Idan
har an yi rajistar samun katin kasa na dan wasu tsawon lokuta sannan ba’a san
ranar da za’a karba katin ba, ko kuma an sha zuwa offishinsu tambayar ko ya matsayin
wannan kati yake amma kuma haka zalika ba’a ji sabon labari ba, wata kila kuma
an gaji da ziyartar offishinsu har an cire tsanmani. hukumar NIMC a yanzu ta
samar da shafin duba matsayin katin ta yanar gizo wanda zai bada damar sanin
cewa ko katin ya fito ko dai har yanzu da saura. Ga cikakkaiyar hanyoyin da
mutum zai bi ya duba matsayin katin sa na kasa a yanar gizo.
1.==>
Abu na farko dai shine, mutum zai ziyarci shafin NIMC a yanar gizo a wannan
addreshin: https://touch.nimc.gov.ng/
2.==> Idan
an shiga sai a danna mabullin ‘proceed button’ wadda ma’anar sa karasa zuwa
gaba
3.==>
Daga nan sai mutum ya cika wurin ababen da ake bukata na sunayen sa, wanda
akwai wurin cika suna na farko kafin sunan karshen wato sunan uba, sai kuma ya
saka lambobi na katin kasa da aka ba shi (yana jikin katin da aka bayar).
4.==>
Da mutum ya cike wadannan abubuwa da ake bukata sai ya danna mabullin ‘check
now button’. Bayan an danna sai a jira na dan wasu daki kai, yana gama dubawa
za’a nuna ma mutum matsayin katin sa. Ya fito ko kuma dai yana hanyar fitowa.
Allah
yasa ayi sa’a
-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:
Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan
Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
No comments:
Post a Comment