Idan ana kwalliya kada a manta da tsaftar
baki wadda duk yadda mutum ya kai ga kyau idan har yana magana kuma ana jin
warin bakinsa akwai babbar damuwa. Yana da kyau a kula da yadda ake wanke baki
da hakora da kuma harshe. Domin idan daya daga cikin wadannan ababen da kidanya
bai wanku ba, hakan zai iya haifar da warin baki. Yawan cin tafarnuwa da albasa
da kuma shan giya na haifar da warin baki. A yau na kawo muku hanyoyi da za a
bi domin magance warin baki.
==> Idan ana sanye da hakorin roba ne, yana da
kyau a rika wanke su sannan a cire su a baki a lokacin da za a kwanta bacci da
dare. Kwanciya da su a baki na haifar da cututtuka da ke sanya warin baki.
==> A yawaita shan ruwa sosai; shan ruwa na
wanke kowace datti da ke baki. Yana da kyau a rika kurkura bakin da zarar an
tashi bacci, domin fitar da kowace dauda da ke cushe a tsakanin hakora.
==> Idan an san ana da warin baki, a kasance
cikin wanke baki da magogi hade da man goge baki a duk lokacin da aka gama cin
abinci domin magance matsalar wari.
==> Yawaita amfani da magogin hakora na haifar
da cutar warin baki. Don haka, yana da kyau a rika canza magogi bayan watanni biyu
zuwa uku, domin samun hakora masu lafiya.
==> Kada a manta zuwa ganin likitan hakora,
domin ya taimaka wajen wanke hakoran da magunguna domin rage warin baki.
==> A yawaita cin kanamfari sosai, cin kanamfari
na magance kwayoyin cututtukan da ke haifar da warin baki.
==> Yawan cin ‘ya’yan itatuwa kamar su amfuna da
lemu da mangoro da abarba da dai makamantansu na rage warin baki.
==> A samu garin ‘baking soda’ sannan a kwaba da
ruwa sai a rika Kurkure bakin da shi, amma kada a hadiye. Za a iya samun
‘baking soda’ a shagunan da ke sayar da kayakin hadin ket.
No comments:
Post a Comment