Assalamu Alaikum barkanmu da sake saduwa daku
a cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa muku kai tsaye daga mujjalar Duniyan
Fasaha, insha Allahu maudu’inmu a yau zamu tattaunane akan wani abu mai muhimmanci
wadda sau da dama mutane sukanyi tambaya akan sa; Ana ce masa ‘Garcinia kola’
amma a sauƙaƙe anfi kiransa da Namijin Goro kuma tushensa da tsirransu sun fito
ne daga Afrika ta tsakiya. Wanda hakan ke nuna irin mahimmancin da nahiyar ta
Afirka ke da shi a fannin tsirrai. Namijin Goro yana samar mana da ɗimbin
hanyoyin warkar da cututtuka na mamaki. Yana daga cikin dangin tsirrai na
Fulawa yana kuma fita da launin ruwan ƙasa.
AMFANIN
GA HUHU: Yana magance Huhu da
wasu sassa na jikin mutum sannan suna taimakawa wajen gudanar manyan ayyuka a
cikin jikin mutum. yana taimaka mana wajen yin numfashi.
Cin irin sa yadda ya dace, yana taimakawa
Huhu wajen gudanar da aiki yadda ya kamata kuma ya bada kariya a cikin jikin
mutum. Yana kuma taimakawa hanyoyin Jini haka yana magance sanyi na zuciya.
Saboda haka, ga mutane masu zuƙar Taba Sigari, namijin goro na iya zame musu
magani.
MAGANIN
CUTAR CIZON SAURO: Irin
Namijin Goro ana taimakwa wajen warkar da cutar cizon Sauro. Ba mamaki da masu
magungunan gargajiya suka bada shawara a riƙa yin amfani dashi. Ba a bayyana
wata illa da Namijin Goro keyi wa mutum a jikin sa ba saboda yin amfani dashi.
Amma a wasu lokutan, cin Namijin Goron yana
janyo wasu illoli a jiki. DAIDAITA BUGUN ZUCIYA YADDA YA KAMATA: Wasu sassan na
jikin mutum sukan nuna ƙyama wajen cinsu ɗin wasu itatuwan, inda cinsu ke
janyowa jikinsu wani irin yanayi. A irin wannan yanayin yana da kyau mutum ya
tuntuɓi Likitansa ya kuma daina yin amfani dashi.
Karanta: Matsalar Ciwon Sanyi Ga Mace
A yanzu mun riga mun san cewar Namijin Goron,
ba wai lallai ɗaci kawai yake dashi ba, yana kuma da ɓangare na zaƙi wanda kuma
yana taimakawa wajen ƙara lafiyar jiki a gare mu.
No comments:
Post a Comment