Yadda ake hada ’Yar tsala
Assalamu
Alikum barkan mu da sake saduwa da ku cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa
muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha, Uwargida barkanmu da warhaka tare
da fatan alheri da kuma fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda
ake hada yar tsala. Yana da kyau Uwargida ta kasance mai tsabtace jiki da kuma
iya sarrafa girki dabandaban da kayan marmari. Don haka dole ne mace ta dage
wajen taka rawar gani a harkar girki tare da koyon kowane irin salon girki.
Kayan hadi:
==> Gero
==> Mangyada
==> Yis
==> Gishiri
==> Dakakken yaji mai kulikuli
Yadda ake yi:
Za a surfa
gero sannan a bushe a wanke sai a shanya, idan ya bushe sai a kai a niko a
tankade shi, sai kuma a jika yis da ruwan zafi. Sai a dauki ruwan yis din a
kwaba garin geron da shi bayan an sanya masa gishiri.
Idan an
gama kwabawa sai a bar shi ya dade kamar misalin sa’a biyu zuwa uku, ya
danganta da yanayin gari, ma’ana idan lokacin zafi ne ba sai ya dade sosai ba.
Idan kullin ya kumbura ko ya tashi sai a dan kara ruwa a juya ana son kwabin ya
zama da dan ruwaruwa.
Idan aka
gama hadawa sai a asa cokali a rika diba ana soyawa a cikin mangyada. Idan ’yar
tsalar ta soyu sai a kwashe. Ana ci da yaji wanda ya ji kulikuli sosai.
No comments:
Post a Comment