Amfanoni sha biyu (12) da Lalle keyi Ga ‘Ya Mace
|
Assalamu Alaikum barkanmu da sake saduwa da
ku a cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar
Duniyan Fasaha, kuna tare ne da Muhammad Abba Gana insha Allahu yau zamnyi
bayani ne akan amfanin lalle gaya mace, hakika Lalle na cikin wani sinadarin da
ke dauke da alfanu iri iri, kuma addini ta kwadaitar da mata yin lalle akwai
sirrika acikin sa mai griman gaske. Menene
Amfanin Lallai?
In nace lalle wasu zasu dauka zanen henna
nake nufi ko, to lalle dai na gargajiya wanda muka rabu da yinsa yanzu shi nake
magana akai. toh a hakikanin gaskiya lalle yana da amfani diyewa ga rayuwan ya
mace amma ga manyan daga cikinsu:
1.==> lalle Kariya ce daga sihiri, Kariya ce daga aljanu
sannan kuma Kariya ce daga cututtuka da dama.
2.==>
Yin lalle a kafa na zuqe cutar dake kafa
sannan yana kula da dumin mace, bi maana yana inganta ni’imar mace ba tare da
ya gushe ba.
3.==>
Ga duk mace mai infection, ta tafasa lalle in
ya dan huce sai ta yi sit bath dashi na sati biyu in Allah ya yarda zata warke.
4.==> Ana
iya sha ruwan lalle cokali 1 don wankin dattin ciki amma banda masu ciki.
5.==>
Don gyaran Fata; lalle dai ba karamin tasiri
yake dashi wajen gyara fata ba, domin shi natural toner ne wanda ba bilicin
yake yi ba amma yanasa haske mai kyau kuma yana goge dattin fata.
6.==>
A bangaren gyaran fuska, tana sa fuska tai
kyalli, laushi, da haske in an kwaba da ruwan Kwai amma banda kwaiduwar kwan.ki
kwaba ruwa ruwa amma ba sosai ba ki lizimci shafa shi kullum na mintuna talatin
(30) kafin wanka sai Kinga bambanci a cikin sati biyu Insha Allahu.
7.==>
Ga masu son hasken fata, ki kwaba lalle da
ruwa, ki shafe a jikinki inya bushe ki dirje da man zaitun za kiga canji.
8.==>
Ga masu fama da pimples, yar’ uwa ki hada
lemon tsami da lalle kwabi mai dan tauri amma ba sosai ba kina shafa wa a
fuskar ki bayan watanni kuraje zasu mutu sannan tabo bazai zauna ba ga hasken
fuska da laushi.
9.==>
Sannan gamai son kamshin fata, Ki kwaba lalle
da turaren ki mai kyau na ruwa wanda ake durawa ki zuba isasshen ruwa a bucket
ki sa garin lalle ta jika tai já zir sai ki tsiyaye ruwan ki diga turaren ki
mai kamshi ciki Bayan kinyi wankan sabulunki sai ki dauraye jikinki dashi inkin
lizimci haka to bake ba rabo da kamshin jiki in sha Allahu
10.==>
Sannan ga Amare Kafin kiyi dilke na aurenki
ki kwaba lalle mai kyau tare da turare mai maiko, turaren gargajiya mai mai, ki
jika kamar bucket daya kada yayi ruwa ruwa sosai kamar dai kunu, kullum sai ki
shafa a dukkan jikinki sai ki zo ki saka turaren wuta akasko ku burner ki rufu
akai ki turara jikinki har sai hayakin turaren nan ya shiga jikinki sosai sai
ki fita kije kiyi wankan ki,za kiga canji a fatar ki rapid canji kuwa. Fata za
tayi laushi, haske da kuma santsi. Wata biyu kafin bikin ki zaki iya wannan
kedakanki kuma zakiji dadin hakan.
11.==>
Lalle nasa cikan gashi, ba yasa gashin kan
mace ya zube, yana da matukan amfani wajen gyara gashin mace, inda wasu ke tura
(steaming) gashin su dashi ma’ana.
12.==>
A karshe mata na yin ado da lalle wajen kara
kyaun kwalliyar su. wanda su ke zanawa a jikin su.
No comments:
Post a Comment