Amfani da gishiri wata hanya ce ta gyaran jiki, alokaci guda yana kawar da gajiya da kuma bada kuzari. Tarihi ya nuna tun shekara ta 3150 kafin zuwan Annabi Isa al’ummar kasar Masar suke amfani da ruwan teku mai dauke da gishiri wajen inganta lafiyar jikinsu. A shekara ta 400 kafin zuwan Annabi Isa kuma mutanen kasar Girka suka fara amfani da gishiri wajen gyaran jiki, al’amarin ya rika tafiya da zamani wanda har zuwa yau ake kara fito da sababbin hanyoyin amfani da gishiri wajen gyaran jiki.
A wannan makon mun taho miki da matakan da za ki wajen amfani da gishiri don gyaran jikinki.
Akwai bukatar ki samu gishirin da ake kira ‘sea salt’ ko ‘rock salt’, wannan gishiri yana kunshe da sinadarin ‘sodium’ da kuma ‘chloride’, sannan ki nemi gishirin da ake kira ‘Epsom salt’, wannan gishirin yana kunshe da sinadarin ‘magnesium’ da kuma ‘sulfate’, haka za ki nemi gishirin da ake ‘dead sea salt’, wannan gishiri kuma yana kunshe da sinadarin ‘magnesium’ da ‘sodium’ da ‘calcium’ da ‘potassium’ da ‘chloride’ da kuma ‘bromide’, sannan ki nemi bakar soda, mai kunshe da sinadarin ‘bicarbonate’, sai kuma man ‘essential oil’. Sau da dama mutane suna amfani da sinadarin Borad a matsayin kayan hadi lokacin da suke hada sinadaran da za su sanya a ruwan gishiri don gyaran jiki, to gaskiya amfani da sinadarin Borad yana haifar da matsala a jiki.
Kayan hadi:

Cikin kofin shan ruwa na gishirin ‘rock salt’ Cikin kofin sha ruwa daya na gishirin ‘epsom salt’ Cokali biyu na bakar soda
digo 15 na man essential, misali; Labender da Rose da Peppermint da Citrus. Sai dai a tabbata an narkar da man sosai a cikin ruwan da za a yi wankan da shi.
Matakai:
(a) Ki samu babban kwano ko babbar roba, sai ki hada dukkan gishirin da na lissafa a sama, bayan nan sai ki zuba bakar soda, sannan ki gauraya sosai, daga nan sai ki zuba man essential, idan kin yi hakan sai ki sake gaurayawa sosai.
(b) Gauraya rabin kofin sinadaran da kika hada a (1) cikin ruwan da za ki wanka da shi. Ba a so ki yi wanka da ruwa mai sanyi da yawa, haka ba a so ki yi amfani da mai zafi. Ki yi amfani da ruwa mai dumi. Idan kina da bandaki na zamani, wanda akwai kwanon wanka (Baths) za ki yi cika shi da ruwa sannan ki zuba sinadaran (1) da yawa. Idan kin yi hakan sai ki shiga ciki, a lokaci guda ki shafe kamar minti talatin ko awa daya a ciki, yin hakan zai kara wa fatarki haske da laushi da kuma taushi; zai kuma kara miki kuzari.
No comments:
Post a Comment