Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan filin namu na Duniyan Fsaha. Uwargida tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya, So da yawa mutane kan dauki suga a matsayin abinci ne, kawai ba tare da tunanin ana iya amfani da ita wajen gyaran jiki ba. Tabbas an fi amfani da siga a matsayin abinci, amma idan aka tsaya a matsayin abinci sai na ce lallai har yanzu an bar wasu a baya. Siga tana da matukar amfani wajen kawata jiki, domin tana fitar da dattin jiki da ko kin yi amfani da sabulu ba zai fitar da wannan dattin jikin ba. So da yawa ana amfani ne da wannan hadin ga amare, daga nan sai a ki ci gaba da shi. A wannan mako mun taho muku da matakan da za ki bi wajen amfani da suga don gyaran jikinki. Muna fata za ki bi bayanin sau da kafa. A sha karatu lafiya:
Kayan hadi:
• Ruwan lemo guda biyu
• Babban cokali daya na zuma
• Siga kashi daya bisa hudun kofin da ake shan shayi (¼)
• Man banilla (don ya bayar da kamshi)
Yadda ake hadawa:
Ki hada kayan hadin da na lissafo a sama cikin kwano ko roba. Daga nan sai ki gauraya su. Sannan ki shafa a fuska da kuma sauran jikinki. Sai ki fara gogawa da soso mai kaushikaushi, za ki ga datti yana fita, idan dattin ya fita sosai, sai ki yi wanka da sabulu. Yin wanka da sabulun zai sanya fatarki ta yi yalki da santsi da kuma sheki. Kada ki manta ki
sanya sauran a na’urar firij. Za ki iya amfani da shi na tsawon wata uku, sai dai ki tabbata yana cikin firij. Ba kullum ake amfani da wannan hadin ba, za ki iya amfani da shi sau biyu a sati. Ana amfani da wannan hadin ne musamman ga fata mai gautsi. Wannan hadin yana magani
kyesbi da ciwon fata na ‘psoriasis’. Ki guji sanya wannan hadin a wajen da yake da ciwo. Kada ki bari ya shiga idanunki, hakan zai iya haifar miki da matsala. In kin samu wannan post din da muhimmanci ki taimaka ki turawa yan uwa su anfana.
No comments:
Post a Comment