Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

YADDA AKE DUBA SAKAMAKON JARABAWAR JAMB NA SHEKARAN DUBU BIYU DA SHA TARA 2019

YADDA AKE DUBA SAKAMAKON JARABAWAR JAMB NA SHEKARAN DUBU BIYU DA SHA TARA 2019


Muhammad Abba Gana

Barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa daku a cikin sabon shirin namu wadda yake zuwa muku kai tsaye daga mujjalar Duniyan Fasaha, insha Allahu yau zamuyi jawabine akan yadda ake duba sakamakon jarabawar Jamb na shekaran dubu biyu da sha tara (2019).

Mutane da dama sun kosa matuka wajen son suga sakamakon jarabawar jamb na shekaran dubu biyu da sha tara (2019), musamman ma iyaye da kuma dalibai. Wasu daliban suna cikin tsaka mai wuya saboda labarai da ke fitowa yan wasu makonni da suka shude cewar dalibai da dama baza suga sakamakon jarabawansu ba sabili da sun jefa kansu cikin haramcecciyar hanya wato sata. Haka zalika wasu daga ciki za’a rage addadin abinda suka samu a cikin jarabawar.


Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a ta Kasa wato (JAMB), ta bayyana cewa jarabawar JAMB na shekaran dubu biyu da sha tara (2019) ta fito a Asabar data gabata. Sannan kuma hukumar ta ce babu ruwan dalibi da zuwa cibiyoyin rubuta jarabawa domin ganin sakamako.    

“Daga yau har zuwa ranar Litinin, wannan ce kadai hanyar da za’a iya ganin sakamakon jarabawa.” Ya ce sun fito da wannan tsarin ne domin hana ‘yan damfara su damfari mutane batun ganin sakamakon jarabawa. Sannan kuma an fito da wannan dabara ce domin duk wanda bai ga sakamakon sa ba, to ya na daga cikin wayanda aka rike sakamakon su.

Karanta: Yadda Za’a Duba Ko Katin Kasa (National I.D) Ya Fito


Sannan ya ce hakan ya na nufin an daina zuwa ana yin cunkoso a wurin duba jarabawa, inda wadanda ba su ga ta su ba ke yin dafifi a wuraren duba jarabawa ana haddasa cinkoso.

YADDA AKE DUBA SAKAMAKON JARABAWAR JAMB 2019


Wannan wata hanyace mafi sauki ga wadanda suka rubuta jarabawar shiga makarantun jami’a ta JAMB na shekaran dubu biyu da sha tara (2019) da zasu iya duba sakamakonsu.

Babu bukatar sai mutum yaje cibiyar CBT ko kuma inda ake aiki da yanar gizo wato CYBER CAFE domin duba sakamako.

Oloyede ya kara da cewa muddin ka tura sakon RESULT zuwa ga 55019 ta hanyar amfani da lambar wayar da akayi rajista da ita., to idan sakamakon ka ya fito, za ka ga an turo maka amsa cewar:

“Zuwa Gare ka, ga sakamakon jarabawarka kamar haka….”

Idan kuma an rike maka sakamako ne, to za a turo maka sakon: “RESULT WITHHELD”, wato “AN RIKE SAKAMAKON KA.”

Idan ka yi rajista amma ba ka rubuta jarabawa ba, za a turo maka sakon “CANDIDATE ABSENT”, wato “BA KA RUBUTA JARABAWA BA.”

Idan kuma an rike sakamakon ka, har zuwa lokacin da za a kammala wani bincike, to za a tura maka sakon: “AN RIKE SAKAMAKON KA sai an gama bincike a turo maka.”

Da fatan wannan rubutun ya taimaka sosai, zaku iya tuntubanmu ta wayannan hanyoyin idan kuna bukatar taimakon gaggawa ko kuma Karin bayani:

Kira: 09039016969
Whatsapp: 09039016969


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *