Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

WAYAR HANNUNKA NA YIN ZAFI? GA DALILAI DA YADDA ZA KA MAGANCE MATSALAR CIKIN SAUKI



ASSALAMU ALAIKUM...Muhammad Abba Gana daga DUNIYAN FASAHA ke muku fatan alkairi, insha Allah yau zamu tattauna batu a kan wayar hannu da yake zafi, Wani abu da ya ke yawan damun masu amfani da wayoyin zamani hannu musamman irin wadannan wayoyin taba ka latsa wato Smartphones ko android a turance shi ne yawan yin zafi kamar zata kona hannu ko kuma dimi da mutum bai samun kwanciyar hankali da shi. Wani lokutan a wurin maza sai su ce idan suka saka ta a cikin aljihunsu sai ta dau zafi, wani lokaci ma sai da ka dauko ka duba kawai sai ka ga ai ta mutu saboda da irin wannan zafi da ta dauka na tsahon lokuta. A wannan darasi da zamu yi zamu fada muku abubuwan da ke kawo waya ta rika yin zafi da kuma hanyoyin da zamu kiyaye tare da yanda zamu magance su. Masu yawan sauraron labarai sun sami labarin kiranye da janye wayar kamfanin Samsung suka yi a ‘yan kwanakin baya kasancewar sabuwar wayar da ta shigo kasuwa haka nan kawai sai ta kama da wuta saboda matsala da aka samu wurin gina batirin ta. Wannan ya sanya muka ga ya dace muyi muku bayani game da irin zafin da idan kaji wayarka tana yi ka gane cewar akwai matsala.


Waya Na Yin Dumi


Bako ko sabon mai amfani da wayoyin zamani wato smartphone su sani cewar irin wannan wayar tana yi dumi wanda ya sha banban da irin kananan wayoyin da suke amfani da su a zamanin baya. Mu sani wayoyin zamani kayan wutan lantarki ne, saboda haka don kaji tayi dumi ka sani ba wani matsala babbae ba ne. Amma kuma idan kaji tayi zafi wanda kake jin tsoron zai iya lalata ta, ko kuma ta yi zafin da kake jin tsoron za ta iya fashewa ko ma ta la’anta masu amfani da ita to lallai ya dace ka kasha ta, domin abin da zamu tattauna ke nan. Duk da cewar mafi yawan abin da zan fada sun fi karfi ga wayoyi masu amfani da fasahar wayar Android/smartphones domin kusan su aka fi amfani da su a wannan nahiya tamu ta Afirka musamman Najeriya ta Arewa a zamanin yanzu.


Ta wane wuri waya ke yin zafi?


Abu na farko da ya kamata mu fara kiyayewa shi ne ta wani wuri wayar take fara daukan zafi? Duk da cewar nasan ba kowa bane zai iya lura ko sa hankali ba, amma dai zai iya yiwuwa ta batir ne ko kuma cajar wayar ita take haifarwa. To amma bari mu zayyano wuraren da waya zata iya daukar zafi ko kuma ta inda ake iya gane cewar waya tana zafi ba dumi ba domin akwai banbanci.


Zafin zata iya kasan cewa wurin caji ne


Wani lokaci zaka samu wayar bata yin zafi ko fara yin dumi sai bayan ka saka ta a cikin chaji, wannan matsalar tafi faruwa a lokacin da mutum ya ke amfani da wata cajar da ba ta asalin da wayar ta zo da shi ba. Domin mutane da yawa basa fahimtar cewar ba kowace irin caja ba ce ke yiwa kowace irin waya caji koda kuwa bakin su iri daya ne ko da kuwa kamfani daya ne da wayar mutukar ba irin na wayar bane. Ita waya tana karbar wuta ne wanda aka kira da Direct Current domin ajiyar wutar lantarki cikin batirin waya ko laptop da dai makamantan kayan na’uran zamani da suke amfani da batir domin su yi aiki. Kowace waya tana da nata karfin wutar da ake son ya caza ta. Shi yasa zaka samu wata wayar idan aka aro mata caja sai yayi awanni bai iya cika wayar ba, wani kuma cikin dan kankanin lokaci sai ya cika maka wayar ka. To wannan matsalace sosai domin yin amfani da cajar wayar da ya ke sata tayi caji da wuri yana bata batir shi kanshi ga kuma bata injin da yake lura da karfin shigar wuta a cikin wayar salulan. amma wannan ya ke nuna mana cewar idan muka tsinci wayarmu na daukan zafi daga bakin caja mu sami wata caja irin ta wayar ko muce follow come kamar yadda muke fadi, idan muka gwada muka ga bata zafin ko dimi to kunga mun gane matsalar. idan kuwa muka gwada muka ga har yanzu dai tana zafi ya nuna kodai batir din shi ke dawo da wutar da ke shiga cikinsa, ko kuma daga charging point ne wato inda ake jona chajar din da kansa.


Bayan wayar ke yin zafi


Duk lokacin da ka ji jikin wayarka wato gidan batirinta, to ka sani ba wayar bace ke da matsala batirin wayar shine ke kawo zafi a wayar. To idan ka tabbatar da haka ka samo wani batiri irin nata ka saka ka gwada idan ka ji wannan batirin baya zafi to sai ka je ka sayo wani sabo ka canza in kuma yana kan yi ka sake samo wata ka kwada zayyu wancan din irin naka ne.


Yin zafi ta baya amma saman batiri


In kuma ka duba kaga wayar tana yin zafi ta baya amma kuma sai ka lura da cewar ba daga wurin zaman batirin ba ne, to zai iya yuwuwa ita karan kanta wayar ce ke yin zafi. Idan kuwa haka ne to bari in dan lissafo wasu wuraren da zamu taba ko lura domin mu gane ta ina zafin ke  asalin farawa?
Wayar na zafi ta wurin sauraron magana (Speaker)
Wasu lokaci za ka ji idan kana waya sai kaji kunnen ka ya dau zafi ta wurin speaker to irin wannan matalar ba wai zafi da konewar kunnan naka a ke ji ba wannan zafi zai iya shafar lafiyar kwakwalwarka saboda haka duk lokacin da ka ke amsa waya a kunneka na zafi to ka canza wayar ko kuma ka nemi headphone mai kyau ka siya ka rika amfani da shi.


Lalataccen Batiri


Batiri mara kyau ko lalacewar ta yana kawo zafi sosai a wayoyinmu wanda shima yana daya daga cikin manyan matsaloli mai zaman kanta. Idan kana da tabbacin cewa batir din wayarka ya fara lalacewa ta wurin ganin yana zubar da ruwa ko kuma yana dan kumbura to kana bukatar ka cireshi a jikin wayarka ka canza shi. Mu sani yin amfani da kumburarren batiri akwai hatsari sosai domin zai iya yin bidiga ko kamawa da wuta kodawane lokaci, kuma wannan yayi sanadiyar mutuwar mutane da yawa ko kuma dukiya saboda abu ne mai matukar hatsari in ya pashe.



Fuskar wayar ke yin zafi wato Screen a turance


Wani lokaci zaka samu idan kana amsa waya fuskar wayar ne ke daukan zafi, to idan haka na faruwa akwai abubuwa da zamu lissafo wadanda ya kamata mu yi domin hana wayar tamu yin wannan zafi ta fuska suna nan kamar haka.


Boyayyun Abubuwan da ke sa waya yin zafi wanda baka san dasu ba


Tun da mun fado wadansu hanyoyi da ake iya gane waya na yin zafi a zahiri, to bari mu fado wadansu abubuwa ko hanyoyi da suke sanya ita wayar ta rika yin zafi wanda ba kowani mutane suke fahimta ba.


Application da yawa suna aiki a lokaci guda


Wani lokutan ba wadancan abubuwan da muka lissafo a baya su suke sa waya ta rika yin zafi  kowani lokaci ba, yawan kunna application na wayar da kuma barinsu a kunne kodawane wasu lokutan shima yana sa waya ta rika yin zafi. Saboda haka yake da kyau duk lokacin da mutum yaji wayarsa na yawan yin zafi ya ringa bude Application Manager din sa yana goge budaddun application wannan zai taimaka masa sosai. Akwai wadansu application na musaman wadanda suke yin irin wannan aiki kodayake suna da tasu matsalar suma amma dai mu sami application da yake irin wannan aikin domin taimakawa wayar ta mu.


Aikin Abu mai nauyi da tsawo da cin lokaci


Babu shakka cewar wayoyin Android akwai dadi wurin yin amfani da su musamman idan muka yi la’akari da irin abubuwan da ake iya yi da su, kamar daura musu bidiyo mai nauyi, ko kuma kallon bidiyo mai tsawo, ko daura game mai nauyi da kuma amfani da shi ta wasu bangarorin, ga sauraron sauti na karatu koh nishadi, ga yadda muke shiga intanet da duba imel da dai makamantansu dukkansu kuma akan wannan ‘yar karamar wayar da bata wuce ta zauna a tafin hannunka ba. Saboda haka mu san dace wa kallo ko sauraron abu mai nauyi zai iya sanya waya tayi matukar zafi musamman idan tana rike a hannunmu ne domin ga zafin hannu ga na riko ga kuma nata zafin na kanta, saboda haka yana da kyau mu guji matsawa wayoyin mu da kallon bidiyo masu tsawo ko kuma buga game masu nauyi musamman irin wadanda suke bukatar higher configuration wurin amfani da su ko kuma daura su a jikin wayoyinmu na salula.


Rashin samun Iska


Daya daga cikin abin da zai iya sa waya ta dau zafi akwai karancin isaka wanda ya kawo wadansu dalilai da zamu lissafa wadanda suma suna taimakawa wurin sa waya tayi zafi, ga kadan daga ciki.


Sakata a Aljihu


Wani lokacin wayoyinmu suna daukan zafi saboda yawan sawa da mukeyi a aljihu. Mu kan mu lokacin sanyi idan muka fito waje muna tafiya sai sanyi ya dame mu mukan saka hannunmu a cikin aljihu domin muji dimi. To yana da kyau duk lokacin da ka saka wayar ka a cikin aljihu sannan ka ji ta fara zafi to ka cirota na wani dan lokaci domin ta dan numfasa. Wannan zai taimaka sosai wurin hana wayar lalacewa ko kamawa da wuta ko wasu matsaloli makamancin haka.


Sanya Rigar Waya


Rigunan da ake sakawa waya wato jacket a turance suna taimaka mana wurin kiyaye wayar daga fashewa ko kuma zubar wani abu mai ruwa a jikinta amma kuma idan ba mun samu rigar wayar da ta dace da wayarba zai iya taimakawa wurin sa wayar ta yi zafi. Akwai wuraren da waya take amfani da shi  domin ta numfasa ko kuma samun iska to idan ba an sami rigar da aka yi ta musamman domin ita wayar ba za a iya samun matsala babba Allay ya kiyaye.


Tsohon Application


Barin tsohon Application a jikin waya yana iya cin karo da sabon tsari a jikin wayar wanda zai iya sanya waya ta yi zafi. Shi yasa kashi 60% na wayoyin ‘yan Afirka musamman Hausawan mu suna amfani da application ne da wani ya saukar a wayarsa ba zuwa suke yi kai tsaye su saukar ba. Wani lokaci ma zaka samu wani yana mafani da application amma kuma wani ne ya saka mishi bai kuma taba hawa intanet ba ballantana ya sabunta wannan Application. To barin tsofaffin applications a cikin waya zai kawo matsalar sanya wayar ta rika yin zafi.


Rashin samun Hutun Waya


Mu sani waya tana bukatar hutu kamar dana dam ko da na ‘yan mintuna ne, idan kana daga cikin wadanda suke kunnan waya basa kashewa kodawane lokaci tana kunne, idan batir dinta ya kusan karewa sai ka jona mata caji to wani lokaci rashin hutunta zai iya kawo matsalar zafi ko wasu yan matsaloli.


Haduwar Waya da Ruwa


Idan ka san wani lokaci kana shiga wanka da waya, ko kuma irin ruwan sama ya doke ka kuma wayar na tare da kai, ko kuma aka yi rashin sa a ta fada cikin ruwa wani abu mai ruwa, to koda ka gyara wayar zai iya yuwuwa wayar ta rika yin zafi, domin haduwar ruwa da kayan lantarki kan iya haifar da matsaloli masu yawa. Akwai wata ‘yar karamar takarda dake boye a kasan wurin batir ko idan ka bude murfin waya wacce ake kira da LDI wato Liquid Damage Indicator. Amfanin wannan yar takarda tana zuwa ne a fara idan har ruwa ya shiga wayar ka zai canza zuwa wani kalan.


Hardaware


Wani lokaci kuma hardware wato kayan da ake iya gani a taba a jikin waya suma idan suka fara samun matsala suna iya haifar da waya ta rika yin zafi.


Cire tsarin da ba a da bukatarsa ko amfani dashi


Wannan yana daga cikin babban matsalar da mutane da dama basu fahimta ba wurin yin amfani da wayoyin hannu, akwai wadansu tsare –tsaren da suke cikin waya wadanda ba kodawane lokaci muke amfani da su ba. Misali irin su hotunan fuskar waya masu motsi, ko kuma irin karin agogon jikin waya na musamman mai zama a fuskar waya, ko irin apllications na duba yanayi wato weather app a turance da dai makamantansu. To ire iren irin wadanna Applications din yana da kyau idan ba amfani da su za mu yi ba mu rika dakatar da su wato disabling din su.


Abubuwan da ba ayi idan waya ta dau zafi


Kada don kaji wayar ka tayi zafi kamar zata kone ko zata kama da wuta ka ce zaka saka ta a cikin firij ko gidan kankara. Bama bada shawaran yin haka domin kun san dai waya da ruwa sai a hankali, kuma sanyi da zata dauka daga kankara ruwa zai koma, kuma zai yi wa wayar babban lahani.


Wayar dai taki dai na zafin ta


To idan duk abin da muka lissafo maka a wannan darasi ka gwada amma wayar ba ta dena zafi ba, to idan kasan wayar kace ka sayar ka sayi sabuwa  ko kuma lasisin garantin ta bai shekara ba zaka iya mayar da ita kamfanin wayar. Shi yasa yake da kyau mutum ya ringa siyan irin wadannan kayan a wurin manyan diloli domin zai taimaka wurin idan wayar ta samu matsala za su iya karba su canza maka wata sabuwa. Amma da sharadin ba ka yi ganganci wurin lalata ta ba, ko baka kaiwa injiniyoyin gyara samun sa a ba.


Rufewa


Lallai zafin da waya ta ke yi hatsari ne ga remu da jama’a da kuma wadanda suke tare da su, sai sa yake da kyau ko wani lokaci mu ringa kula da yanayin da wayoyinmu suke shiga domin kare lafiyar mu da kuma dukiyan mu.


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

1 comment:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive