Folder wanda a turance ma’anarsa wani fasaha ne da ke amfani dashi wajen sakaye kaya a cikin kwanfuta, wato shi folder waje ne da ake zuba, tattara ko kuma ajiyar kaya a cikin kwanfuta waɗanda aka fi sani da ‘data’ a turance. Ita folder ta na daga cikin abubuwa masu muhimmanci a cikin kwanfuta, domin kusan da ita folder ake shirya dukkanin kaya wato document na kwanfuta a shirya su kamar yadda ake shirya kaya a file na ofis ninki ninki ko kuma yanda ake shirya kaya acikin akwati. Ita folder kamar yadda muka faɗa kamar ma zubi ne, saboda haka, kusan ita kanta Kwamfutar ana shirya komai ne bisa tsari a cikin foldoji daban-daban. Haka kuma folder ta na iya shiga cikin wata folder, wa ta ma a cikin wata ya dangana da yanda kake bukatar ajiye ko kuma adana kayanka.
Kusan dukkanin application da suke cikin kwanfuta duk suna cikin folder ne a shirye. Shi ya sa kake iya ganin kayan kwanfuta suna ba ka sha’awa domin suna killace ne. Ɗauki misalin ofis ne babu drawer da za a iya ajiyar takardu, duk takardar da ta shigo wannan ofishin sai dai a ajiye ta a ƙasa, ko’ina takardu sun yi kaca-kaca a ciki. Na san ba sai an faɗama mai karatu ba cewar wannan ofishin komai kyanshi ba kintsattse ba ne. To, da waɗanda suka ƙirƙiri kwanfuta ba su yi tsarin folder ba to da wanda zai yi amfani da ita da bai san inda zai fara ba. haka ma in mun dauki misali da akwati wato wajen jera kaya duk kayanda ka dinka koka goge in har suna ajiye a kasa bazasu taba kyau ba haka kuma zai iya bacewa.
A misalin mutumin da yake amfani da kwanfuta kuma shi mai ɗaukar hoto ne, to waɗanda su ka ƙirƙiri Operating System a turance sun tsara shi a kan ya yi amfani da ‘My Picture Folder’ a cikin ita wannan folder zai kuma iya ƙirƙirar wata folder ya kira ta da misalin sunan shi wato son ranka, sannan kuma zai iya ƙirƙirar wata folder a cikin ita folder ya saka ma ta sunan hoton da ya ɗauka a misalin ya kira folder da AUREN MALLAM MUSA, sannan ya zuba waɗannan hotuna a cikin ta. Yin haka ya tabbatar da cewar duk lokacin da ya zo neman hotunan da ya ɗauka a bikin auren mallam musa to zai je kai tsaye cikin my picture – folder mai sunansa – AUREN MALLAM MUSA. Haka wanda yake son ya zuwa karatu a cikin Kwamfutar shi, kamar yana son ya saka karatun tafsiri na Sheikh Abubakar Muktar da na Sheikh Abubakar Gumi da na Sheikh Abubakar gero to zai shiga cikin folder ‘my music’ daga nan sai ya ƙirƙiri wata folder ya saka ma ta suna Tafsir daga nan sai ya shiga cikin wannan folder daka bude a baya ya ƙara ƙirƙirar wata ya saka mata sunan malamin farko. Misali Sheikh Abubakar Muktar 2012 bayan ka gama sa ka sunan sai ka buɗe ta ka zuba karatun a ciki. To, duk lokacin da kake son ka ɗauko ko ka saurari karatun ɗaya daga cikin waɗancan malaman sai ka shiga my music – tafsir – Sheikh Abubakar Abubakar gero 2011. Haka rubuce-rubucen da mutane suke yi a cikin kwanfuta ko kuma abubuwan da ka ɗauko na karatu a intanet suma haka ake son ka shirya su daki-daki a cikin kowace folder ta na wakiltar document da suke cikin ta.
Yaya Ake Ƙirƙirar Folder Ana iya ƙirƙirar folder ta wurare da dama a kuma kowane wuri a cikin kwanfuta sai dai yana da kyau duk lokacin da kake son ka ƙirƙiri folder to ka tabbatar wurin ba shi da alaƙa da wurin da ba a son a ajiye wani abu ‘reserve place’ wato a turance. Waɗannan wurare ne da waɗanda su ka yi Operating System a turance ba sa son kowa ya saka wani abu domin saka wani abu a cikin wurin zai iya cin karo da wani tsari da zai hargitsa kwanfutan ka. Wanda yake son ya ƙirƙiri folder a fuskar kwanfutanka wato Desktop zai bi wannan hanyar >> danna hannun dama Right Click a jikin sararin fuskar kwanfuta wato Desktop >> sai ka danna New >> Sai ka latsa Folder. Za ka ga ya kawo maka folder amma wurin sunanta ya sa ka ma ka suna ‘New Folder’ nan take sai ka rubuta sunan da kake buƙata son ranka, kamar ‘beebah’s Files’. Sai ka danna ‘Enter Key’ da ke jikin ‘keyboard’ na kwanfutanka ko kuma ka latsa wani wuri a jikin Desktop ɗinka da ‘left click’. Wannan shi ne hanyar da ake bi a ƙirƙiri folder a cikin kwanfuta kuma da wannan hanyar ce a kowane wuri ka ke son ka yi folder haka za ka yi. Wanda kuma ya yi kuskuren sa ka suna kuma yana son ya gyara sunan, to, zai je kan ita folder daya bude ne ya yi right click a kanta sai ya taɓa rename wanda a rubuce sai ya gyara sunan sannan ya taɓba wani wuri na daban gafen folder ɗin.
No comments:
Post a Comment