Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Farfesun gandaAssalamu alaikum uwargida tare da fatan alheri. A yau na kawo muku yadda ake hada farfesun ganda, walau gandar akuya ko ta shanu domin sanya kunnen maigida motsi a kodayaushe. Ina fatan kuma ana gwada wadannan girke-girke da muke kawo muku domin neman kwarewa a harkar girki. Abubuwan da za a bukata • Ganda •Attarugu •Albasa •Tumatiri • Nutmeg •Tafarnuwa •Maggi • kori • Kayan kamshi • Tukunyar dafa ganda (Pressure cooker) Hadi Bayan uwargida ta wanke ganda da ruwan kanwa domin cire karni, sai ta zuba a tukunyar dafa ganda domin samun farfesu mai laushi . Sai ta yayyanka albasa da tumatiri. Ta jajjaga attarugu daidai misali da tafarnuwa. Sai ta daka garin nutmeg ta zuba da maggi da kori da thyme. Sannan sai ta zuba ruwa daidai misali ta rufe. Sai ta jira ya nuna na tsawon awa daya. Sannan ta sauke. Ana son cin wannan girkin da safe ko da dare. Wannan irin girki, shi ne, wanda ya fi dacewa da masu son rage kiba. Domin ganda ba ta dauke da sinadarin dada kiba, illa a ci kawai don dadi. Tafarnuwar da aka sanya a cikin girkin na rage mura da kuma kare wadansu cututtuka kamar su mura da sanyi da sauransu. Ana son a rika girka irin wannan girki ga maijego, domin samun ruwan nono da karin koshin lafiya. Da fatan wannan girki zai sanya kunnen mai gida motsi. Ga dadi ga kuma arhar kayan girki. A sha lagwada lafiya.


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

1 comment:

  1. Way cool! Some extremely valid points! I appreciate you writing
    this article plus the rest of the website is very good.

    ReplyDelete

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive