Home »
wayar salula
» ABUBUWA DA ZA AYI LA’AKARI DA SU KAFIN SIYAN WAYA KO ANDROID(SMARTPHONE)
ABUBUWA DA ZA AYI LA’AKARI DA SU KAFIN SIYAN WAYA KO ANDROID(SMARTPHONE)
ABUBUWA DA ZA AYI LA’AKARI DA SU KAFIN SIYAN WAYA KO ANDROID(SMARTPHONE)
ASSALAMA ALAIKUM……..Barkan mu da war haka insha Allah yau zamu tattauna a kan abubuwan da ya kamata muyi la’akari dasu kafin mu canza waya ko kuma mu siya sabo, Android waya ne da ta cika gari a wannan zamanin wacce zai yi wahala ka samu mutum uku wadanda suke rike da waya amma kuma ba a samu mai irinsa ba. Irin wadannan wayoyi sun cika ko’ina a fadin duniya, ga shi kuma kamfanonin da suke sarrafasu kullum kara fito da sababbi suke yi cikin kasuwa. Kodayake a irin tunani namu na bakaken fata kasancewar waya na da tsada shi ne ke nuna cewar wannan wayar tana da matukar kyau da kuma lafiya, wani lokutan kuma neman iyawa da bajinta da nuna isa shi ke sa mu mallaki waya wacce take da tsadar tsiya ba yin la’akari da me ke cikin wannan wayar ba ko kuma me wannan wayar zata iya yi mana nan gaba ba.
Wani abu kuma da yake daurewa jama’a da dama shine suna son su siya sabuwar waya, idan na samu kudi wace irin waya ya kamata na rike, ko kuma mene ne abin yin la’akari da shi idan ina son canza waya ko kuma sake siyan sabuwa. Amsoshin wannan tambayar ya danganta da me kake son yi da wayar ko cimma manufar wayan, domin wani yana yin la’kari da karfin wayar wurin rike wuta wato caji, wani kuma yana yin la’akari da kyau na hoto da take dauka wato clean camera a turance, wani kuma yana yin la’akari da karfin network da take da shi wato high network capacity, wani kuma yana yin la’akari da girman fuskarta waro screen size, da dai makamantan irin su. A cikin wannan darasi zan kawo mana abubuwa da jama’a suke yin la’akari da su wurin siyan wayar wato taba ka latsa wanda akafi sani da android ko smartphone a turance.
1- KAMARA DAUKANSAUTI (CAMERA AND AUDIO RECORD)
Sauti da kamara Hakika wadannan abubuwa guda biyu sun karawa wayoyin tafi da gidanka daraja sosai, kusan a yanzu mutane da dama suna yin amfani da kamarar jikin wayoyinsu domin daukar shagulgulan biki da suna da taron siyasa, wa’azi, wasan kwaikwayo da sauran makamantansu. Wannan dalilin ne ya sanya wayoyi a wannan lokacin suke kara yin tsada, duk da cewar mutane da dama basu cika kiyaye haka ba. Kusan a yanzu akwai wayoyin da ake da su wadanda saboda karfi da kyau Yanayin hotuna da suke dauka hatta mawaka suna amfani da su wurin shirya wakokinsu. Haka yan jarida a wannan lokaci suna yin amfani da wayoyi wurin nado sauti da zasu iya kai rahoto da shi. Duk da cewar karfin wata wayar ya fi na wata, amma waya da kamara da kayan daukan sautin da ke jikinta ya mayar da mutane ‘yan jaridan tafi da gidanka amma wasu ba su sani ba. To ba kowace waya bace ta ciki inganci a kan haka. Sannan idan ka san kai baka damu da kyau na hoto ba to ba sai ka sayi waya mai tsada ba.
2- KAURI DA NAUYI (OHONE WIEGHT)
Kauri da nauyin waya abu ne mai muhimmanci sosai a lokacin da mutum zai sayi waya ko tablet a turance. Kauri dai an fi lura da shi akan komai, wani lokaci sirantaka a wurin kayan computer bai cika bayar kaya masu inganci ba a wani lokaci. Saboda haka ya danganta gare ka idan kana son kyau fiye da inganci sai ka tsallaka siriyar waya ko tablet abunka. Kodayake wadansu wayoyin suna da jikin karfe ne saboda haka tun kafin kabar wurin siya ka tabbatar ka duba don kada karfen ne ya sata tayi nauyi.
3- MANHAJOJIN (Operating System) DA WAYA TAKE AMFANI DA
SU (INSTALLED OPERATING SYSTEM)
Babbar Manhajar wato os a turance da take sarrafa komai da ke jikin waya shi ake kira da Operating System, shi yake lura da hatta maballan da kake tabawa wurin kunnawa da kashewa, shi yake lura da sauti da kalan da yake fita a wayar bai tsaya nan ba kusan shine waya saboda komai yana karkashin ikon sane. To lallai wurin siyan waya yana da kyau ka duba da kyau domin ka san wane irin manhaja ce a cikin wannan wayar. Kamar yadda da yawa daga cikin mu suka sani cewar wayoyin da muke rikewa suna da banbanci wurin gininsu da kuma wani company nine ya buga Kunga dai wayoyi idan ya zo ga maganar Operating System akwai na Android, sannan ga iOS, sai Microsoft Phone 7, sai Blackberry ga kuma webOS da Symbian, akwai java dukkan wadannan da na lissafo da yawa daga cikin mu sun dauka cewar waya ce. A a kamfani da yake yin karfe da kyan da suke jikin waya daban sannan manhajar da ake saka mata da ba. Wadancan sunaye da aka ji na lissafo mutane sun fi sabawa da su a matsayin waya maimakon Babbar Manhaja ce.
4- GIRMAN FUSKAR WAYAR (SCREEN SIZE)
A wurin siyan waya ko tablet mutane suna yin la’akari da girman fuskar wayar wato (screen). Wani yafi so ya ga waya faskekiya a wurin sa ko a aljihunsa, wani kuma baya son ganin haka. To shi dai maganar fuskar waya ra’ayi ne, kuma wanda yayi maka ba dole ba ne yayi wa wani. Amma dai a zahiri idan kasan kai mutum ne mai son wayarka ta rika zama da caji to girman fuskar waya da barin ta cikin haske sosai na taimakawa wurin sanye caji da wuri.
5- GIRMAN WURIN ADANA BAYANAI (FILE STORAGE CAPACITY)
Mafi yawan kanfanonin da suke yin wayoyi da tablet a wannan zamanin suna kokarin ganin sun yi mata mazubi da ya kai girman gig 16GB, wanda zai baka dama domin a jiyar hotuna da rubutu da sauti da hotuna masu motsi wato video. Kodayake wadansu saboda yanayin yadda suke tara abubuwa a cikin wayoyinsu suna bukatar karin abubuwa a ciki. To a nan yana da kyau ka sani wayoyin da kamfani Apple suke yi su basa bada ramin kara ma’ajiya wato Memory, saboda haka idan kasan kai mai sun ajiyar abubuwa na tarkce ne sai ka nemi koda wayar Apple amma mai mafi girman mazubi a cikinsu.
6- KANA NAN MANHAJOJI (APPLICATION CAPACITY STORE)
Daya daga cikin abin wasu mutane da dama suke yin la’akari da shi shine idan na sayi waya iri kaza shin dawe application ne zan iya aiki ma;ana zai iya daukawa, kusan a wannan lokaci da muke ciki kasancewar wayoyin Android sun fi yawa da kuma saukin koyan yadda ake kirkiran manhajojinsu, yasa mutane da dama suke son siyar wayar Android. Amma kuma idan aka zo ga zafafan Manhajoji to sai muce manhajojin da ake amfani da su a waya kirar Apple sun fi shahara da kwarjini. Misalia shagon Apple akwai manhajoji dubu dari uku na kyauta da kuma na siyarwa, a kuma shagon Android akwai manhajoji dubu dari biyu da hamsin na kyauta da kuma siyarwa. Suma sauran manhajoji irin su Blackberry da makamantansu suma suna da shagunan da ake samun manhajojinsu saidai ba su kai na Apple da Android yawa ba saboda yanda ake yawan amfani da su a wannan zamamin namu.
7- KARFIN SHIGA INTERNET (INTERNET SPEED)
Kusan dukkan wayoyin tafi da kidan ka suna zuwa da tsarin sadarwa maras waya wato wireless a turnce wanda ya ke basu damar iya kulla alaka tsakaninsu da ko kamfanin layukansu ko kuma hanyoyin shiga intanet da yake gida ko kuma ofis da dai makamantansu. Irin wadannan hanyar da ake amfani da ita domin samun sinadarin shiga intanet ba tare da amfani da layin waya ba shine ta hanyar amfani da Wai-Fai (Wireless Fidility). Amma yana da kyau wanda zai sayi waya a wannan lokaci ya san cewar yanzu ma muna karni na uku bane 3G (Third Generation) ta wurin shiga intanet, a’a a wannan kasa yanzu haka akwai kamfanoni da suka tsallaka karni na hudu 4G. Wayoyin da aka yi a baya sun fara ne da 1G sai kuma suka shiga 2G wanda irin wadannan wayoyin ba sa ba mutum damar shiga intanet da sauri, koda kuwa a inda mutum ya ke akwai network mai kyau da karfi. Daga baya suka shigo da 3G wanda yake bamu damar har kallon hotuna masu motsi (video) muke yi ba
tare da yana tsayawa ba. Saboda haka yanzu mafi yawan wayoyin da ake yi suna baka damar amfani da karfin network na 3G da 4G, sai a kiyaye idan an je siya.
8- DADEWAR BATIRI (BATTERY CHARGE RETAIN)
Lallai ko ba a fada maka ba kasan cewar batir yana da matukar muhimmamci a jikin waya domin duk irin aikin da waya zata yi maka idan har batirin wayar baya dadewa ya zama shiririta. Shi yasa mafi yawan kamfanonin da suke kirkirar waya suka fi mayar da hankali wurin ganin batar na dadewa, duk da irin kurakurai da ake samu wadansu kamfanonin suna yi sai ka samu kamfani yayi waya kuma cikawa batirin sinadari da idan ya ji rana zai kama da wuta, amma dai suna iya kokarin su. Zaka samu wayoyi a wannan lokaci ana inganta batirinsu har kaga waya tana iya kwana uku tana aiki, kodayake ba kowa yasan wayoyin wannan lokacin suna haka ba, kasancewar idan muka sayi waya bama karanta takardar da take zuwa da ita. Wannan shine abubuwan da zan iya kawo muku wadanda sune abubuwan da ya kamata mu rika yin la’kari da su wurin sayin waya sabo koh canzawa.
mawallafi: Faty Afreen
unana fatimah YB hassan wacce akafi sani da faty Afreen.. Ni yar garin katsina ce kuma an haifeni acan..amma ynxu HK inna zama a jos..kuma inna karatu a bayero university kano inna karantar BOTANY.. Ni marubuciyar littafan Hausa ce a yanar gizo.. Inna da sauqin kai kuma innaso naga nayi qawaye da abokai kuma naga nasasu farinciki amma na tsani a batan rai.. Inna daya daga cikin wa anda suka assasa *DUNIYAN FASAHA* (gidane wa kowa Wanda ya shirya koyan abubuwa na yau da kullun) Ku kasance tare damu domin samun nishadantuwa da kuma taimakon Ku akan matsalolinku.
No comments:
Post a Comment