Assalamu Alaikum barkanmu da war haka, kuna tare da Muhammad Abba Gana daga DUNIYAR FASAHA yau insha Allah zamu tattauna kan Matsalar shanyewar batirin waya da sauri, zamanin mu na yau matsalar shanyewat battery ya zama ruwan dare, kayi cajin wayar ka amma sai ya ringa sauka kamar ruwa ake diba a cikin bokati wannan yana faruwane saboda wasu dalilai wanda da izinin ubangiji zamu taimaka wurin kawo muku manyan makasudin da suke kawo wananan matsalar da kuma hanyar magance su cikin sauki.
RAGE YAWAN APPLICATION (UNINSTALL UN-USEFULL APP)
Abu na farko shine yawan tara application a waya wanda basu aikin komai kuma baka aiki dasu, sau dayawa mutane na tara wasu application wanda basu ma san aikin me suke yi ba kawai suna sa wane saboda a ga suna da abubuwa a waya ko kuma dan ado, hakan yana shan batter saboda akwai wasu da dama wanda sukanyi aiki a larkashin kasa ba tare da ka sani ba, yana da kyau mutum ya kayyace applications da yake aiki dasu saboda wasun su suna zukan batteri ne ko kuma su janye maka yan canji da kake dashi, yana da kyau mutum ya cire wanda baya aiki dasu ko kuma bai san aikin me sukeyi saboda mahancewa ko kuma kujewa wayannan matsalar.
TSAYAR DA APPLICATION (STOP RUNNING APPLICATIONS)
Abu na biyu shine sanin wasu application da suke shanye batir da wuri a waya, sannan mene ne amfanin su a lokacin da suke yin aiki. Domin a wani lokaci mutum zai iya kunnan application a wayarsa kuma bai rufe su ba sannan ya sake bude wadansu. To barin application a kunne suna aiki a karkashin kasa, na daga cikin abubuwan da suke janyo karewar batiri da sauri. domin sanin wasu applications da suke aiki a karkashin kasa kuma ya yanayin jan batiri da suke yi, mutum na bukatar ya shiga settings sai ya je zuwaga Battery. Wannan zai sa kaga wadansu Applictions ne suka fi zukar cajin batir da kuma shin wadanda kake son yin amfani da su, ko kuma wanda dole wayar tana da bukatar su domin ta yi aiki, Idan Application na wayar ce ke butakarsu to dole ka yi hakuri ka barsu su ci gaba da aikin su, domin hana su aiki zai kawo matsala da katsalanda ga aikin da ita wayar take yi. Amma idan application ne wadanda suke taimaka maka wurin yin aiki to sai ka danna force stop. Akwai applications masu dinbin yawa a Play Store wadanda suke taimakawa wurin sanin hakikanin mai yake faruwa da batirin wayar mutum. Mu a nan zamu iya ba da shawarar saukar da GSAM Battery Monitor. Idan ka saukar da wannan Application, zai iya daukan kwanaki yana binciken lafiyar batirin wayar da kuma abubuwan da suke zukarsa. Bayan ya kammala zai baka cikakken bayani dangane da batirin. Canza sabon Batir Wani lokaci zaka iya samu cewa wayar da mutum ke amfani da ita tsohuwa ce. Misali kamar yadda da yawa daga cikinmu suke siyan wayar hannu wacce wani yayi amfani da ita, To gaskiyar magana shi ne, idan har ka duba cewa babu irin wadancan Application masu aiki a karkashin kasa masu zuke batir, kuma ka rage hasken fuskan wayar, to magana ta gaskiya shi ne yana bukatar sabon batir. Kamfanonin da suke yin batirin waya sun ce ana iya yin cikakken cajin waya har sau dubu daya (1000) kafin ya fara saurin zukewa, amma shima hakan ya danganci wani kamfanin ne yayi batir din. Idan ka yi dace wayar ana iya cire batir din ta, to babu matsala sai a cire batir din ka canza shi da sabo, amma kuma idan irin wayoyin da ba a cire batir din su ne, to yana da kyau ka kaiwa kwararru ko ma kamayar da wayar zuwa ga kamfanin da suka kera ta idan a garin da kake akwai su, su cire maka batir din su mayar da sabo. A wurin canjin batir akwai korafi da jama’a suke yi musamman idan suka sa sabon batir sai su ce shima sabon baya dadewa, ko kuma yana dadewa bai cika ba. To akwai matsaloli guda uku ga hakan. Matsala ta farko shine ba a duba karfin batirin da wayar take bukata ba. Domin bakin da ake zura batir yayi daidai da naka amma kuma karfin da wayar take take bukata bai kai ba, matsala ce, kuma idan batir din bai kai karfin da wayar ke bukata ba zai yi saurin zuke batir din. Matsa ta biyu Cajar Wayar bata aiki yadda ya dace Matsala ta uku kin yin caji da sauri, shima yana da alaka da sabon batirin da ka saka, misali ka saka batirin da yake da 1200mAh kuma sai ka sami cajar wayar da take sa karfin 240mAh to yana nuna maka cewar sai kayi jira har sau uku kafin ta cika. Wadannan matsalar abin lura ce kuma haka ake magance su. Shi yasa yake da kyau sosai duk lokacin da mutum ya ke son sayan caja to ya tabbatar ya sayi ta kamfanin wayarsa. Wani lokaci amfani da caja mai karfin da tafi na batiri shima matsala ne, domin zai yi saurin kona sinadaran da suke ajiyar caji da wuri, kuma gasa batirin da sauri zai iya lalata shi ba zai jima ba, kuma wani lokaci koda ka samo cajar asali da aka yi domin wayar sai ka ga bata iya yin komai a wayar. Tsarin wayar yana amfani da batir sosai Daya daga cikin abin daya fi komai zukar batir shi ne Android System. Android System shine babbar application da take taimakawa wayar domin ta yi aiki kamar yadda ya kamata, tsayar da ita tamkar tsayar da wayar ne ko kuma lalata ta. Ga ka’ida na wadanda suke yin OS na Android sun ce Android System bai kamata ya wuce kashi ashirin da biyar cikin dari (25%) na batirin wayar ba. To amma idan aka samu ya wuce haka, to ya nuna cewa akwai matsala sosai, kuma babu wata hanya da za a iya magance wannan sai ta hanyar ragewa wayar babbar manhajar da ita kanta wayar take amfani da ita. Misali ace wayar tana amfani da android Lollipop ne sai ka dawo da ita zuwa Android Kit-kat. Akwai hanyoyi da dama da ake amfani da su wurin ragewa OS an Android daraja da ake samu a shafukan intanet, kawai ka rubuta downgrade (sunan wayarka). Yin hakan shi ne kawai mafita, amma mu sani hakan kuma na matsayin kayiwa wayar flashin ne, amma wani abun jin dadi koda lokacin da kake kokarin rage mata daraja an sami matsala zaka iya yin factory reset, wayar zata dawo daidai.
MATSALA TA UKU:
Google Play Services yana zuke batir Google Play Services shima yana daga cikin abubuwan da suke zuke batir da wuri, abin haushi shine ba zai yiwu ka tsayar da shi ba, domin shi ke taimakawa wurin ganin applicaions da suke cikin wayar suna da alaka tsakaninsu da wanin su, musamman ta wurin musayar bayanai. Amma duk da haka akwai yadda zaka iya rage wannan cajin. kaje Settings saike latsa Applications sai kaje zuwa ga All sai ka danna Google Play Services sai ka taba maballin Clear cache. Wannan zai goge duk wani abubuwa da wannan application ta ke tattare da su sannan ta fara gina wadansu, wanda wannan zai rage shan batir, zaka iya sake yin haka kowani farkon wata.
DAKATAR DA AUTO-BRIGHTNESS (CANCEL AUTO-BRIGHTNESS)
Dangane da matsalar hasken fuskar waya, kusan da yawa daga cikin matsalar mun fi barin cewar wayar mu ta rinka lura da haske da kanta wato auto brightness a turance. Barin wayar ta rika lura da shi da kanta ba shi ke nuna hakan ba daidai bane. Matsalar a nan ita ce, sensor da yake jikin wayar yana aiki tukuru wurin sanin wani wuri ita wayar take, shin akwai haske mai yawa ko kuma babu, idan akwai haske to sai fuskar wayar yayi duhu, idan kuma akwai dubu a wurin sai ta yi haske, saboda haka barin sa a auto yana taimakawa wurin ganin cin batir. Yadda idanun mu suke bukatar haske ya sha banban da na kowa, saboda haka yana da kyau ka tsayar da wayar ka zuwa hasken da ka san shi ya fi dace da kai, kuma hakan zai taimaka wurin ganin batirin baya karewa da wuri.
RAGE DADEWAR DISASHEWAR HASKEN WAYA (REDUCE DISPLAY TIME)
Kamar yadda muka sani hasken da ke fita ta fuskan waya na daya daga cikin manyan abubuwan da suke kawo shanye batir musamman wayoyin Android. Saboda haka a lura da tsawon lokacin da wayar take yi cikin haske sosai yana da amfani. Lura da tsawon lokacin yana da matukar muhimmanci domin a wani lokaci wasu sukan bar hasken ya kai kusan minti biyar ko goma kafin ta tafi barci. To kamar dai yadda na fada dadewar hasken fuskar wayar yana zukar batir sosai. Yana da kyau mu rage daga dogon lokaci zuwa gajere, misali daga minti guda zuwa dakikoki ishirin ko kasa da haka. zai taimaka wurin kara rage shanyewar batirin waya. Lura da ‘yan kanzagin app wanda aka fi sani da widgets turance da masu aiki karkashin kasa Wadannan Application da ake kira da Widgets su wakilan application ne da suke tsayawa a fuskar wayar mutum suna sanar da shi wadansu al’amura da asalin manhajar take yi. Misali manhajar duba yanayi, wato Weather App, application ce mai zaman kanta amma kuma wadanda suke yinta sai su yi mata dan kanzagi (widgets) wanda zai wakilci shi babban da bai bukatar kodawane lokaci sai an budeshi za’aga abin da ke ciki. irin wadannan applications kasancewar akwai guda daya ko biyu nasan mutum ba zai damu ba, amma yana da kyau mu sani cewar irin wadannan applications suna aiki ne a karkashin kasa domin aiwatar da ayyukansu. To idan mutum yana da su da yawa a cikin wayarsa to ya sani yana saurin shanyewar batiri. Saboda haka, irin wadannan applications irin na labarai masu neman shiga yanar gizo da yin aiki ta karkashin kasa yana da kyau a ciresu. Haka irin application da suke bukatar yin update kodawane lokaci suma suna da matsalar cin batiri wani lokaci yana da kyau mutum ya tsayar yin automatic update na wayar sa ya sa shi zuwa wani ayyanennen lokaci kamar sau daya a wata. Shima hakan zai taimaka wurin rage shan batiri.
Wannan su ne dan kadan daga wasu abubuwa wanda muka ga suna daga cikin musabbabin shanye karfin wutar batiri, kana da wata matsala ko abun cewa? Mu tattaunata a wannan wuri! In kuma ka samu wannan post da bansha’awa taimaka ka turama yan uwa da abokan atziki dan su amfana.
No comments:
Post a Comment