Yadda za ki yi amfani da man kade wajen magance kyesbi
Sau da yawa masu fama da kyesbi sukan ce
kyesbin ba ya jin magani, har sukan yi masa kirari da ‘kyesbi; tsoho mai ran
karfe’. Idan wannan ce matsalar sai mu ce ki sha kuruminki, domin mun taho miki
da hanyoyin da za ki bi wajen magance kyesbi.
1==> A karon farko, ki samu man kade wanda ba a
sanya masa wani abu ba. Misali, man kade da ba sanya turare ko aka hada shi da
wani mai ba.
2==> Kafin ki yi amfani da man kade wajen magance
kyesbi, yana da kyau ki shafa man a wani bangare na jikinki, misali, a
kumatunki ko gefen kunnenki, kasancewar man kade na haifar da matsala ga wata
fata. Idan bayan kin shafa man bai kuma haifar miki da matsala ba, sai ki yi
amfani da shi wajen magance kyesbi.
3==> Ki samu ruwa mai dumi, sai ki debi man kade,
sannan ki zuba kofin shan shayi daya na gishiri a cikin ruwan da za ki yi
wanka. Bayan kin yi wanka sai ki tsane jikinki da tawul mai kyau da kuma
tsabta.
4==> Daga nan sai ki shafa man kade a jikinki da
kuma wurin da kyesbi ya fito miki, sannan ki rika yin tausa (massage) a wajen.
Za ki iya yin hakan sai biyu a rana.
5==> Bayan kin shafa man kade, sai ki guji sanya
tufafi mai kauri, ko kuma mai kaushi wanda zai rika sosa fatar jikinki.
Wadansu hanyoyin magance kyesbi:
1==> Daga farko ki wanke duk wurin da akwai
kyesbi da ruwa mai dumi, daga nan sai ki goge wurin da tsumma mai tsabta. Bayan
nan sai ki samu man E45, sai ki shafa a wurin. Yin hakan zai magance kyesbi.
2==> Amfani da man da ke dauke da sinadarin
‘hydrocortisone’ na magance kyesbi. Daga farko ki yi wanka da ruwa mai dumi.
Bayan nan sai ki shafa man. Ire-iren wadannan man suna busar da kyesbi. Amma
kafin a yi amfani da ire-iren wadannan man kamata ya yi a nemi shawarar
likitoci.
No comments:
Post a Comment