Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

SIFFOFIN UWA TA GARI




ABUBUWAN DA SUKE CIKI


 Godiya
Gaisuwa
  Gabatarwa
Mace Tagari
Siffofin mace Tagari
Bayanin siffofin Mace Tagari
Bayani akan Lalle
Bayani akan ado
kisisina da kareraya
Damuwa da damuwarsa
Bayani akan girki

  §  Ya yar’uwata mace bata cika mace ba idan bata iya kisisina irin ta mata ba, kamar su kareraya, yanga da rigima. Kuma ki sani irin wadannan dabi’un su suke daukaka martabar mace a wurin mijinta acikin dukkan alamuran su, Magana ko tafiya ko kallo da makamantansu.

GODIYA
Dukkan godiya su tabbata ga Allah (S.W.T) Ubangijin Talikai bias ni’imominsa bayyanannu da boyayyu tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa da dukkan wanda sukabi tafarkinsa. Har zuwa ranar Alkiyama Ameen.
GAISUWA
Dukkan gaisuwa ga yan uwa musulmai maza da mata Allah ya hada mu a Aljannah. Baran manta Da:
v Albudullahi ahmad
v Abubakar Garba
v Abubakar sadeeq (takai)
v Ahmad bello Hassan
v  Beebah Wadata
v Habeebullah yareema usman
v  Rabiatu Sk Mashi
v Zainab isa
v Zahra bb
v  Faty Afreen
v Asma’u umar babayi
GABATARWA
Ina gabatar da wannan littafi wanda ya kunshi takaitaccen bayani akan iyaye mata. Domin a hakikanin gaskiya iyaye mata sun bambanta wajen tarbiyar ya’yansu Allah yasa mu dace, Ameen a karshe ina mika godiya da fatan alkairi ga malamina Abdullahi Mustafa a bisa shawarwarin daya bani har littafin ya kamala. 15/10/2016. Bayan haka wannan wata fadakarwace ga yanuwa mata zalla, ko zasu fadaka daga gurbatattun dabi’unda sukeyi a gidan aurensu. Muna rokon Allah ya daidaitamu bisa bin hanya madaidaiciya kuma ya shiryemu ya sanya mu cikin bayinsa salihai Ameen.
AURE
Da farko yake yar’uwa ki sani aure bautanena ubangiji ne. To amma mai yasa ku mata kuke banbanta yanayin zaman aurenku bayan Annabinmu dayane, domin da yawa daga cikin yan uwa mata basu dauki aure a matsayin bautaba wallahi. Bayan aure itace babban hanyar shigarki Al-jannah idan kikayi hakan kuma kika yarda da hakan to kinci riban duniya da kuma lahira.Allah yasa haka Ameen. Sannan ki sani yar’uwa duk wata ibada tana tareda jarrabawa musamman ma aure, domin zamane da ya kunshi farin ciki da bakin ciki, dadi. da mara dadi, hakuri da rashin hakuri, da sauran wasu abubuwan da basai na ambacesu ba, Yake yar’uwa ki sani aure anayinsa saboda wasu abubuwa da dama amma babban su shine natsuwa. Kuma natsuwa baya samuwa sai idan mace ta zama tagari shiyasa da yawa daga cikin maza basuda natsuwa saboda matansu ba nagari bane. Manzon Allah (S.A.W) yace duniya abin jin dadi ne, amma mafi alkhairin jin dadin duniya shine mace tagari, don haka ya yar’uwata idan harke ba mace tagari bace to ki sani baki da amfani a zaman gidan aurenki da mijinki idan kika sake baki gyara zamanki da mijinki ba, to wallahi zaki samu mummunana sakamako a wurin Allah. Allah ya karemu Ameen.
MACE TAGARI
 Mace ta gari za a same ta da:
    1.    KAMEWA: Daga duk wani abu da zai sosa wa maigidan ta rai, a kanta ne ko gidansa ko abincinsa da sauransu.
    2.     GASKIYA: In za ta yi magana ba ta qarya, domin samun riqe gidan gaba daya.
    3.    AMINCEWA: Duk abin da yake so ta yi ta amince, don yarda da cewa ba zai halakar da ita ba, tana qaunarsa.
    4.    TAWALU'U: Ta qanqar da kai gare shi koda kuwa tana da ilimi, arziqi da shekaru sama da shi, kamar dai Khadeejah R.A da Annabi (S.A.W)
     5.     NATSUWA: Kar ta riqa tuno abubuwan da suka gabata, kuma ta dena tsoron masu zuwa.
    6.     KUNYA: Ta riqa jin kunya, wannan ado ne gare ta, masamman in tana tare da mijinta a cikin jama'a, wannan zai qara masa qaunarta.
    7.     KWANCIYAR HANKALI: Mantawa da matsalolin rayuwa da qoqarin tura farin ciki ga mai gida koda suna cikin matsala.
    8.     GODIYA: Duk abin da ya zo da shi a nuna masa jin dadin zuwa da shi komai girmansa komai qanqantarsa.
   9.    HAQURI: A kan duk abin da zai bayyana daga miji (wannan ne kawai muka dauka alhali suna da yawa)   
   10.                       TSAYUWA QYAM: A wajen bauta da qarfafa mijin da 'yayan su.

    11.                       AMANA: Ta zama mai amana, kar ta yarda maigidan ta ya ga ha'incinta koda kuwa sau Daya ne, ta riqa gaya masa abin da za ta yi domin maganin shedan.‎
     12.                       CIKA ALQAWARI: Yana Daya daga adon mace da namiji.
     13.                        TSORON ALLAH: A duk abin da za ta yi.
     14.                       DANNE ZUCIYA: Yayin da aka baqanta mata rai.


Wadannan abubuwa guda 14 su suke nuna mace nagari, dan uwana kada ka riqa binciken qyalqyal banza, ke ma yar uwa ki dai na kallon kudi ki duba rayuwarki idan kin shiga gidansa, komai kudinsa in ba kwanciyar hankali ba za ki ji dadinsu ba. Biyayya ga miji ba mai iya wa sai mace ta tagari,da yawa mata suna so a ce su ne wadan da Annabi (S.A.W) ya sifanta dinnan da (Nagari) sai dai biyayyar ce ta yi qaranci, ko za a yi sai dai a gabansa in ya matsa an watsar kenan.

           Mace ta gari takan yi qoqarin ta zama wa mijinta aljannarsa ce, ba ta son ta ga gazawarta a idanunsa, don haka takan yi farin ciki in taga murmushinsa, takan damu matuqa in ta ga fushinsa ko da ba da ita yake ba, ba ta jinkiri a wajen abinci, kuma ta iya dafawa ba tare da almubazzaranci ba, ita ce amin taccen abokin shawararsa,mai iya riqe masa sirri, ba ta yarda wani ya sani ko waye kuwa, sannan ga taimako.


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive