Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Yadda ake hadin ‘Ardeb’



 Assalamu alaikum. Uwargida, tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. Na san mutane da dama ba su san me ake kira ‘ardeb’ ba. Wannan ardeb dai yana nan ne kamar lemun tsamiya. Kuma yana da alaka da mutanen Maiduguri. A irin wannan yanayi da muka shiga ana yawan hada wannan ‘ardeb’ din ko kuma jus din tsamiya, sannan a sanya shi ya yi sanyi domin sanyaya zuciya a lokacin zafi. Akwai hanyoyi biyu da ake bi don yin wannan hadin. A sha karatu lafiya. Abubuwan da ake bukata •Tsamiya • Siga •Masoro • Kanamfari •Citta • Ruwa Hadi A samu tsamiya a wanke tsaf ya fita sannan a jikata ta jiku sannan a daka kayan yaji; masoro da citta da kuma kanamfari. Sannan a dora tukunya a wuta, bayan tayi zafi, sannan a zuba sukari, har sai ya narke, sannan a zuba ruwa. A dauko wannan jikakkiyar tsamiyar a tace a zuba a cikin ruwan sukarin, sannan a tankade dakakken kayan yajin a zuba a gauraya sannan; Kuma sanya shi a gidan sanyi domin dandano ya fito sosai. dayan hadin kuma shi ne, a tafasa tsamiya tare da kayan yaji sannan a tace. A dora tukunya a wuta bayan tukunya tayi zafi, sannan a zuba sukari ana gaurayawa, har sai sukarin ya narke sannan a zuba ruwa da wannan tsamiyar da aka tace. Hadin ‘ardeb’ ya hadu. A sha lafiya.


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive