Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

ABUBUWAN DAYA KAMATA MUYI LA’AKARI DASU WAJEN SAYAN SABUWAR TAFI DA KAYAN KA WATO LAPTOP

Assalamu Alaikum barkan mu da warhaka barkanmu da sake saduwa acikin sabon shirinmu insha Allah yau zamu tattauna akan abubuwan daya kamata muyi la’akari dasu wajen sayan sabuwar kwanfuta, Wai shin, menene abubuwan da ya kamata ayi la’akari in a nason siyan sabuwar tafi da kayanka wato laptop a turance kuma wani wani campani yafi inganci a yanzu?  abu na farko da ya kamata muyi la’akari da shi a lokacin da zamu siya kwanfuta zai sayi kayan wuta ba ma dole sai kwanfuta ba, shine suna da inganci sosai? idan aka zo ga maganar kwanfutan tafi da kayanka wato laptop kusan gaskiya campanoni da dama a wannan lokaci suna matukar kokari wajen ganin sun wuce tsara, amma idan maganar wace irin tafi da kayanka laptop zaka ka siya saboda ingancinsa to ya danganta da aljihunka domin kare da kudin shi ai zai sha lahaula. Idan kuwa ka zo siya ka duba mene ne girman processor dinsa ma’na yanayin gudunsa, kuma mene ne girman RAM din su, mene ne kuma karfin batirin ta awa nawa yake yi, domin a wannan lokacin karanci ka samu sabuwar laptop tana kai awa hudu da rabi cikakke kafin ta dauke, daga baya sai ka duba girman HARD DISK dinta wato girman kwakwalwanta, sannan kuma ka duba girman ta domin wata ta fiye kankanta wata kuma tafi girman da yawa ka duba matsakaiciya wacce ba zata baka wahala wajen dauka ba kuma wajen aiki. sannan bayan ka biya ka lura da yi mata charging kafin ka fara amfani da ita domin rashin yi mata charging da farko yakan lalata batir, A yanzu campani da aka fi samun kayansa a kasuwa shine HP da kuma DEL yana da kyau mutum in zai siya ya takaita a cikin biyunnan domin wasu in sun samu matsala kafin a samu kayansu a kasuwa yana da matukar wahala, sannan kuma kada ka rinka saka mata program ko applications da ba zaka yi amfani da suba kuma ka guji saka games da video da baka san daga inda suke ba. Kuma tunda ka yi kokari ka sayi tafi da kayanka laptop da kudi mai yawa to ka daure ka siya sabon antivirus daga company kaspersky ko kuma norton domin duniya anyi ittifaki babu wanda ya fisu defination na virus wato fasahar virus amma bayansu akwai wasu da dama wanda suke taimakawa sosai kamar su smadav.


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive