Hanyoyi Guda 5 Da za’a Magance Kumburin Ido
Matsalar kumburin ido tana haifuwa ne a sakamakon rashin barci, matsanancin kuka, sauyin yanayi, matsalar mura har ma da cin wasu kalar abinci. kumburin ido na sauyawa mutum kamanni kaga mutum kamar ya kara tsufa, ko kuma yayi kamar ba shi da lafiya ko yayi alamun ya gaji da yawa, wannan ya sa ba karamar matsala ba ce musamman ga mata duba da yadda ya ke karawa mutum muni, kuma yake bata kwalliya.
Duniyan Fasaha ta kawo muku hanyoyi guda 5 da zaku iya magance wannan matsala
Gurji (cucumber): Gurji yana dauke da sinadaran da suke rage kumburi, da tattarewar fata a karkashin ido. Domin amfani da gurji wajen rage kumburin ido, da farko za’a yanka gurjin sai a saka shi a cikin _rji yayi sanyi sannan sai a kwanta a dora shi a kan ido na tsahon mintuna 10 zuwa 30. A maimaita haka sau 3 ko fiye da hakan a rana.
Cokula: Za’a saka cokula kamar 5 ko 6 a cikin firij suyi sanyi sosai ko kuma a dora masu kankara. Sai ana dauko daya bayan daya ana dannawa ido har sai yayi dumi, sai a dauko wani daban. Haka za’ayi har cokulan su kare. Sanyin cokulan yana taimakawa wajen sanyaya idanu da kuma matse kofon fata dake a karkashin ido, hakan ya kan sa kumburin ya sace.
Ganyen shayi: Shi ma ganyen shayi yana dauke da sinadaran da suke magance kumburi da kuma rage jan Ido. Yadda za’a yi amfani da shi shine, bayan an dafa shayin sai a tsamo ganyen kamar guda 2 a saka a firiji suyi sanyi na tsahon kamar mintuna 30. Bayan sun yi sanyi sai a dora su a kan ido a daure da kyalle na tsahon mintuna 10 zuwa 15 kuma a maimata hakan sau 2 a rana.
Dankalin turawa: Banda rage kumburi, dankalin turawa yana taimakawa sosai wajen magance bakin da ke zagaye ido (dark circles). Za’a fere dankali danye a nika shi. Sai a zuba nikakken dankalin a tsumma mai tsafta a kulle a saka a firiji yayi sanyi. Sai a dauko shi a dora a kan ido na tsahon mintuna 10.
Aloe Vera: Ruwan Aloe vera na dauke da sinadaran da ke rage kumburi da tamushewar fatar karkashin ido. Za’a matso ruwan shine kawai ana shafawa a gurin kumburin akai akai har sai kumburin ya sabe. Amma fa a hankali don kar ya shiga ido.
Da fatan wadannan hanyoyi sun wadatar wajen tabbatar da an magance kumburin ido
Mungode da wannan taimakon
ReplyDelete