Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

yanda zakayi dowloading video a facebook

Assalamu Alaikum


Yau zamu koyi yanda ake downloading na video a facebook da wayar salula cikin sauki. Akwai video da dama a facebook wanda yan uwa da abonkan arziki ke sawa wanda zakaji dadi in har zaka samu a wayanka dan gani ko wani lokaci amma saboda wasu daliloli bazaka iya downloading nasa ba. Insha Allah yau ni Muhammad Abba Gana zan nuna muku yanda zakuyi downloading na video a facebook cikin sauki, zamuyi amfani da wani Application a turance mai suna ‘video Dowloader for facebook’ yana daya daga cikin hanya mafi sauki dake taimakawa wajen saukar da video a facebook.
Matakai da zaka bi wajen downloading na video a facebook:

- Sauke ka shigar (download and install) video downloader for facebook sannan ka bude, zaka iya samu a google playstore ‘click on browse facebook’
- Shiga Facebook naka sannan ka duba bangon ka wato walls a turance
- Ka bude video da kake so ka saukar
- Sai ka danna ’yes to download video’ ma’ana na yarda na saukar zai dan dau lokaci ya dogara da nauyinsa. In ya gama----
- Shikenan ka dubi dakin nuna zane-zane wanda akafi sani da gallery a turance zaka samesa a wajen
Bayanin kula
- Wannan application din a Facebook kawai yake aiki
- Kafin kayi amfani da application nan ka tabbatar da kai shekara sha biyar 15 years a turance.
In ka samu wannan post da ban sha’awa taimaka ka turawa yan uwan da abokan arziki dan su karu.

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Za'a iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan


Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive