Kowa da kallar cikinsa sannan kuma da abunda
shi cikin nasan yake so, abincin wani yakan zama gubar wani. A mafin yawanci
lokuta mukan sami matsaloli da dama ta bangaren shi ciki yakan kasance munci ko
munsha wani abu wadda cikinmu bayaso hakan shi yake jawo mana matsala wani
lokutan sai kaga mutum ya sami barkewar ciki in kuma hakan ya auku ba wani
abunda mutum zayyi tayi face gudawa in kuma yazo da rashin sa’a sai abun ya
hade harda amai.
Karanta: Cikakken bayani yadda kayan kwalliyan zamani ke haifarwa fata mummunan matsala
Idan an dauki misali da ni kaina cikina baya
kaunar wasu abubuwa da dama wadda ya kama da irinsu yalo, geda, wake, miyan
karkashi, miyan zogale da dai sauran su, duk sa’an dana kuskura daya daga cikinsu
ya ratsa cikina tofa lallai ranar sai de na bada labari badai a bani ba dan
kuwa ranar na ringa zirga zirga wajen ziyartar bandaki kenan kuma sharrin abun
baya tashi lokacin da ido ke ganin komai sai lokacin da kake barci mai dadi
wata kila ma ka fara mafarki mai dadi irinsu karfe daya, biyu ko kuma uku na
dare a daidai wannan sa’ar ne zai fara numfasawa sannan kuma ya tayar da kai.
Dan gujewa wannan matsalar na kanyi kokarin
hanawa cikina wayannan abubuwan dana lissafo duk da cewar bakina na matukar
marmarin ci, amma kasancewar cikakken lafiya shine jari guje musu shine
alkairi, amma akwai mutane da dama masu tarar aradu da kai sun san cewar inhar
sun kuskura sunsa wannan abun a cikinsu to lallai zasu fuskanci matsala babba
amma hakan baya hana su gwadawa domin suna biyewa bakinsu, wadda hakan yake
kawo babbar matsala ga lafiyan jikin dan adam wadda ya kama da karewar ruwan
jiki ko kuma rashin isasshen jini a jiki.
Idan an kasance ana son cin abinda ciki baya
bukata sannan kuma a zauna lafiya, Insha Allahu yau a mujallar Duniyan Fasaha
zamu lissafo wasu abinci da mutum zaici bayan ya gama dauka abinda cikinsa baya
bukata domin gujewa gudawa…
karanta: Amfanin Cin Namijin Goro
A sami abincin da ciki baya bukata sannan aci
kamar ba gobe, aci daga safe har zuwa dare; idan ciki ya tsuge, sai a sami
flagin sannan a hada da wadannan abinci kala 6 da ke tsayar da gudawa:
1.==> Tuffa: Tufa na dauke da sinadarin ‘pectin’ wanda ke
taimakawa wajen karfafa kashi. Sannan yana dauke da sikari mai kau da ke mayarda
karfin da aka rasa a lokacin da ake zawo.
2.==> Dabino: Dabino na taimakawa matuka wajen dakatar da
zawo ta hanyar daure ciki, a mafi yawancin lokuta ana amfani dashine lokacin
sallar layya wato babbar salla inji yara
wai sallar nama koda kuw mutum ya yayi hadama a wannan lokutan in dai yaci
debino to yakan iya kwana lafiya ba tare da wata matsala b aba tare da kuma
wani fargaba ba. Debino yana kuma maganin cututtuka da dama wadda bazan iya
lissafowa ba saboda imgancinsa.
3.==> Ayaba: Ayaba na daya daga cikin abincin da a kaiwa
lakabi da ‘Binding foods’ a turance. Ma’ana, suna taimakawa wajen karfafa
bahaya. Bayan haka, suna cike da sinadarin ‘Potassium’ wanda yana daga cikin
sinadaran da jiki ke rasawa a lokacin da ake zawo. Saboda haka a yi tanadin
ayaba.
4.==> Shinkafa: Abun harda su baiwar Allah shinkafa. Dadin
abun shine tana daya daga cikin abincin da aka fi ci a lokacin sallah. Sai dai idan ana so a yi amfani da
ita wajen tsayarda zawo, toh za’a ci ta ne gaya, babu miya, babu wasali.
5.==> Nono Kindirmo ko yogurt: Akwai ‘bacteria’ masu kyau da ke taimakawa
wajen daidaita yadda bahaya ke haduwa a cikin ciki. Rasa wasu daga cikin
wadannan bacteria na sakar da bahaya. Shan Nono na taimaka wajen mayarda
wadanda aka rasa.
6.==> Gasasshen biredi: Cin gasasshen biredi zalla shi na taimakawa
wajen karfafa bahaya, kuma yana taimakawa wajen kara karfin da aka rasa a yayin da ake zawo.
Karanta: Matsalar Ciwon Sanyi Ga Mace
Abubuwan da ba za’a ci ba har sai zawo ya tsaya:
·
Gyada
·
Ridi
·
Wake
·
Abinci mai
dandano da yawa
·
Soyayyan
abinci
·
Abinci mai
zaki da yawa
·
Kayan
itace
·
Abinci mai
yaji, dss.
Shin akwai wani hanya da za’a bi wajen
magance sakewar ciki wato gudawa cikin kankanin lokaci wadda ban ambata ba a
cikin wannan kasidar zaku iya gaya mana naku ra’ayin ko kuma fasahar ta hanyar
ajiye comment a kasa.. Allah yasa mu dace..Ameen!
-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Za'a iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:
Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan
Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
No comments:
Post a Comment