Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Abubuwa 10 wanda wayar salula keyi wanda bamu da masaniya a kansaAssalamu alaikum, mun dade muna amfani da wayar salula stawon lokuta amma bamu taba karanta littafin shugabanci ba wanda aka fi sani da manual a turance, muna alfaharin cewa mun iya amfani dashi ko kuma muna da ilimi akan sa kuma yana faruwa, sau da dama zaka ga mutum yana abu wanda bai dace ba da wayar salulansa ko kuma yayi abu wanda bai ma san yanda ya faruwa ba hasalima yasan yanda zai sake, kawai de yaga yayi, yan uwa kada ka bari wani dan uwanka koh abokinka ya fika da fasaha ko kishi. Ga wasu daga cikin asiri da ke binne a cikin wayarka wanda baka san da zamansu ba amma zaka sansu yau.


NA FARKO: DAUKA HOTO (TAKE A SCREENSHOT)
Shin ka taba son ka dauki hoton wani abu a wayar salulanka wanda akafi sani da screenshot a turance? Wata kila sako daga abokin arziki koh dan uwa koh kuma wani abun ban sha’awa da kaga a facebook koh kuma kana da abu a waya kana so ka turama wani yanda zaiyi abu ko yanda abun yake?.
Yanda zaka dauki abu cikin sauki tare da wayanka na android-
Danna ka Rike wajen kunna wayar tare da wajen rage sauti a lokaci daya. zakaji karan daukan abu Hoton ya dauku yana cikin dakin nuna zane-zane wanda akafi sani da gallery a turance. Amma yana aikine gamasu wayoyi android 4-0 zuwa sama wanda nasa kasa da haka bazayyi aiki ba.
 Yanda zaka dauki abu cikin sauki tare da wayanka na iphone-
Dannna ka Rike wajen gida tare da kwana/tashi wanda akafi sani da sleep and wake a turance zakaji karan daukan abu zaka samesa sa a shashen ‘camera roll  ko kuma a saved photos.  NA BIYU: TOSHE KIRA (BLOCK CALLS)
Shin kana yawan samun kira daga wajen wanda bai kamata ba? ko wani yana yawan damunka ga yanda zaka toshe kiransa ko kuma toshe sakoninsa shiga layin wayarka.
          Yanda zaka toshe kira a wayanka na android-
Ka shiga saituna ka danna setting>> call settings>> call block karkasin ‘incoming calls’ danna ‘call block list’ sai ka danna ‘create’ zaka iya sa number ko ka danna wajen gumaka dan nemo number daga lambobin cikin waya koh a cikin register kira.                                                                                                                                                                                                                                                             
                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                          
          Yanda zaka toshe kira a wayanka na iphone-
Dan toshe kira a wayarka na iphone bude wajen ‘phone’ ko kuma ‘ face time app’ in mutumin kana dashi a cikin wayarka, danna kan sunansa sauka zuwa karshen shafin sai ka danna ‘block this contact’ in kana so ka cire number da kayi blocking sai kaje settings>>>phone>>>blocked.

  NA UKU: AMFANI DA KALMAR SIRRI NA HAKIKA (USE A REAL PASSWORD)
Android da iphone, nokia da wasu wayoyin salula dukkan su asalin number sirri dake ciki shine 0000 koh kuma 1234 amma nasan akwai mutane da dama dake son tsaro a wayoyin salulansu ga yanda zaka canza asalin number sirri dake ciki zuwa wanda kake so.
          Menene amfaninsa?? Amfaninsa shine suturche wayarka da ga shige-shige na mutane da yara.
          Yanda zaka saka Kalmar sirri a wayar ka na android-
Kaje zuwa ga setting ka sauka kasa zuwa’ security’ sai ka shiga ‘screen lock’ sai ka danna zai tambayeka wani iri kake son sawa, na farko akwai ‘pattern’ wanda shi zana wa akeyi akwai kuma ‘pin’ wanda shi numbobi ake sawa akwai kuma na ukkun shine ‘mixed password’ a wasu wayoyin ‘password’ duk abu daya ne shi wannan zaka iya sa harrufa koh kuma ka hada harufa da numbobi, in ka zabi daya  zai tambaye ka kasa lambar sirrin, ko ka zana son ra’ayinka inna zana wane abun kula!! Ka tabbar ka san abunda ka sa ko kake sawa ko kuma ka zana, sai ka danna ‘continue’ zai sake tambayarka ma’ana ka sake sa abunda ka sa abaya, in kayi hakan sai ka danna ‘confirm’ yanzu wayanka ya kullu duk lokacin da ka kunna ko ya dan zauna na dan wani lokaci ba tare da aiki ba zai tamabayeka kasa in ba daidai ba bazai taba budewa.
          Yanda zaka saka Kalmar sirri a wayar ka na iphone-
Sai kaje zuwa ga settings >>password daga nan sai ka danna zabin dayace ‘simple passcode’. Daga nan sai kasa zabin ranka abun kula!! Ka tabbar ka san abunda ka sa ko kake sawa, sai ka danna ‘continue’ zai sake tambayarka ma’ana ka sake sa abunda ka sa abaya, in kayi hakan sai ka danna ‘confirm’ yanzu wayanka ya kullu duk lokacin da ka kunna ko ya dan wani lokaci zai tamabayeka kasa in ba daidai ba bazai taba budewa.NA HUDU:  CANZA GIRMAN RUBUTU (SEE TEXT MORE EASILY)


Shin kana samun matsala wajen karanta abu a waya saboda kankantar rubutu? Karo girman rubutu na wayar salulanka zuwa yanda zaka gani kuma ka gane
          Yanda zaka canza grima rubutu a android-
Kaje zuwa ga setting na wayar ka, ka shiga general ka sauka kasa zuwa ga Display sai kaje zuwa ga front size zaka same sa a normal sai ka canza sa zuwa ga large wasu wayoyin zaka ga extra large wasu kuma medium duk wand aka gani a cikin wayannan sai ka zaba daga nan sai ka danna ok shikenan zaka ga rubutun wayar ka ya canza zuwa babba.
          Yanda zaka canza girman rubutu a wayarka na I phone
Kaje zuwa ga setting na wayarka sai ka sauka zuwa ga general daga nan sai ka shiga accessibility sai ka danna bold text and larger. Zaka iya zaban daya ko dukka biyu ya danganta ka da yanda kake so yayi kafin ya fara aiki dole sai ka kasha ka kuma kunna wayar taka.


NA BIYAR: KARANTAWA (READ THINGS LOUD)


Shin kana so ka kulle idonka yayin da wayarka zai karanta ma abu kaji. Ga yanda zaka seta:
          Yanda zakayi a wayar ka na android
Kaje zuwa ga setting ka sauka kasa zuwa inda aka rubuta accessibility sai ka shiga sai ka danna talkback in baka gani ba zaka iya saukar dashi a google play store.
          Kunna shi wayarka yanzu zai karanta komai da ka taba ko kuma wani sanar wa ko in sako ya shigo da sauransu, dan shigan abu dole sai ka danna sau biyu ba daya ba kamar da, dan gyara maganan sai kaje zuwa ga settings sai ka shiga Accessibility sai ka danna text-to-speech.   
                   Yanda zakayi a wayarka na iphone
Kaje zuwa ga settings ka shiga general kaje zuwa ga accessibility sai ka kunna voice over si ka gyara farashin maganar da sauransu.


NA SHIDA: CUSTOMEREIZE JIJJIGA ALAMU (CUSTOMIZE ALERT VIBRATION PATTERNS)Ka saita ringintone na wayar sallulanka  amma wani sa’in baka jin karan kira yayin da kake wasu yan sungulloli mussamman maza abin farin zaka iya saita vibration a ciki.
          Mene vibration? Vibration shine ci gaba kadan girgiza na tafiya ma’ana wani fasaha ne dake cikin waya da yake sa waya yake motsi ko kuma ya na juyawa.
          Yanda zaka sa vibration a wayar ka na android-
Kaje zuwa ga settings na wayarka latsa kan sound and vibrate sai ka latsa kan vibrate sai ka zaba dukka uku da suke ciki, shikenan
          Yanda zaka sa vibration a wayar ka na iphone-
Kaje setting na wayarka sai ka sauka zuwa inda aka rubuta sounds sai ka latsa kai sai ka je zuwa ga ringtone daga nan sai ka danna kan vibration, shikenan.


NA BAKWAI: WALKIYA NA SANRWA/KIRA KO SAKO (FLASH ALART NOTIFICATIONS) Shin kana son kasan lokacin da sako ya shigo ko kira yayin da kake wasu ayyuka in baka son aiki da vibration,
          Yanda zaka saita walkiyar wuta na sanarwa a wayar ka na android-
Kaje zuwa ga setting na wayarka sai ka sauka zuwa inda aka ce Accesibillity sannan ka kunna shi, amma sau da yawa wasu wayoyin basu zuwa dashi zaka iya saukar da wani application a google play store wanda ake kira ‘flash alerts’ in ka saukar shigar wato download and install a turance  sannan ka bude zai nuna ma “thanks for using flash alerts…da sauransu sai ka danna inda aka sa Next zai kai ka zuwa ga wani shafi sai ka danna Test,  zai sake kaika zuwa ga wani page inda aka rubuta ‘the app recognized a camera flash please press next to proced’ ma;ana wanna application ya gano wutar wayar danna next dan cigaba abin kula!! dole wayar kay a zamana yana da wuta a da yake haskawa in ba haka b aba zayyi aiki ba, daga nan sai ka danna Next zai kaika zuwa ga wani shafi  inda aka rubuta ‘ the test will be started with module type 1. The flash will be blinked for 5 times please press ‘test’ button’ ma;na wannan application din zai jarraba wuta zai kawo ya dauke sau biyar  sai ka latsa inda aka rubuta ‘Test’ wuta dake jikin wayar ka zai kawo ya dauke sau biyar in y agama zai kaika zuwa ga wani shafi  inda aka rubuta ‘ did you see the blinked flash for 5 times? If you did, please press ‘flash confirmed’ button, if you didn’t please press ‘test type2’ button” ma’na shin ka ga wuta sau biyar a baya ko saman wayanka?? In ya kai biyar to latsa inda aka sa ‘flash confirmed’ in kuma har in bai kai ba ko bai kawo ba ka latsa inda aka rubuta ‘test type 2’ dan sake jarrabawa, in ya kai biyar  zai sake dawo da kai shafin in har yanzu ya kai biyar sai ka danna ‘flash confirmed’ zai kaika zuwa wani shafi daga nan sai ka latsa ‘complete setup’ shikenan ka gama yanzu duk wani kira ko sako da ya shigo wayar ka wuta zai haska,

          Yanda zaka saita walkiyar wuta na sanarwa a wayar ka na iphone-
Shiga zuwa ga setting na wayar salulanka ka sauka zuwa inda aka rubuta general sai ka latsa sai ka sake sauka zuwa kasa zuwa inda aka rubuta Accessibility sai ka danna zaka ga inda aka rubuta ‘turn flash for alerts’ sai ka latsa shikenan yanzu duk sa’in da sako ko kira ya shigo wutar wayan zai kawo ya dauke. 

kana da wata matsala ko abun cewa? Mu tattaunata a wannan wuri! In kuma ka samu wannan post da bansha’awa taimaka ka turama yan uwa da abokan atziki dan su amfana.
mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive