi cewa daga tsarin.
Amma idan ya kasance mutum yana cikin tsari fiye da guda kuma sannan yana son ficewa
daga dukka tsarin zai iya bin wannan matakin:
Za’a latsa *123# sannan a kira bayan shafin ya budu sai a zabi number na biyar
wato “My Services” sannan kuma sai a zabi mataki na farko mai dauke da “Active
Services” wadda shine na farko “1” a jerin ababen da aka lissafo, bayan anyi
haka sai a latsa madannin “Send”
hakan zai bawa mutum damar wucewa mataki na
gaba wadda za’a zayyano masa duk tsarukan da yake ciki domin ficewa daga duk
tsarukan da aka lissafo wa mutum sai a zabi number na biyu mai dauke da “Cancel
All” ta hanyar rubuta “88” a dan karamin akwatin da aka tanadar, sannan a latsa
madannin “Send” wadda ke karkashin akwatin.
Shikenan za’a sami sakon ficewa
daga duk wasu tsarukan da mutum ke ciki.
Dafatan
wannan hanyoyin ya taimaka matuka wajen magance matsalar da ake fuskanta a
layin sadarwa MTN. Shin akwai wata
hanya mai matukar sauki da za’a iya bi wajen magance wannan matsalar wadda ba
muyi Magana a kai ba? Za’a iya turo mana ta hanyar tuntubanmu ko kuma ta
hanyoyin sada zumuntan mu na WhatsApp da kuma twitter. Asha Ruwa Lafiya!
No comments:
Post a Comment