Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

YANDA ZAKA GYARA SOCKET IN YA BACI

ASSALAMU ALAIKUM...Muhammad Abba Gana daga DUNIYAN FASAHA ke muku fatan alkairi, insha Allah yau zan koya muku yanda ake gyara kan socket na fanka, tibi, sidi kodai wani abu makamancin haka mai amfani da wutan lantarki in ya bachi ko ya karye ba tare da zuwa wajen mai gyara ba ko tuntuban wani, amma a yanzu zanyi amfani da dutsen guga ne, Abun kula!! bazamu dauki alhankin jinkata ko mutuwar wani ba, da izinin Allah in ka bi sharruda da hanyoyin da zan zayyano ba wani matsala da za,a samu.  Wutan lantarki de kowa yasan illarsa kuma da yanda ake amfani dashi, Abu na farko shine ka cire tsoro a zuciyanka in har kasa tsoro a zuciyarka, shakka, ko mumunar fata ko kuma cewa bazan iyaba ko ba hurumina bane to bazaka taba tsinana abun kirki ba.
Abun da kake bukata wajen yin gyara:-

    1.     Ma dauri kuma magwaji (school driver)
    2.     Kan socket mai kai biyu

    3.     Malika wanda akafi sani da black-tabe

   1-    Ma dauri ko magwaji (school driver) wanda aka fi sani da tester a turance wani kayan aikin fasaha ne da masanan wutan lantarki ko gyaran mota suke amfani dashi dan sawwake aiki, shi wannan abun aikin sa shine daure note yayin da ake aiki, kuma ana iya amfani dashi wajen gane ko akwai wuta a jikin igiyar da kake aiki, ana iya samun sa wajen masu siyar da kayan wuta, rahusar farshi ne dashi komai tsadar sa baya wuce naira hansin 50 zuwa naira saba’in 70.



   2-    Kan socket wanda akafi sani da head plug a turane, wannan wani dan karamin malika ne da masanan wutan lantarki suke amfani da shi wajen canza kan soket na wuta in yasamu matsala, socket plug din sun kasu kashi biyu akwai mai kai daya sannan akwai mai kai biyu,  ko wannen su akwai mai stada akwai mai saukin sa amma ko wanne ka siya zaka iya amfani dashi sai dai  komai mai tsada yafi jimawa akan mai sauki kuma ba tsada ba har zuwa can bane mai kyaun kafa biyu baya wuce naira hamsin 50 zuwa dari 100. Mai kafa uku ne suke da dan tsada saboda akwai wanda ake sawa a abubuwa masu jan wuta kamar su firiji, murhun girki da dai sauransu, dan amafani da kaya masu jan wuta sai ka siya mai stadar wanda farashinsa a yanzu ya kai naira dari biyar 500.  Amma dan sawa a yan kana nan abubuwa wanda basu jan wuta zaka iya siya mai saukin wanda farashin sa bazai wuce naira dari 100 zuwa dari biyu 200 ba, wasu lokutan yakan iya jimawa ya dangana ne da aikin da ake masa. 


    3-    Malika wanda akafi sani da black-tabe shi wannan malikar ana amfani dashine wajen lika igiyan daya bule koya dan samu targade saboda gudun matsaloli dazai iya jawowa, amma mata suna aiki dashi a harkokin su na yau da kullum irin su lalle, duk abunda na irgo za,a iya samunsu a kasuwa wajen masu sayar da kayan wuta baza,a kuma rasa a kananan shagunan mu ba.




Yanda zaka canza wanda ya samu matsala

Abu na farko da zaka farayi shine cire tsohon kai da yake jikin round socket naka wanda ya samu matsala sai ka kunce shi da testern ka, amma akwai wasu igiyar irin na tv koh na fanka wanda ba,a taba canza musu kai ba wannan zayyi wuya ka iya kunce wa, saboda ba wajen note in haka ya kasance to mafita daya kake dashi shine yanke sama kusa da kai din wanda ba wani mastala zai kawo ba muddin ka siya wani kai din.


Bayan ka kunce kai din ko ka yanke in kasa hankali zaka ga igiyoyi biyu ja da kuma baki amma ba lallai bane ka samu ja da baki zai iya zama wasu kaloline koma wani irin kala ka ci karo dashi zayyi aiki sannan akwai wasu wanda suke zuwa da igiya uku a ciki za,a iya samun biyun da abu a ciki dayan ba komai zai iya zama kuma dukka su zo dashi in har haka ya kasance to ja da baki kawai zaka dauka saboda sune masu amfani dayan baya aikin komai ana sasane in daya daga cikin biyunnan ya samu matsala sai a maye gurbinsa.

Abu na biyu shine stefe kan igiyar saboda samun damar shiga cikin sauki, sannan zaka yanke dayan da bazakayi aiki dasi ba, zaka samu rezan ka ko kuma wuta wanda zaka dan kona yayi saukin fita akwai wani kuskuren da mutane suke yi shine tsefe igiyar wuta da baki ko wani igiya makamancin haka, yin hakan babban illane saboda duk wani abunda aka kera ana sarrafasa ne da wasu sinadari wanda ni ko kai ba lallai bane musan su ba balle kuma musan menene aikinsa saboda haka yana da kyau mu daina amfani da bakin mu wajen biyan wani yar karamar matsala dan zai iya haifar da illa babba bangaren lafiyarmu.



 Abu na uku shine bude kan socket da ka siyo, zakayi amfani da madaurinka wato tester koh schooldriver a turance, wajen bude note dake daure a jikin kan wanda zai baka damar  sa igiyoyin, bayan ka bude marfin zai rabu kashi biyu daya ta bangaren nan dayan kuma ta can hakan ba wani matsala bane zai koma daidai kamar yanda yake a da. Bayan ka bude marfin wannan mazaunin mai dauke da kafafuwan da suke shiga cikin socket din zaka ga wasu notuna guda biyu wanda aikin su shine rike igiyoyin da za,a cusa cikinta wanda kowanne da zaman sa da kuma aikin sa, notunan wasu suna zuwa a bude wasu kuma suna zuwa ne a daure  in ya kasance a daure sai ka dauki madaurinka  ka bude wannan notunan guda biyu yanda igiyar zata samu damar shiga tsakiyar ba tare da wani gardama ba. 

Abu na hudu sai ka dauki igiyar naka na fanka ko tv wanda ka tsefe bakin sa sai ka tura na faro cikin rami daya, zaka iya sa ko wani kala a ramin farko saboda basu da takamammen wajen zama duk wanda ya samu zai yi aikin sane amma abun kula anan shine kada ka yarda koda itsinin gashin dayan igiyar ya hadu da dayan wajen sawa saboda zai iya kawo babban hatsari, ka zuba hankali sosai ka tabbatar da cewa ko wanni gida yana zaune da dan gidansa, bayan ka sa ka tabbatar daya shiga sai ka daure note dake rike sa sosai sannan ka sa dayan kabi da’idan da ka dayan wajen sawa shima sai ka daure sa sosai, ka dan ja kasan saboda tabbatar da cewa sun shiga sosai in ka ja sai wani  ya fito to ka kunche note nasa kasake cusasa sosai yanda note din zai kamasa sosai.



Abu na biyar shine mayar da murafan da suke cire kafafuwan zaka fara sa daya in ya zauna daidai sannan ka saka dayan in su hau cibcib sai ka dauki note da ka fara kuncewa sai ka mayar tare da dauresa da madauri sosai ka tabbatar ya dauru daidai sannan kada ka daure sa can yanda zai iya fashewa saboda bashi da karfin da zai jure dauryiya sosai. Wasu igiyoyin suna da kauri sosai zayyu ka gama daurewa kasan bai kamu sosai ba sai ka dauki malikanka wato black-tabe sai ka matse kasan sosai sannan ka daure sa da mallinkan shikenan ka gama.
Abu na karshe shine gwadawa in babu wuta sai ka jira a kawo in kuma akwai sai ka je ka saka sa da izinin Allah zayyi,


Abun kula!!
     1-    Ka tabbatar igiyoyin da suke ciki guda biyu basu hadu da junansu ba
      2-    Ka tabba a jikin gaba daya igiyar ba inda ya bare ya hadu da junanasa, yin daya daga cikin wayannan zai iya kai mutun zuwa ga jinkata ko kuma mutuwa wanda muke fatan hakan bazai faru ba.
Bazamu dauki alhankin jinkatar ko mutuwar wani ba
 in baka/ki fahimti wanana mujallar sosai ba zaka/ki iya ganin video kai tsaye ta hanyan ganin wannan videon

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Za'a iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan
Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan



mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive